GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Kasa ce mata komai yayi, ci gaba da kukan ta tayi, a hankali ya jawo ta jikinsa ya rungume ta sosai, take shima ya fara zubar da hawaye, gaba d’aya jikin kowa a wajen yayi mugun yin sanyi, a hankali ya zame jikinsa daga Ikram ya karb’i Na’eem,
juyawa wajen su Momy yayi yana hawaye muryarsa na rawa yace ” Momy, Dady zan tafi lokaci na k’urewa kar nayi late,
rungume shi suka yi su duka suna hawaye ” Allah yayi maka albarka, ya tsareka ya kuma baka kariya, dan Allah ka kula da kanka, da Na’eem, da kuma addininka, al’adarka ta k’arasa maganar tana fashewa da kuka.

Hawayen dake zubowa daga idan Momy ya goge mata,
shima yana hawaye muryarsa na rawa yace ” in sha Allah Momy zan kula sosai,
kan Naseer Dady ya shafa yana murmushi hawaye na zuba yace ” Allah ya baka sa’a ya d’oraka akan mak’iyanka.

Dakyar Naseer ya iya cewa ” Amin ya Allah nagode sosai Momy,& Dady, ya fad’a yana goge hawayen dake zubo masa, yayi saurin fita,
ai Ikram na ganin ya fita da Na’eem ta durk’ushe a wajen had’i da fasa rikitaccen kuka,
dakyar Mamy ta rarrashe ta ta kaita bedroom d’inta, sannan suma suka wuce nasu bedroom d’in.

Naseer na fita ya shiga mota driver yaja, direct kabarin Zarah ya fara nufa,
yakai wajen 15 minutes a kabarinta yana kuka had’i dayi mata addu’a,
sannan suka nufi Aminu kano international airport,
driver ya ajeshi ya shiga ciki d’auke da Na’eem a kafad’arsa.

Misalin k’arfe 6:00am na safe Mannir yazo gidan,
ganin ba kowa a parlor ne yasa shi zama akan sofa yana san ya gani ko akwai wanda idansa biyu,
ganin yakai wajen 15 minutes amma bai ji motsin kowa bane ya sashi mik’ewa cikin sand’a ya nufi bedroom d’in Ikram.

Daga bakin k’ofar bedroom d’in nata ya rink’a jiyo kamar motsi,
tsayawa yayi ya d’an saurara had’i da kasa kunnensa ajikin k’ofar,
sheshshekar kukan Ikram yaji yo daga cikin bedroom d’in,
da sauri ya tura k’ofar ya shiga, a k’asa ya ganta a zaune ta d’ora kanta akan bed tana ta faman kuka,
da hanzarinsa ya k’arasa gare ta.

Hannu yasa ya d’ago ta yana kiran sunanta ” Ikram lafiya kuwa, meke damunki?

Cikin kuka ta fad’a jikinsa tana cewa ” Dady na shiga uku, ba Zarah ba Na’eem,
gaban Mannir ne yayi wani irin razanannan fad’uwa a kid’ime yace
” meya same Na’eem d’in?

“Dady sun tafi sun bar ni,

Iya tashin hankali Mannir ya shige shi, dan a tsammaninsa wani mummunan abu ne ya samu Na’eem d’in,
take zuciyasa ta shiga bugawa da tsananin k’arfi,
kirjinsa ya d’auki dokawa, yayinda yake jin kamar k’irji sa zai tsage,
gaba d’aya jikinsa ya d’auki kerrrrrrma da tsananin rawa,
jikinsa na b’ari gami da tsuma, cikin rawar murya yace ” me ya same shi?

cikin muryar kuka tace ” Na’eem da Uncle sun tafi Holland, a zabure ya saki Ikram ya mik’e tsaye,
Muryarsa na cracking yace ” yaushe suka tafi?

” Yau zasu tafi, d’azu suka tafi airport, bai k’ara bi takan Ikram ba ya fito a kid’ime ya shiga mota had’i da figarta a 360 yayi Airport,
da mahaukacin gudu ya shiga Airport d’in, yana yin parking ya fito a rud’e ko tsayawa rufe motar bayyi ba ya fito ya nufi reception,
amma ina ya riga da ya makara,
yana zuwa jirginsu Naseer na d’agawa zuwa k’asar Holland.

Wata ma’aikaciya dake aiki a Airport d’in ya tambaya ” please yau she jirgin Holland zai d’aga?

Murmushi tayi had’i da cewa sun riga da sun tashi yanzu 5 minutes ago, hannu Mannir ya d’ora aka ya durk’ushe a wajen gami da fasa rikitaccen ihuuuuuu da kuka,
gaba d’aya hankalin jama’ar dake gurin yayo kansa, take ma’aikatan wajen suka zo wajensa suna tambayar shi abinda ke damusa,
amma ko kallan inda suke bayyi ba,
, sai da yayi kuka iya san ransa sannan ya tashi ya shiga mota ya wuce gida jikinsa a matuk’ar sanyaye,
shi ko tunanin Zainab bayyi ba ta kansa kawai yake,
baima tsaya tunanin abinda zai ce mata ko halin da zata shiga ba,
saboda kwata-kwata baya cikin hankalin sa da nutsuwarsa.

