GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Duk iya tunaninsa ya rasa wata mafitar kamawa, yayi-yayi amma babu wani kwakkwaran abin kamawa balle ya samu hanyar da zai kasance da Na’eem farin cikin rayuwarsa,, ajiyar zuciya ya sauke da k’arfi, sannan ya kashe shower ya fita daga bathroom d’in, kan bed ya fad’a yana ci gaba da tunanin naimarwa kansa mafitar da zata fishe shi, ganin har lokacin bai samo mafita bane yasa shi mik’ewa ya nufi parlor.

Bai iske kowa a parlor ba, dan haka tunanin shi ya bashi tana bedroom, kai tsaye ya nufi bedroom d’in Zainab, a hankali ya tura k’ofar ya shiga, akan bed ya iske ta tayi rud da ciki tana ta faman rusa uban kuka kamar ranta zai fita har shid’ewa take yi amma tak’i yin shiru, hannayen shi ya harde a kafad’arsa ya zuba mata ido yana magana shi kad’ai a ransa ” hmmmmmm Zainab kenan ke kin ma samu damar yin kuka kin gusar da naki bak’in cikin rayuwar, idan damuwa da bak’in ciki sukayi ma mutum yawa baya iya yin kukan fili sai na zuci, duk abinda kikaga ana yi masa kuka yana da sausauci ne, amma ni dayake nafi tsananin san kasancewa da Na’eem kwata-kwata na kasa kukan, ni so nake ma nayi kukan hawaye ya zuba kona samu sausaucin rad’ad’in da zuciya ta keyi min.

A fili kuma yace ” subhanallah yana sauri ya k’arasa inda take had’i da d’ago ta ya rungume a k’irjinsa, yana cewa ” kai haba Zainab mai yasa kike irin haka ne kwata-kwata kin k’i ki yarda da k’addara ki mik’a dukkan lamuranki da Allah, k’ara sautin kukan nata tayi tana k’ok’arin kwace jikinta daga nashi, shi kuma ya k’ara matseta da k’arfi yadda bazata iya kwace kanta ba, hak’ura tayi ta kwantar da kanta akan k’irjinsa tayi luf tana ci gaba da kukan nata.

Cikin rashin nutsuwa Zainab ta d’aga kanta tana kallan fuskar Mannir tana shashshekar kuka tace ” idan har kana sona, kuma san da kake yi min gaskiya ne, ta nuna sai tin zuciyar sa tace ” idan har zuciyar ka tana bugawa da tawa bugun zuciyar, idan har kana san naci gaba da rayuwa a duniya, idan har kana k’aunar ci gaba da ganina a duniya, kasan duk hanyar daza kabi ka kawo min Na’eem cikin gidan nan, matuk’ar kana k’aunar ganin farin ciki da walwala ta ka kawo min Na’eem, duk hanyar daza kabi, kabi kowacce irin hanya ce, kuma komai zaka aikata koma meye kayi ka kawo min Na’eem…………

MOMYN ZARAH
[14/02, 22:00] Atk: GADAR ZARE!!!

(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)

       ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

GARGAD’I

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO

BEST FRIEND FOREVER & EVER
ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~

58

Ta k’araashe maganar cikin matsanancin kuka, kanta ya shiga shafawa kawai batare dayace mata komai ba, dan shi kad’ai yasan irin abinda yake ji a zuciyarsa zuwa k’irjinsa, dan wani irin mugun tafasa jinin jikinsa keyi, ga k’unar da rad’ad’in da zuciyarsa keyi masa, k’irjinsa ko jinsa yake kamar yana ci da wuta, mak’ogwaronsa kuwa ko yawu ya had’iya ji yake kamar mad’aci.

Idanuwansa ya runtse da k’arfi yana sauraran yadda zuciyarsa ke bugawa da tsananin k’arfi kamar zata fasa k’irjinsa ta fito, shima yasan matuk’ar aka raba shi da Na’eem to kwanakinsa na duniya sun k’are, yasan raba shi da yaron dai-dai yake da tsinkewar numfashinsa, domin yasan lokacin mutuwarsa yayi, Allah kad’ai yasan irin mugun son da yake yiwa Na’eem, wanda shi kansa yasan Allah ne ya jarrabeshe da tsananin sansa, wanda shi kansa yana mugun mamakin yadda yake jin yaron a ransa.

