
Tun mutuwar Zarah ya gama ayyanawa a ransa shida Nigeria haihata-haihata matsawar yana san ko kwatankwacin farin ciki da walwalar sa na baya zasu dawo masa, amma matsawar yana cikin Nigeria, ko yaci gaba da zama a cikin ta, rayuwarsa ta baya bazata tab’a barin zuciyarsa ba,
ya kuma san muddin hakan zata ci gaba da faruwa barazana ce ga lafiyarsa dama rayuwarsa gaba d’aya,
dan haka ya gama yanke hukuncin barin k’asar nan kota halin k’ak’a inko ba haka ba za’a waye gari aga gawarsa shima zuciyarsa ta buga.
Shi kad’ai yasan halin dayake ciki, dauriya kawai yake yana k’ok’arin danne damuwarsa, dan kar hakan ya haifarwa da rayuwar iyayensa matsala ya gusar musu da farin cikin su kamar yadda nashi ya gama gushewa ya kuma tarwatse,
a kullum kwanan duniya idan ya waye gari ya ganshi a cikin gidan, bak’in cikinsa tsananin k’aruwa yake, kewar Zarah da mugun santa na k’ara harbar zuciyarsa, yana k’ara tsintar kansa da rayuwarsa cikin matsanancin bak’in ciki da damuwa mai d’auke da zafi da k’una.
A hankali ya lumshe idansa hawaye na zubo masa, sai da yayi wajen 10 minutes a haka sannan ya bud’e idan nasa da suka gama rikid’ewa zuwa launin ja!!!!,
ya sauke su akan iyyen nasa, kansa Momy ta shafa tana dukan sa cike da tausayawa, ji take kamar ta d’ora hannu aka ta fasa kuka saboda tsananin rad’ad’in da take ji na ganin Naseer a cikin muguwar damuwa, mai tsananin yawa,
dan kallo d’aya zakayi masa ka fahimci halin daya ke ciki.
Kansa Dady ya shafa yana kallansa yace ” Son kayi magana mana dan alamunka sun nuna kasan magantuwa.
Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi sannan yace ” please ina san barin k’asar nan d…..
Bai k’arasa ba Momy tace ” kamar yaya ban fahimci ka ba, me kake nufi da kana san barin Nigeria?
Fuska ya b’ata kamar zayyi kuka cikin rawar murya yace ” please Momy & Dady allow me to leave this country please I beg you in the name of almighty Allah ,
wallahi nayi mugun tsanar k’asar nan yadda kuka san akan k’aya nake haka nake ji na.
A zabure Momy tace ” kana nufin tafiya zakayi ka bar mu ko me kake nufi Naseer?
Kuka ya fara sannan yace ” please still I beg your permission, wallahi Momy matuk’ar kuka ce dole sai naci gaba da rayuwa anan tabbas wata rana za’a wayI gari bana nan duniyar ma gaba d’aya sai dai kuga tawa gawar nima dan nima zuciyata gaf take da tarwatsewa,, Momy k’ok’ari kawai nake ina danne damuwa da halin bak’in cikin danake ciki dan karna jefaku a halin damuwa.
“Momy Allah ne kad’ai yasan gaskiyar abinda ke raina, shi yasan me nake ji a cikin rai na da zuciya ta, so please Momy allow me to go, please don’t say no ya k’ara maganar yana zubewa a gaban su bisa gwiwowinsa yana had’a hannayen shi biyu alamar rok’o (magiya).
Momy zatayi magana Dady yayi saurin dakatar da ita ta hanyar d’ora hannunsa akan nata ya danna, hannun tabi da kallo tana sauke ajiyar zuciya dan ta fahimci abinda yake nufi, dole yasa ta yin shiru badan ta so ba, shi ko Dady gaba d’aya jikinsa ne ya gama yin mugun sanyi, take zuciyarsa tayi la’asar tausayin Naseer yayi mugun kamashi,
sai da ya faki idan Naseer da Momy ya goge hawayen tausayin Naseer dake zubo masa had’i da sauke ajiyar zuciya sannan yace.
” Wacce k’asa zaka?
Sai da Naseer ya lumshe ido hawaye na ci gaba da zubo masa sannan yace ” HOLLAND.
murmushi Dady yayi had’i da shafa kansa yana kallansa cike da tausayawa yace ” bakomai Naseer mun yarje maka ka tafi mun baka izini ko yau ma kana iya tafiya,
amma kayi min alk’awarin zaka cire damuwa a ranka zaka ci gaba da rayuwarka cikin farin ciki da nishad’i,
sannan ka kula da addininka, al’adarka da kuma mutuncinka dana addininka da namu mutunci.
