GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin kuka Zainab ta mik’e ta nufi wajen Momy da Dady duk ta rud’e ta fita daga hayyacinta kwata-kwata babu ko d’igon nutsuwa a tattare da ita, gaba d’aya a kid’ime take, ta zube a gaban su Dady tace “Dan girman Allah Momy kusa baki Naseer ya bar min Na’eem, wallahi nayi mugun yin nadama jikina yayi mugun sanyi, wallahi nayi danasanin abubuwan danayi, kuma Allah zan rik’e shi da amana bisa gaskiya da tsoran Allah, duk duniyar nan babu wanda yafi ni cancanta dana rik’e Na’e………..

“Ke awa? cewar Nasir, a zafafe ya yarfa hannayensa da k’arfi zuciyarsa nayi masa suya gami da rad’ad’i mai zafi, ya kalle ta ido cikin ido yana hawaye yace ” ko ke a makashiyar mahaifiyar sa, idan har na bawa wacce tayi sanadiyyar mutuwar mahaifiyarsa ta rik’e shi banyi masa adalci ba, banyi masa gata ba, nasan idan ya girma sai yaji ya tsane ni, ko ma yasani acikin jerin wad’anda zayyi hukunci.

Tana kuka ta mik’e ta nufi inda Naseer yake cikin matsanancin kuka tace ” please Naseer ka bar min Na’eem kona ji sassaucin abinda nake ji a zuciyata, walahi ji nake kamar na mutu dan mutuwar zata fiye min sauk’i da salama akan bak’in halin bak’in cikin danake ciki.

” To ki mutu mana, da uban waye ya hana ki mutuwar, in kin mutu waye zayyi bak’in cikin mutuwarki, mun ma rage mugun iri a doron k’asa, banza wofi kawai.

A hankali ta zube a gabansa bisa kan gwiwowinta (ta durk’usa) tana kuka kamar ranta zai fita, zuciyarta nayi mata suya had’i da k’una tana jin k’irjinta kamar zai tsage zuciyarta ta fito saboda tsabar tsananin zafin take ji a k’irjinta, tace ” dan girman Allah Naseer ka bani Na’eem bazan tab’a sawa kayi dana sani ko nadamar bani rik’on shi, please ka bani dama ta k’arshe na gyara kurakurai na, in sha Allah zan sa kayi alfahari da hakan, na nuna mashi so da tsantsar soyayyar kamar yadda kowacce uwa take bawa d’anta, please Naseer.

A matuk’ar fusace Naseer yace ” soyayarki ta banza da wofi, Allah yayi wadaran soyayya irin taki, soyayyar mara amfani, wacce da zarar mutum yayi kuskure d’aya kuma koda akan rashin sani ne, bakya bashi uzuri, nan take zaki manta da tarin soyayyar kiyi watsi dashi da lamuransa, daga k’arshe ma ki zama sanadiyyar salwantar rayuwarsa, me za’ayi da irin soyayyarki.

K’ara k’arfin kukanta tayi ta zube a gaban shi tana rok’onshi tana yi mishi magiyar ya bar mata Na’eem, ” please Naseer kaji tausayi wallahi ina buk’atar a tausaya min.

Murmushin takaici Naseer yayi yace ” Allah ko?

“Ashe ke kina buk’atar a tausaya maki?

“Amma ke kwata-kwata baki jin tausayin wasu, baki jin rok’on su ko kukan su, baki da saurin yafiya, baki tab’a manta laifin ke da akayi miki, amma ke kin iya magiya, kin iya rok’on a tausaya miki, bayan ke baki aikata d’aya daga cikin abinda kike rok’on ayi miki, haka Zarah tayi ta kuka tana baki hak’uri tana neman yafiyarki, tana tsananin buk’atar tausayawa daga wajenki amma kika k’i sauraranta balle ki tausaya mata, ga abinda kikayi ya janyo nan, sai kema ki d’and’ani bak’in cikin inda gaske kikeyi.

“Naseer duk duniya babu wanda yafi cancanta daya rik’e Na’eem sama dan……..

Tun kafin ta k’arasa ya katseta da cewa ” sai ni, Zainab sai ni ubansa kuma mahaifinsa na fiki cancanta dana rik’e d’ana, ke kin isa ma ki kalli tsabar ido na kice min duk duniya babu wanda yafi cancanta daya rik’e min d’ana sama dake bayan ina nan a raye.

Da sauri ta mik’e ta nufi wajen Abban Zarah dake tsaye tace ” dan Allah kasa baki Naseer yabar min Na’eem naga yana matuk’ar jin maganarka, kafin Abban Zarah yayi magana Naseer yayi saurin cewa.

