
Da sauri Naseer ya goge hawayensa, dan yasan matuk’ar Na’eem yaga hawayensa to fa ba zaman lafiya,
dan Na’eem yana tsananin san Naseer, kwata-kwata ya tsani duk wani abu da zai saka Naseer a damuwa,
idan yana k’aunar mutuwar sa yana san yaga hawayen Naseer,
wasu lokutan idan Naseer ya tuna Zarah yana kuka, Na’eem zuwa yake yana goge mai hawaye shima yasaka kuka sai dakyar ake iya rarrashinsa,
idan ko ya ganshi a damuwa ya rink’a tambayar sweet Dad waya b’ata maka rai,
kowaye bazan barshi ba,
idan na girma sai na rama maka na b’ata mishi ran shi ma,
hakan kuwa yana yiwa Naseer masifar dad’i had’i da sashi cikin farin ciki har yaji kamar he is the best father in the whole world.
Murmushi Naseer yayi had’i da cewa ” I’m absolutely fine son,
dariya Na’eem yayi had’i da cewa ” amma sweet Dad ya baka chirya ba?
” In shirya kuma, ina zamu?
Fuska Na’eem ya b’ata cike da shagwab’a yace ” sweet Dad ka manta ko?
Kai Naseer ya d’aga alamar tunani yana murmushi yace ” ayiwa Dad afuwa ya manta a taimaka a tuna masa,
K’afa Na’eem ya d’an shura had’i da cuno baki yace ” yau fa Saturday,
“Ok I’m so sorry Son yau akwai zuwa shan ice cream ko?
“To har yanzu banyi late ba, bari na shirya sai mu fita,
dariya Na’eem yayi yana cewa ” my best Dad.
Ba tare da b’ata lokaci ba Naseer ya shirya cikin boyel riga da wando, da hula suka fita,
diret Hilton garden suka nufa, bayan sun siya sun biya suna fitowa Naseer ya hango Lisah na shigowa,
take duk ilahirin jikinsa ya d’auke kerrrrrma had’e da tsuma, gaba d’aya jikinsa rawa yake yana shaking,
take zuciyarsa ta shiga bugawa da tsananin k’arfin tsiya,
bai san sanda ya saki hannun Na’eem ya nufe ta,
a baya Na’eem ya biyo shi.
Gabanta Naseer yasha had’i da k’ura mata ido yana hawaye,
cikin matsanancin kuka Naseer yace ” please Zarah me mukayi miki a rayuwa ni da Na’eem da zakiyi mana haka?
” Why Zarah, kin san irin mahaukacin son da nake miki, kin san bazan tab’a iya jurewa rashin ki,
ya zube bisa gwiwoyinsa a gabanta, dai-dai lokacin da Na’eem ya k’araso wajen, ganin Dadynsa yayi kneeling down yasa shi ma yin kneeling down d’in kamar yadda yaga Naseer yayi had’i da rok’on hannun Naseer, shima ya fara kuka dan matuk’ar Na’eem yaga Naseer yana kuka shima sai yayi.
Cike da tsananin mamakin gaske Lisah ke kallan su,
Naseer yace ” please Zarah ko ba danni ba, kodan Na’eem ki dawo gare mu dan girman Allah, kar laifin wasu ya shafe mu kiyi mana horo abisa laifin mak’iyan mu, ki tuna duk duniya baki da kamar mu,
wannan d’anki ne ni kuma mijin kin, ya k’arasa maganar yana k’ara fashewa da rikitaccen kuka,
ita dai Lisah tsayawa tayi sororo tana ganin ikon Allah abu kamar a film,
cike da tsoro Lisah tace ” wallahi Allah bawan Allah ban san ka ban tab’a ganin ka, ban ma san akan me da wa kake magana ba.
A zuciye Naseer ya mik’e had’i da rik’o ta cikin matsanancin b’acin rai yana zubar hawaye yace ” wallahi karya kike yi Zarah,
kece Zarah ta, bugun da zuciya take min a halin yanzu ba k’arya bane,
shi kad’ai ya isa ya shaidata min ke Zarah tace ta gaskiya,
Zarah so ba k’arya bane, san gaskiya na tsakani da Allah har bada baya tab’a canjawa,
idan ke ba Zarah ta bace babu yadda za’ayi zuciya ta rink’a bugawa a duk sanda na ganki,
idan ke ba Zarah ta bace babu yadda za’ayi body reaction d’ina ya rink’a’ canjawa a duk sanda na tab’a jikinki.
“Zarah ana kama sak da sak a duniya sosai har murya har movements d’in ku ya zama iri d’aya da mutum amma banda bugawar zuciya da kuma soyayya,
hannu ya d’ora akan saiti zuciyarsa yace ” wannan bugawar da zuciya ta keyi yana yi ne domin ke kad’ai Zarah, bayan ke babu wata ‘ya mace da zuciya ta ta tab’a bugawa akanta kamar haka,
sannan ya d’ora hannunsa a saitin zuciyarta yace ” wannan bugun da zuciyar ki keyi kad’ai ya isa ya shaidamin ke Zarah ta ce,
domin zuciyar mu d’aya ni dake, a take suke bugawa, matuk’ar tawa tana bugawa da k’arfi haka kema taki zata kasance tana bugawa da k’arfin.
