
Nan da nan yasa aka nemo masa Umar aka gawo masa shi gabansa, kallansa Sanata Sambo yayi yace ” Umar ko? da ido kawai Umar ya bishi baice masa komai ba, Sanata Sambo yaci gaba ” d’an fashi, d’an daba, d’an maye, sannan wanda ya makance akan san abun bazai taba samun saba wato Ramlat, d’an niger wanda iyayensa suka mutu, ya taso a hannun mak’otansu.
Tsaki Umar yayi yace ” kaga ni ba shirme da b’ata lokaci ne ya kawo ni ba, idan baka da abincewa ni zanyi gaba, dariya Sanata yayi sosai sannan yace ” ni ko ke da abincewa, ai abin cewar ne ma yasa ni kiranka, ” Ok ina jinka, ” nasan halinka, nasan sirrinka, nasan abubuwa da dama akan kawanda kai kanka baka sani ba, nasan baka da wani buri daya wuce na mallakar Ramlat, kuma kasan hakan bazai taba faruwa ba, idan Abdul yana raye, kai Ramlat kake so ni kuma rayuwar Abdul nake so, shiyasa na kiraka dan mu had’a hannu wajen cikar burin mu, saboda idan har Abdul yana raye bazan tab’a samun siyasata ba, haka kai ma bazaka tab’a samun masoyiyarka da Ramlat ba.
Dan hak……… Wata mahaukaciyar tsawa Umar ya dakawa Sanata Sambo wanda yasa shi yin shiru da bakin dole,batare daya dasa aya ba .
Umar ya mik’e tsaye yayiwa Sanata muguwar shak’a yace “wallahi in banda nayiwa Mama da Abdul alk’awarin na daina munayen halayen na da anan take zan murd’e maka wuya na jefar da wulak’antacciyar gawarka.
Saboda nasan ko awajen Allah kai wulak’antacce ne banza kawai wanda bai san darajar amana, halacci da alk’awari ba, iyayen na su mutu tun ina da 6yrs, mutanan nan suka d’auke ni, duk unguwar babu wanda ya kalle ni balle yasan Allah yayi ruwa na, sune ci na, sune sha na, sune sutura ta, sune komai nawa, su sukayi min komai arayuwa babu abinda basuyi min, sun yi min gata, sun rik’e ni kamar d’an cikin su, tunda nake dasu basu tab’a yi min wani abu na b’atanci ba, sannan dan kai jaki ne, jahili, wanda bai san me yake ba kace naci amanar wad’annan mutanan, wallahi Allah ya rufa maka asiri baka same ni sanda nake HORROR ba, da tuni ka tsufa a lahira, yayi jifa da Sanata yayi tafiyar sa, sosai Sanata ya bugu sakamakon jifan da Umar yayi dashi, bayan Umar Sanata Sambo yabi da kallo, yana murmushi bak’in ciki.
Bayan Umar ya koma gida ya samu Mama da Abdul yake sanar dasu yadda sukayi da Sanata Sambo, aiko sosai hankalin Mama yayi masifar tashi, ta kalli Abdul tace ” Abdullahi yanzu meye mafita? “addu’a mana Mama, addu’a itace babar mafita, bamu da wani abinyi sai ita, Umar ko sai huci yake yana sauke ajiyar zuciya da k’arfi, an tab’a masa ahalinsa, Mama ta kalle shi tace ” lafiya dai Faruk’u, naga kana ta faman huci? shiru yayi bai bata amsa ba, saboda ranshi ya b’aci yake sosai, murmushi tayi ta shafa kansa tace ” a dai dinga samawa zuciya salama, ana kwantar da hankali, tashi ka shiga d’aki ka kwanta, baiyi magana ba ya tashi yayi shigewar sa d’aki, Mama tace “Allah ya shige mana gaba, “Amin ya Allah, cewar Abdul.
Ganin irin wulak’anci da Umar yayi masa ga kuma wanda Abdul yayi masa yasa Sanata, k’ara hura wutar fansa a zuciyar sa, gashi yana ji yana gani al’umma tayi masa buye had’e dayi masa zanga-zanga akan dole sai an gurfanar da d’ansa a gaban kotu, haka yanaji yana gani aka kai d’an shi gidan yari, tun daga ranar ya k’uduri niyyar d’aukar fansa fiye da abinda Abdul yayi masa, ya shiga bin duk wata hanya dayasan zata fisheshi.
A kwana a tashi ba wuya a wajen Allah, ga shi har Ramlat da Yasmeen sunyi candy, kuma cikin nufin Ubangiji ya sake fitowa da Ramlat miji na gani na fad’a, dama hausawa sunce wani hanin ga Allah baiwa ne, kasancewar sunyi candy yasa aka saka bikin babi dad’ewa, sosai aka shiga shirye-shiryen bikin Yasmeen & Abdul, Ramlat & Jamil, sosai Mama da Umar ke farin ciki, Umar ya shige gaba akan komai, duk wata hidama ta bikin shi yake yinta.