” Banda a wannan b’angaren, Zainab dama kin hak’ura kin dai na wahalar da kanki wajen rok’on na, da bin mutane akan su sani nabar miki Na’eem, dan wallahi tallahi duk duniya babu wani mahaluk’i daya isa yasani nabar miki ruk’on Na’eem, wallahi ko waye shi, idan ma mutum yasan ina ganin girman sa da mutuncinsa karya sake ya soma saka baki a maganar nan, dan zan iya shafawa ido na toka na zage na tsula rashin mutunci, ke dai dayake kwata-kwata baki data ido sai kiyi tayi.

” Wallahi tallahi, wallahil azim, na rantse miki da girman Allah Zainab ko zaki mutu, bazan tab’a baki Na’eem ba koda zakiyi mushe a gaba na, zan sa k’afa na tsallake mushenki nayi gaba da d’ana, ya juya ya d’auki Na’eem daya ajiye akan sofa, ya nufi bedroom d’in sa.

Cikin kuka Zainab tace ” ni ban san me nayi maka a rayuwarka ba, na rasa me nayi maka haka, cak ya tsaya had’i da juyowa ya tako har gabanta ya sunkuyo da fuskarsa saitin tata fuskar yana kallanta ido cikin ido yace ” Au tambaya ta ma kike yi, kina nufin baki san abinda ki kayi man ba, lalle Zainab kwakwalwar ki bata aiki, ta samu matsala tunda har kike cewa kin rasa abinda kika yi man, Na’eem dake rungume a k’irjin Naseer ganin ya sunkuyo saitin Zainab ya juyar da fuskarsa daga kallan Zainab ya cusa kansa cikin k’irjin Naseer ya k’ara k’ank’ame Naseer had’i da tsandara kuka.

Ganin abinda Na’eem yayi yasa Naseer dakatar da maganarsa batare daya gama fad’ar abinda yake san fad’a ba, ya mik’e tsaye yana kallan Na’eem, duk ya rud’e ya fita hankalinsa, murmushi Naseer yayi yace ” Alhamdulillah Masha Allah, nagodewa Allah, ya kalli Zainab yace ” kinga tsantsar k’iyayyar da Na’eem yake miki ko, ko k’aunar kallan fuskar ki baya san yi, ji yadda ya fita daga hayyacinsa saboda kawai na sunkuyo dashi sai tin ki, kin dai gani da idanki, bai girma ba balle kice ni na koya mishi yadda zai tsane ki.

Gaba d’aya jama’ar wajen cike da matsanancin mamaki suke kallan Na’eem suna al’ajabin abinda yaro d’an 6 months yayi, hannu Zainab ta d’ora aka had’i da fashewa da matsanancin kukan bak’in ciki.

K’ara rungume Na’eem Naseer yayi tsam a k’irjinsa yana murmushi hawaye na zuba daga idanuwansa yana sauke ajiyar zuciya, batare dayace komai ba, ya shige bedroom d’in sa ya rufo k’ofa, anan Zainab ta durkushe tana matsanancin kukan bak’in cikin rayuwa, anan kowa ya barta Alhaji Abdullahi, da Abban Zarah sukayi tafiyar su, Dady da Momy suka haye samansu, sai da dakyar Mannir ya lallab’e ta ta yarda suka tafi gidan su suma.

Tun a parlor Zainab ta zube tana ci gaba da kukanta, shiko Mannir dayake yafi Zainab shiga matsanancin halin damuwa da bak’in ciki shiru kawai yayi ya shige bedroom d’in sa ya fad’a bathroom ya sakarwa kansa shower had’i da dafa bango yana tunanin mafita dan shi kansa yasan bazai tab’a iya ci gaba da rayuwa cikin farin ciki da walwala muddin ba Na’eem a kusa dashi ba, zaman lafiyar sa d’aya, da kwanciyar hankalinsa shine yaga Na’eem a tare dashi, dan shi da kansa yasan tunda yake a duniya bai tab’a san wani abu kamar yadda yake mugun san Na’eem ba, dan idan ya ganshi jikinsa har rawa yake, ga yaron kyakykyawan gaske fari fat kub’ul-kub’ul dashi kamar yaron turawa, muddin aka raba shi da Na’eem dai-dai yake da raba shi da duk wani farin ciki, jin dad’i, walwala, nishad’in sa.

Dan duk duniya a halin yanzu babu abinda Mannir yake so yake kuma k’auna kamar Na’eem yafi san shi fiye da kowa da komai, akan yaron babu abinda bazai iya ba, muddin zai dawo masa da yaron kusa dashi ko meye shi zai iya yin abun komai wahalarsa, tsaki yayi had’i da kaiwa bangon bathroom d’in naushi da hannunsa, take yaji ciwo jini ya fara zuba amma shi ko kad’an bai ji zaifin ciwon ba, dan zafin da zuciyarsa take masa yafi ciwon yi mishi rad’ad’in, babu abinda zuciyar sa keyi masa sai rad’ad’in zafi da k’una, ga wani mahaukacin suya da k’irjinsa keyi masa kamar an zazzaga petroleum an kunna ashana.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button