GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

” A fusace Mannir yace ” ina sanar maka ne,

Murmushi Naseer yayi sannan yace ” kai a matsayinka wa, a wajensa?

Shiru Mannir yayi ya rasa abin cewa, ya kama kame-kame, ganin haka yasa Naseer motsi da bakin yayi sauti yace ” ayya ashe kai ba kowa bane a wajensa, tun baka da wani matsayi a wajensa,
sai ka koma wajen wacce ta aiko ka, kace mata hak’onta bai cimma ruwa ba, dan karrrrrr nake kallan ku, kuma ka sanar da ita Naseer dattijo ne dan magana d’aya kawai yake, baya tab’a canja maganarsa, sannan kace mata Naseer cikekken namiji ne ba irin lusarin mijinta wanda sai abinda tace yake ba.

Cikin tsananin fushi Mannir ya d’aga hannu zai mari Naseer, da sauri Naseer ya rik’e hannunsa had’i da cewa karka soma inba so kake yanzu jikinka ya gaya maka ba, dan daga wa baka kau ba, banza sakarai, hotiho,lusari, sauna, shashasha.

Naseer na kaiwa nan yayi hayewarsa sama yabar Mannir nan tsaye yana cizon yatsa.

A parlor ya tadda Zainab tana ta faman safa da marwa tana jiran dawowarsa, tana ganin shi ta nufe shi da tsananin sauri tana murmushi had’i da waiwayen bayan sa tana san hango Ikram d’auke da Na’eem, ganin babu kowa a bayansa yasata ja da baya da sauri,
tana girgiza kanta wahaye na zubo mata.

Duk abinda ya faru tsakaninsa da Naseer ya kwashe tasssss ya fad’a mata bai b’oye mata komai ba, ai yana gama gaya mata ta sulale k’asa sumammiya……………!!!!!!

MOMYN ZARAH

GADAR ZARE!!!

(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)

       ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

GARGAD’I

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO

BEST FRIEND FOREVER & EVER
ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~

59

A razane Mannir ya k’arasa inda take ya shiga jijjiga ta yana kiran sunanta ” Zainab!? ganin bata motsi yasa shi mik’ewa da sauri ya nufi fridge, da sauri ya d’auko ruwa, yana zuwa ya zuba mata, sai da ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi,
sannan ta fara tari, da sauri Mannir ya ajiye ruwan a gefe ya rungumo ta jikinsa.

A hankali – a hankali Zainab ta fara bud’e idanuwanta, da farko dishi-dishi ta fara gani kafin daga baya idanuwanta su washe tarwai,
ganin ta akan k’irjinsa yasa ta saurin zabura ta mik’ewa daga jikinsa had’i da ja baya.

K’ara motsowa jikinta Mannir yayi yana niyyar rungume ta,
da sauri Zainab ta k’ara ja da baya, hawaye na zubo mata ta kalle shi ido cikin ido tace ” karka sake ka soma k’ok’arin tab’a ni, bakin Mannir a bud’e cike da matsanancin mamaki ya k’ara matsowa yana cewa ” Zainab lafiyar ki kuwa?

Da sauri Zainab ta buge hannun Mannir daga jikinta tace ” karka sake ka soma tab’a ni na gaya maka,
matuk’ar kana san ci gaba da gani na cikin farin ciki da walwala gami da annaashuwa kamar da ka kawo min Na’eem.

Tsaye kawai Mannir yayi yana kallanta ya kasa cewa komai,
harta gama ta shige bedroom, sai da yayi wajen 10 minutes yana tunane-tunane gami da sak’e -sak’e,
sannan ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yabi bayanta zuwa bedroom d’in,
kwance ya iske ta tayi rub da ciki tana ta faman kuka kamar ranta zai fice.

Cikin mutuwar jiki Mannir ya zauna a kusa da ita a gefen gadon,
ido ya k’ura mata na wani lokaci sannan yayi numfashi mai k’arfi yace ” Zainab wallahi nafi ki buk’atar san kasancewa a kusa da Na’e……………

Kai ta d’ago a d’an zafafe tace ‘ idan ka fini san kasancewa dashi mai yasa ka kasa bin duk wata hanya dan ganin ka kawo shi gidan nan?

” Zainab ya kamata ki gane Naseer yana da matsananciyar zuciya da kafiya gami da taurin kai tun yana yaro, kuma a wannan zamanin ko d’anka na cikinka yak’in soja bayayi sai dai mulkin farar hula da campain da komai dan matuk’ar kace zakayiwa yaranka dole a wannan zamanin zaka ba dai-dai ba.