Yana yin parking ya fito baima tsaya rufe motar ba, Zainab na bedroom akan bed a kwance sai juyi take cike da farin ciki,
tana jiran dawowar Mannir da Na’eem,
tana jin tsayawar motarsa ta fita da gudu,
a parlor sukayi kicib’us dashi,
tana murmushi ta tare shi dan ita tsammaninta tare da Na’eem zata gansu,
ganin yanayin dayake ciki,
kwata-kwata babu alamar nutsuwa a tattare dashi, kallo d’aya zakayi masa kasan yana cikin mummunan tashin hankali.

Cikin rawar baki tace “Mannir lafiya,
ya banganka da Na’eem d’in ba?

Bai ko kalli inda take ba yana ci gaba da tafiya yace ” sun tafi Holland shi da Naseer,
ya fad’a yana shigewa bedroom d’in sa,
anan Zainab ta zube a k’asa had’i da fasa rikitaccen kuka mai tsuma zuciya, ta rink’a ihuuuuuu tana kuka kamar ranta zai fita.

Mannir na shiga d’aki ya fad’a kan bed had’i da fasa kuka, yana jin kamar zuciyarsa zata fashe,
saboda tsananin zafi da zugin da take yi masa, dan ji yake tamkar an raba shi da ransa ne,
sai da taci kuka sosai harta fara shid’ewa sannan ta mik’e dakyar tana had’a hanya ta nufi bedroom d’in Mannir,
tsaye ta iske shi ya dafa bango yana ta faman zubar hawaye,
a fusace ta k’arasa inda yake taci kwalar rigarsa tace.

” wallahi ka shirya ka tafi Holland yau ka kawo min Na’eem idan ba haka ba mutuwa zanyi,
saboda tsananin b’acin ran da Mannir yake ciki, kuma kwata-kwata baya cikin hankali da nutsuwarsa rufe Zainab da duka yayi haik’an kamar zai kashe ta.

Dan gani yake kamar ita ta jawo komai, kuma gashi tazo tana neman k’ara mishi zafi bayan wanda yake ciki,
dakyar Zainab ta kwaci kanta ta gudu bedroom d’in ta,
sai dare sannan Mannir yaje bedroom d’inta ya rarrashe ta sosai, daga k’arshe suka rungume juna suna kuka.

HOLLAND ????????

Da misalin k’arfe 3:30am jirgin su Naseer yayi landing a k’asar Holland ,
dayake Naseer ya riga yasan k’asar sosai kasancewar acan yayi karatunsa na wajen 7yrs,
shiyasa sai da yayi booking komai, har gidan da zai zaune ya rigada ya gama dashi,
Dayake su ranting (haya) gidajensu ba irin namu bane, idan kayi hayar gida zaka samu akwai komai na gida babu abinda babu dai-dai da cokali akwai,
duk wani abu na gida akwai, everything.

Yana fitowa yaga taxi driver sa d’auke da sunansa a board NASEER MUSTAPHA,
direct wajensa ya nufa, tafiyar 40 minutes sukayi daga Airport kafin su isa gidan Naseer, a k’ofar gidan an rubuta NASEER MUSTAPHA 128A,
gidan mai kyau dan an k’ayata shi da kayan alatu na more rayuwar duniya,
gidan 3 bedroom maka-maka, kowanne bedroom akwai toilet & bathroom, sai makeken parlor da kitchen, dinning area, daga waje kuma akwai swimming pool, da garden, irin dai gidajen nan da kuke gani a films d’in turawa, gidan ya had’u iya had’uwa.

Dama tun daga Nigeria ya riga da yayi booking nursing nanny da zata rink’a kula da Na’eem 24hrs, dan haka a gidan yazo ya iske baturiyar mai suna Rose wacce a k’alla zata kai 45yrs ba,
da sauri ta mik’e ganin Naseer ta gabatar da kanta, simple smile yayi mata,
had’i da mik’a mata Na’eem, da bedroom d’aya yace ta d’auke shi, ya kai mata kayan Na’eem can.

Washe gari da ya fita siyayya, ya jibgowa Na’eem iyayen kayan wasa dana sawa, da motoci, machine na yara irin masu amfani da battery, banda lilina daya kwaso, da Teddy’s d’aki guda ya ware ya shiryawa Na’eem kayan wasa.

Sosai Na’eem yayi b’ul-b’ul yayi kyau, dayake yana samun ingantacciyar kulawa, dai-dai da swimming pool sai dai Naseer ya zubawa Na’eem kayan a ciki dayake kullum da yamma sai sunyi wanka a ciki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button