
BAYAN SHEKARA UKU
Sosai Na’eem ya girma yayi wayo ga shegen surutun tsiya kamar aku dan yanzu ya kusan 4yrs,
har lokacin Naseer bai kuma waiwayar Nigeria ba, sau uku su Momy, Dady, Ikram na zuwa Holland wajen Naseer,
duk k’arshen shekara sai sun zo, duk sanda suka zo sai sun so tafiya da Naseer da Na’eem amma yak’i dan a cewarsa shida aure da Nigeria har abada.
Sosai Na’eem ya saba da Rose dan Momy ma yake ce mata shi a tsammanin shi itace Momyn shi,
tare suke komai da ita sun saba sosai.
Duk ranar Friday Naseer da Na’eem ke zuwa shopping,
yau ta kama Friday wajen 7:30pm suka tafi Sharaton dake birnin Holland,
tun da suka shiga gaban Naseer ke muguwar fad’uwa, tsoro da fargaba suka shige shi lokaci d’aya
Na’eem nata zuba mata surutu da unnnnnnn hmmmmmm un’un kawai yake binsa,
bayan sun gama siyayyar da zasuyi kaf har sun tafi wajen biyan kudi Naseer ya tuna bai sai perfumes ba,
dan haka ya juya wajen dake d’auke da perfumes,
Dior wanda tun bayan rasuwar Zarah ya koma amfani dashi ya shiga nema,
idansa ne ya sauka akan wani guda d’aya daya rage a wajen.
Da sauri Naseer ya mik’a hannu zai d’auka,
hannunsa ya d’ora akan na wata mace da itama Dior d’in tazo siya,
jin electric shock ta jashi yasa Naseer saurin d’auke hannunsa daga kan nata had’i da d’aga kai ya kalle ta.
Take zuciyarsa ta buga da tsananin k’arfin gaske, gabansa yayi mugun razanannan fad’uwa, yawon bakinsa ya k’afe ganin ZARAH tsaye a gaban sa,
cikin rawar baki Naseer yace ” ZARAH!!!!…….
MOMYN ZARAH
[17/02, 02:54] Atk: GADAR ZARE!!!
(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)
~NA~
HAUWA A USMAN
JIDDARH
????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
GARGAD’I
MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA
~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO
BEST FRIEND FOREVER & EVERZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~
60
ZARAH!!!!,
bayanta ta juya taga ba kowa, dan haka tayi tsammanin ko ba da ita yake ba,
hannu ta kuma kaiwa zata d’auki turaren Dior, aiko caraf Naseer ya rik’e hannu ta, yana zubar da hawaye yace ” dama kina raye Zarah? ,
kina raye amma kika b’oye kanki?
kin san irin wahalhalun da faman dana sha, ya k’arasa maganar hawaye na zubo masa.
Hannunta ta kwace had’i da cewa ” who are you please?
Tsaida kukansa cak Naseer yayi yana kallanta yace “Do you mean baki sanni ba?
“Ok naji kamar kai ma d’an Nigeria ne, kuma bahaushe ko?
Da hanzari Naseer ya rik’o hannun Na’eem yana nuna mata a gigice duk ya rud’e ya fita daga hankalinsa yace ” kinga Na’eem d’in mu, ya kalli Na’eem yana nuna masa ita yace ” ga Momynka,
ya fad’a yana k’ok’arin rungume ta.
Hankad’a shi baya tayi a fusace tace ” how dare you?
” Don’t ever try to touch my body, Useless man ta fad’a tana jan tsaki mtwwwwwwwww,
had’i da k’ok’arin barin gurin.
Da sauri Naseer yasha gabanta yace ” me kike nufi Zarah?
A fusace tace ” wai wacce banzar ce Zarah?
da zaka dame ni akanta, ni sunana LISAH, kuma ban san ka ban kuma tab’a ganin ka ba, kai ni ko me kama dakai ma ban sani ba!.
Naseer na kuka ya nuna ta yace ” yanzu nine baki sani ba Zarah?
to idan ni baki sanni ba, I am sure you know him ya fad’a yana nuna Na’eem,
tunda shi ke kika d’auki cikinsa har tsawon 9 months sannan kika haife shi kika kuma shayar dashi.
Tsaki tayi gami da cewa Mad man, ta kuma zagaye shi zata bar wajen,
da k’arfi Naseer ya fizgo ta jikinsa a fusace yace ” ke kin isa ki k’ara tafiya ki barni, banza marar alk’awari,
tauuuuuuu ta d’auke shi da mari ranta a tsananin b’ace tace ” banza d’an iska kai yanzu ko kunya baka ji ba,
kana Hausa Fulani kuma Muslim amma ka rungumi macen daba muharramar ka ba a bainar jama’a.