” Dole sai dai mu biyo mishi ta bayan gida ta inda bai tab’a tsammani ba.

” Kamar yaya kenan kake nufi?

” Sai dai mu sace Na’eem!!!

Da sauri Zainab ta mik’e zaune tana murmushi had’i da goge hawayenta ” yawwa this is a good idea, amma ta yaya kake ganin zamu iya sace shi tunda kasan akwai securities da yawa?

” Duk yawan securities sun isa su hanani shiga gidan,
tunda gidan ubana ne, tare da Ikram, Na’eem yake kwana a bedroom d’in ta, zanje gidan da sassafe around 6:00am duk suna bacci sai na d’auko shi, idan na dawo gida sai nayiwa securities d’ina kyakykyawan warning akan kar su sake su bar kowa ya shigo min gida kai tsaye.

Cikin zak’uwa Zainab tace ” yaushe zaka je ka d’auko shin?

Shiru yayi yana tunani wajen 10 minutes sannan yace ” dole sai dai jibi.

Fuska ta b’ata tace ” mai yasa bazaka je gobe ba,
har sai jibi?

” Dole muyi komai cikin tsari da tunani saboda,
kar muyi gaggawa mu lalata komai,kinga yau naje gidan har munyi cacar baki dashi,
idan aka ga babu Na’eem yau, dole ni za’a zarga,
amma idan muka tsara komai cikin tsari, batare da mun bar wata shaida ba babu wanda ya isa ya fito gar da gar yace mune ko da sa hannunmu.

Rungume Mannir Zainab tayi cike da murna da matsanancin farin ciki tace ” thank you so much my love,
light kiss yayi mata a kumatunta yace ” don’t mind my heart make you happy is my duty.

BAYAN KWANA BIYU

Yau ta kama ranar tafiyar su Naseer k’asar Holland ce shida Na’eem,
tun dare ya gama shirinsa tsaf dan k’arfe 6:00am na safe jirgin su zai d’aga,
ya shirya kayansu tsaf tun dare ya saka duk wani abu da zai tafi dashi a boot d’in mota,
a daren ya cewa Ikram ta shirya Na’eem around 5:00am na safe, dan baya son yayi late kuma gashi yana san ya biya ta kabarin Zarah yayi mata addu’a,
dan bai sai ranar dawowar shi Nigeria ba.

Tun k’arfe 4:30am na safe Naseer ya tashi yayi wanka ya shirya cikin wani tsaddaden d’anyan boyel sky blue mai shegen kyau,
ya saka takalmi, hula, agogo ash color, kallo d’aya zaka yiwa kayan jikinsa ka hango tsadar kayan,
Naseer yana bala’in san manyan kaya, dan shi kwata-kwata k’ananan kaya basu dame shi ba, bama shi dasu in dai ba irin simple d’innan na zaman gida ba,
shi dai yasaka Shadda, Boyel, Material na maza, d’an yan yadi sannan zai san ya saka kaya.

Lokacin da yana karatu a Holland abokanansa har tsukanarsa suke sosai suna ce masa sarkin k’abilanci,
k’arfe 5:00am Naseer ya fito bayan ya gama shirinsa, kasancewar ya sanar dasu Momy lokacin tafiyar yasa yana saukowa ya iske su gaba d’ayan su a parlor,
da murmushi a fuskarsa ya k’arasa inda mahaifan suke zaune suna jiransa,
har k’asa Naseer ya durk’usa ya gaida su, suka amsa cike da fara’a.

Bayan ya gama gaida su Ikram dake tsaye rik’e da Na’eem tana ta faman kuka, cikin muryar kuka tace ” good morning Uncle,
murmushi yayi yana shafa kanta yana amsa gaisuwar, cikin muryar kuka ta kuma cewa ” yanzu Uncle da gaske tafiyar zakuyi ku barni ni kad’ai ba Zarah, ba Na’eem?

Sosai tausayin Ikram yayi masifar kama Naseer, dan yasan dama dole kewa tayi mata yawa, duk duniya babu wanda tafi sabawa dashi sama da Zarah, gashi yanzu babu ita,
tayi tafiya mai nisan nisa ta har abada, daga baya kuma tayi sabo da Na’eem shima gashi yanzu za’a raba ta dashi kuma Allah kad’ai yasan ranar dawowar su,
kuma yarinyar tayi masifar sanin ya kamata, dan duk wannan hargitsin dayake faruwa a tsakanin shi da iyayenta bata tab’a shiga ba,
ba kuma ta tab’a nuna masa komai ko a fuskarta bane,
dan haka yake mugun santa da tausayinta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button