Ana gobe d’aurin aure da misalin k’arfe 5:00pm Abdul na zaune abakin masallaci wani yaro da gudu har tuntub’e yake k’afarsa babu takalmi, ya zo gaban Abdul ya tsaya yana ta haki, Abdul na ganin yaron gabansa yayi muguwar fad’uwa ya k’urawa yaron ido ya kasa magana, shima yaron ya kasa cewa Abdul komai, cikin rawar baki Abdul ya kalli yaron yace ” lafiya? Shima yaron a tsorace yace ” gidan ku ne ke ci da wut…… ai kafin yaron ya k’arasa Abdul ya zunduma a guje koda yaje gaba d’aya gidan ya kama da mahaukaciyar wuta yana ci tako’ina mutane ma sun kasa dusar koda jikin gidan domin taimako duk wanda ya nufi gidan sai kaga ya dawo da gudu yana haki da zarar hucin wuta ya buge shi,mutane jungum acan nesa da gida kowa ya na san ya taimaka amma ba damar yin haka saboda tsoran wuta, saboda yadda take ci ya wuce tunanin mai karatu.
Abdul na zuwa ya fara tambayar ina ” Mama ina Ramlat, ina Ja’afar, ina Umar, maganar yake amma kaida ganinsa kasan baya cikin hankalinsa, gaba d’aya Abdul ya gama fita daga hankali sa, kowa ya kasa cewa komai aiko gadan gadan Abdul ya nufi gida, jama’a suka yo ca suka rik’e shi,Abdul yana jiyo Ramlat tana kwala mai kira, haka yana yiyo salatin Mama, da kukan Ja’afar, sosai Ramlat ke kwala mai kira, ihu Abdul yake yi sosai yahau dukun mutane had’e da kiciniyar kwace kansa Daga garesu amma ina sarkin k’arki yafi sarkin yawa Muryar Mama ya jiyo tana cewa ” Abdullahi karka zo, kar kazo, ko kai kad’ai ne ka rayu dan ka d’aukar mana fansa.
“Kar kazo Abdullahi, sai yaji Mama ta kwala kiran U…..MAR……………….
, sai kuma yaji salatinta daga nan bai kuma jiyo sautin muryar Mama ba sai kukan Ramlat dana ja’afar, dake ta faman ihu da kururuwa , itama har ya daina jiyo ta, sosai Abdul yake hauka a wajen ya haukacewa jama’a, yana ihu yana d’ibar k’asa yana zubawa jikinsa yana wanka da ita, sosai yake ihu yana birgima cikin k’asa, jama’a sai rik’e shi suke.
A firgice Abdul ya mik’e daga kan kujerar dayake zaune yana bada labarinsa, yana kallon sauran abokansa da ‘yan jaridan dake d’aukar labarin, fuska cike da hawaye idonsa sosai yayi jawur tamkar an xuba masa garwashi wuta yana kuka kamar ransa zai fita, ya hau buga kansa da bango yana ihu yake cewa ” sun kashe min kowa nawa, bani da kowa yanzu bani da wanda zan kira d’an uwana, ko dangi na, zaman dirshan yayi a k’asa yana kukan tuno mutuwa had’i da ihu, yana yarfa hannunsa zambur ya mik’e ya nufi fridge ya d’auko ruwa mai mugun sanyi ya b’alle murfin ya shiga bulbulawa kansa ruwan.
Cikin kuka yake cewa ” akan idona gidanmu ya k’on e da mahaifiyata, k’anwata, k’anina duk suka mutu akan ido na ina jiyo ihun su, gaba d’aya hankali 6’s STARS ya tashi dukkan su kukan suke babu mai lallashin wani, haka ma ‘yan jaridan, da dumbun jama’an dake sauraron labarin kuka suke, suna masu tausayawa Abdul, dukkan su suka mik’e suka nufi Abdul suka rungume shi ajikinsu suna matsanancin kuka, cikin karfin hali Abdul ya goge hawayen sa ya shiga lallashin sauran abokan nasa, sai da komai ya lafa sannan Abdul yaci gaba.
Bayan mutuwar ‘yan gidan mu ne na samu tab’in hankali amma ba sosai ba, kwakwalwa ta, ta d’an tab’u, bayan sadakar bakwai aka zo da gungun ‘yan sanda aka kama ni akan ana zargi na da kashe ‘yan gidan mu, duk da bani da cikekken hankali a lokacin amma nayi mugun mamaki, sosai naci mugun duka wajen ‘yan sanda kafin aka gurfanar dani gaban kotu, tambayar duniya alk’ali yayi min amma nak’i magana, kwata-kwata a lokacin bana k’aunar zaman duniya na tsani komai da kowa, nima babban buri na shine na mutu, ganin nak’i magana ne, alk’ali ya fusata har yake neman yanke min hukunci mai tsanani, ganin haka yasa Yasmeen bada shaidar bani da hankali, munafukan da suka k’unlla komai suka k’aryata ta, nan alk’ali ya bada damar aje amin test, sannan a dawo dani……….