“Alhamdulillah shine abinda Naseer ya fara furtawa kafin yace ” in sha Allah I will try my best, karka damu Dady ko wannan ma daya faru akan Zarah Allah ya riga ya tsara akwai rabon Na’eem sannan kwanakinta na duniya ba masu tsawo bane.
Kansa Momy ta shafa tana murmushi tace ” Allah yayi maka albarka ya albarkaci rayuwarka, Ubangiji ya tsare min kai da tsarewarsa ya kare min kai da kariyarsa, duk abinda zai fi k’arfinka ko ya zame maka matsala Allah yayi maka maganinsa, sosai Momy tayi ta kwararo masa addu’o’i haka ma Dady shima sosai yayi masa addu’a wanda haka ba k’aramin dad’i da sanya shi cikin farin ciki suka yi ba.
Kallan Momy yayi yace ” Momy a shirya kayan Na’eem dan dashi zan tafi, ya fad’a yana duk’ar da kansa k’asa.
A fusace tace ” kamar ya dashi zaka tafi?
“Eh Momy bazan iya barin shi anan bane, ni ina can hankali na bazai kwanta ba.
“Saboda cinye shi zamuyi, kafin ka dawo mun kanya shi munyi farfesun shi ko?
” A’a Momy ba haka nake nufi ba, Momy kona bar miki shi su Mannir bazasu barshi anan gidan ba, sai sun rabaki dashi nasani, ni kuma babu abinda nafi tsana a doran duniya sama dasu,
ko dabba ta bazan tab’a bari ta k’ara taka gidan ba balle kuma d’ana na ciki na, please Momy ki barni na tafi dashi, ya fad’a cike da ladabi,
dan idan baki barni na tafi dashi ba an bar baya da k’ura dan konaje can d’in ma hankalina ba kwanciya zayyi ba.
Murmushi Dady yayi yace ” oh my son an zama Baba Naseer kana da san d’a da yawa son, yanzu in banda rigima irin taka ya zakayi da shi acan idan an baka?
“Nanny zan d’auka daga hospital sannan zan saka shi a day care, kaga zai samu kulawa.
Ajiyar zuciya Dady ya kuma saukewa sannan yace ” ok badamuwa Allah ya tsare ku baki d’aya, Ubangiji ya baka damar kula da shi.
“Amin Naseer yace, kafin yayi jummmm ko suna da wata maganar dashi, ganin basu da abin cewa ne yasa Naseer mik’ewa har ya kai bakin stairs Dady ya kira sunansa ” Naseer
a hankali Naseer ya juyo yana kallon Dady had’i cewa ” na’am.
Cikin sanyin murya Dady yace ” ka tuna duk lalacewar Mannir da Zainab naka ne su, kuma duk lalacewar naka,
naka ne, dan hausawa sunce naka sai naka, dad’in zama sai bare, kuma d’an uwa rigar k’aya ka saka ya soke ka, ka cire ka tafi tsirara, murmushi kawai Naseer yayi ba tare daya ce komai ba ya haye samansa.
Washe gari tun da safe Naseer ya tashi domin maganar tafiyar sa, ya kama shirye-shiryen haik’an dan yana san nan da kwana biyu ya d’aga, cikin sa’a ya gama duk wasu shirye-shiryen sa kasancewar akwai kud’i a hannu, bai dawo gida ba sai yamma sosai.
A parlor ya iske Dady da Momy, Mannir dake gefen su rai b’ace, bayyiwa kowa magana ba ya fara k’ok’arin hayewa sama, ganin su Dady basu da niyyar yi masa magana yasa Mannir mik’ewa a fusace cikin fushi yace ” Naseer wajenka nazo, magana nake san yi dakai.
Ba tare daya jiyo ba yace ” duk maganar da zakayi dani ka fara yi da magabata na tunda kasan ina da iyaye kuma har yanzu suna nan a raye,
a hasale Mannir yace ” wannan maganar kace, dan maganar Na’eem ce.
Har Naseer ya d’aga k’afarsa zai taka next step jin Mannir yace maganar Na’eem ce ya sashi,
mayar da k’afarsa baya, a hankali ya juya yana taka step d’in one by one har ya isa inda Mannir yake,
ya tsaya daf dashi yana kallansa ido cikin ido yace ” uhnnnn ina jinka.
Ido Naseer ya d’aga ya fara kallansa duk daga k’asa har sama baki bud’e, sannan yace ” izini kake nema ko kuma kazo sanar min ne?
“Ni dai na gaya maka nazo tafiya da Na’eem ne,
“Shine ai na tambaye ka izini kake nema ko kuma kana sanar min ne?