Shima ransa a b’ace yace Ni kike cewa banza d’an iska Zarah?
ni kike cewa ba muharraminki ba?
to ki sani koda zaki canja komai a rayuwarki, baki isa ki canja zuciyar ki da kuma igiyoyin aure na dake kanki ba.
Kasancewar k’asar Holland akwai security take jama’ar dake wajen suka kira police suka sanar dasu halin da ake ciki,
Lisah nata k’ok’arin kwace kanta daga rik’on da Naseer yayi mata amma ta kasa,
ana haka police suka shigo.
Naseer ganin za’a kwace Lisah daga hannunsa yasa shi rik’e ta gammmmm yak’i sakinta,
take ya birkice ya zama cikekken mahaukaci tuburan ya zage yayi ta hauka yana tik’ar uban dambe da police d’in,
dakyar aka kwaci Lisah daga hannun Naseer, ganin an kwace ta yasa Naseer bud’e baki yana gunjin kuka yana cewa ” she is mine, please don’t let her go.
Ganin Lisah ta shiga mota zata tabi su yasa Naseer sakin rikitaccen kuka da tsananin k’arfi yana cewa ” please Zarah karki barni, karki kuma tafiya a karo na biyu ki barni,
idan a baya na iya jurewa yanzu bazan iya ba,
please don’t leave me Zarah I love you please Zarah,
amma ina ita Lisah ma gaba d’aya tsoransa ya gama kamata, gaba d’aya jikinta kerrrrrma yake.
Driver na jan motar Naseer ya durkushe a wajen had’i da sakin rikitaccen kuka,
police d’in suka danna shi a mota suka nufi police station dashi, sai da Rose tazo tayi belinsa sannan suka sake shi,
koda Naseer ya koma gida direct bedroom d’in sa ya wuce Na’eem na tayi masa magana amma ko kallan sa bayyi ba, ya wuce bedroom had’i da dannawa k’ofar key.
Kan bed Naseer ya zube ya shiga tunani tabbas da hannunsa da kuma kanshi ya saka Zarah a kabari,
to amma ya akayi haka ta kasance danshi yasan wannan Zarah’n sa ce,
domin irin bugun da zuciyarsa keyi masa a duk lokacin daya kasance da ita,
ko kuma take kusa in da yake irin bugawar zuciyara tayi masa a lokacin daya shiga Sharaton,
sannan irin reactions d’in dayake ji aduk lokacin daya tab’a jikinta kota tab’a nashi irinsa still yaji a lokacin da hannunsa ya sauka akan nata.
Sannan her best perfume is Dior still yanzu ma shi taje siya,
yama za’ayi ace masa wannan ba Zarah’n sa bace,
a fili yace ” that is impossible,
mik’ewa yayi zaune had’i da yin tagumi da duka hannayen sa ya tallabo fuskarsa,
tunani ya kuma yi, tabbas yasan matuk’ar Zarah ce babu yadda za’ayi ta ganshi ta nuna kamar bata san shi ba,
yasan ko loosing memory tayi shine mutum na farko wanda idan ta ganshi nan take zata dowa hayyacin ta,
kuma ma a ganin da yayi mata babu alamar ciwon komai a tattare da ita,
Cikin cikekken hankali da nutsuwarta ya ganta,
ajiyar zuciya ya sauke da k’arfi had’i da tunanin mafita,
zuciyarsa ce ta bashi amsa da cewa mafita d’aya ce shine ka zama inuwarta, duk inda tasa k’afa ta cire ya zamana kai ka maida taka ta haka ne kad’ai zaka san gaskiyar wacece ita.
Dan tabbas yasan there is something behind,
dan yasan haka kawai babu yadda za’ayi Zarah ta ganshi amma ta nuna kamar bata tab’a sanin shi a rayuwarta ba,
tunawa ya kuma yi da marin da tayi masa,
a fili yace ” Banza d’an iska
yasan babu yadda za’ayi Zarah ta iya d’aga hannu ta mari koda wani ne balle shi, balle kuma harta iya bod’e baki ta zage shi,
haka dai Naseer ya kwana yana sak’a da warwara har garin Allah ya waye.
Washe gari ranar Saturday, around 6:40pm Naseer na kwance Na’eem ya shigo bedroom d’insa da gudu, dan tun jiya da abin ya faru bai kuma fita ko k’ofar parlor ba, balle waje,
yana bedroom d’in sa yana ta tunane-tunanen abinyi, sai kuka yake ya kasa dainawa, muryarsa harta dishe saboda kukan fitar hankalin dayake, dafa
kansa Na’eem yayi yana cewa ” sweet Dad are you okey?