Ko bacci idan ya farka babu abinda yake fara fad’o masa sai Na’eem, idan sallah yana ransa, kai komai Mannir yake da tsananin tunanin Na’eem yake yin sa, baya iya yin ko da 1 second batare daya tunashi ba, tun da Mannir yake a duniya bai tab’a san wani abu kamar Na’eem ba, bai tab’a sanin haka zafin so da rad’ad’in sa yake ba sai akan Na’eem, kwata-kwata baya cikin farin ciki da kwanciyar hankali gaba d’aya ya rasa nutsuwarsa, duk ya d’imauce ya fita daga kamanninsa, duk 1 minute yana jin yadda san yaron yake shigarsa yana ratsa duk wani b’argo da tsoka had’i da jijiyoyin jikinsa zuwa magudanar jininsa, take ya fara zubar da hawaye yana tausayawa kansa da rayuwarsa, a hankali hawayen dake zuba daga idanuwan Mannir ya fara d’iga akan kuncin Zainab.

A hankali Zainab ta d’ago kai tana kallan fuskarsa, taga yadda hawaye ke zubowa da gudu, a tunanin Zainab ta d’auka hawayen tausayinta ne bata san hawayen tausayawa kansa da halin da zai shiga muddin aka raba shi da Na’eem bane, a hankali Zainab tasa hannu tana goge masa hawayen dake bin faskarsa itama tana zubar da hawayen ta shiga girgiza mishi kai alamar yabar kuka, kasa dainawa yayi dan bai isa ya tsaida hawayen dake zuba ba dan baga Idanuwansa suke ba daga zuciyarsa suke.

Dakyar Zainab tace ” please kayi shiru, idan kaima kana kuka nima inayi tsakanin mu wazai bawa wani hak’uri, wazai rarrashi wani?

“Dan Allah ka daina kuka idan kana kuka sai na karaya, kukan ka zai hana zuciyata sakat, zai hanani nutsuwa da farin ciki, kuma zai k’ara saka ni rauni, naji kamar mun rasa Na’eem ne, please control your emotions , ta fad’i maganar tana goge masa hawayen dake zubo masa.

Ajiyar zuciya Mannir ya kuma saukewa yana kallan ta batare dayace mata komai ba, a hankali ta kuma kwantar da kanta akan k’irjinsa tana ci gaba da kukan ta, shiko Mannir ya kasa furta koda kalma d’aya ce saboda halin bak’in cikin dayake ci, kanta kawai yake shafawa yana fidda numfashi da sauri-sauri, yayinda zuciyarsa ke harbawa tana ci gaba da bugawa da tsananin k’arfi.

Su Mannir na fita Naseer ya fito hannunsa d’auke da Na’eem ya iske Momy da Dady zaune a parlor kusa da Momy ya nufa directly, a gefenta ya zauna yana duban k’asa batare dayace komai ba, ganin hakan da yayi ne ya tabbatar wa Momy akwai magana a bakin Naseer dan haka ta karkarta gaba d’aya hankalinta ta maidashi kansa, tana kallan sa, ganin wajen 10 minutes amma Naseer bashi da alamar ko motsa bakinsa balle yace k’ala yasa Momy kallan Dady, shima ita yake kallo, a hankali Dady ya mik’e ya koma kusa dashi ya zauna yana fuskantarsa, yasa hannu yana shafa suman kansa zuwa gadon bayan sa, Momy ma matsowa tayi kusa dashi sosai tasa hannu ta d’auki Na’eem dake kan cinyar Naseer, ba musu Na’eem ya yarda da Momyn had’i da kwanciya luuuuuf a jikinta, Ikram Momy ta kwalawa kira.

Wacce tun mutuwar Zarah ta mayar da kanta zaman d’aki, ta mayar da kanta, shiru-shiru duk ta rame ta koje ta zama kamar ba ita ba dan magana ma ita yanzu ba’a san ranta take yinta ba akan dole ake sawa tayi magana, mika mata Na’eem Momy tayi tace ” kiyi masa wanka ki had’a masa madararsa ki bashi yasha, batare data ce komai ba ta d’auki Na’eem dake ta mik’o mata hannu tun fitowarta daga bedroom.

Mai da hankalinta Momy tayi kan Naseer tace ” meke faruwa ne Naseer?

Shiru yayi yana tunanin ta inda zai fara b’ullo musu da maganar barin Nigeria, dan yasan ba lalle ne su amince masa ya tafi can shi kad’ai ya koma can da zama ba, amma shi hakan shine kad’ai kwanciyar hankalinsa da nutsuwar sa, dan kwata-kwata Nigeria ta gama fice masa a rai, yadda kasan akan wuta yake zaune haka yake ji.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button