Hannu Lisah tasa ta hankad’a Naseer baya a zafafe tace ” waye kai, daga ina kake, ina ka sanni? da kake neman shigowa rayuwata kake neman matsa min,
wallahi ban san ka ba, ban kuma tab’a ganin ka ba,
tana kai nan ta watsar da ice cream d’in had’i da ture shi tayi waje da gudu.
Sunkuyawa Naseer yayi had’i da duba ice cream,
a fili Naseer yace ” vanilla flavour , Zarah’s best flavor,
har lokacin Na’eem bai daina kuka,
har suka koma gida kuka yake, sai da kyar Naseer ya samu ya rarrashe shi, yasha ice cream d’in sannan yayi bacci.
Washe gari kwata-kwata bayyi niyyar fita ba,
yana kwance akan bed yajiyo Rose na fama da Na’eem, sai daru yake akan bazai je school ba sai yaga Dadynsa,
sanin halin Na’eem da tsinanniyar kafiya da shegen taurin kai yasa shi mik’ewa dole ya zura jallabiya ya fita zuwa parlor,
Na’eem na ganinsa ya tafi da gudu ya fad’a jikinsa,
cikin maganar sa ta yara yace ” Sweet Dad, kaji Mom wai na tafi school ban gan ka ba,
kansa ya shafa had’i da k’ak’aro murmushin dole,
dan yasan Na’eem da shegiyar tambayar tsiya idan ya ganshi a haka ya rink’a damunsa kenan da tambayar abinda yake damunsa,
yace ” yauwa my son, gara daka tsaya kaga Dadynka,
dariya Na’eem yayi yace ” Dady gayi min alkawayi tiya jaka kai ni school yau,
murmushi Naseer yayi yace ” kayi hak’uri son, ka bari sai gobe na kai ka,
k’afa Na’eem ya shiga diddirawa a k’asa had’i da tab’a fuska zayyi kuka.
Da sauri Naseer yace ” ya haka kuma son?
“Ni dai gacciya Dady cai ka kai ni,
kai ne fa kace babu cau cab’a alkawayi.
” Ni na fad’a Son amma yau ayi min uzuri please son, kuka Na’eem ya fara had’i da ajiye school bag d’in akan sofa yace ” to ni ma na faca zuwa,
dariya Naseer yayi yace ” ayi haka kuwa son?
“cocai ma, cewar Na’eem, bayi ka gayi ma bacci zanyi, sosai Na’eem ya bawa Naseer dariya, ganin yadda ya rufe ido yana jan mun shari wai shi bacci yake,
har da sakin hannu,
d’aukarsa cak Naseer yayi yana cewa ” oh my son, Dad d’in naka zaka yima wayau, to muje na kai ka,
dariya Na’eem yayi had’i da yiwa Naseer peck a kumatu yace ” thank you sweet Dad.
Naseer na driving amma gaba d’aya Na’eem ya isheshi da surutun sa,
wani ya bashi amsa wani kuma ya kyale shi, har suka k’arasa school d’in, light kiss Na’eem ya k’ara yiwa Naseer a kumatunsa yana cewa ” I love you Dad,
murmushi Naseer yayi had’i da cewa ” I love you too Son,
tsayawa Naseer yayi yana kallan Na’eem har ya shige school d’in,
murmushi yayi had’i da girgiza kansa yana mamakin tsananin wayon Na’eem,
zai ja motar kenan ya hango Lisah na fitowa daga cikin motar ta tare daya wasu cuties baby’s boy & girl.
Tsayawa Naseer yayi cak had’i da k’ura mata ido, magana suka tsaya suna yi da yaran amma baya iya jiyo abinda suke cewa,
dariya yaga tayi had’i dayi musu kiss, tsayawa tayi har suka shige cikin school d’in sannan tayi murmushi ta shiga motar ta taja,
Naseer na ganin taja motar ya rufa mata baya, yana binta batare data sani ba.
Binta Naseer ya rink’a yi a baya batare data sani ba har suka isa gidan su, Naseer na gani tayi parking ta shiga gidan ya fito ya zagaya k’ofar gidan sannan ya shiga motarsa ya tafi.
Tun daga ranar ya zama inuwarta ya zama duk inda take yana wajen, duk inda k’arta ta taka k’afar Naseer na wajen, data saka k’afarta a waje ta cire Naseer zai mayar da tasa, ya rink’a bibiyar da bibiyar lamuranta,
sosai Naseer yake nazarinta yana karantar halayyarta amma kwata-kwata ya rasa makama balle hanyar dazai b’ullo mata.