
Naseer na haka ranar Mother’s day tazo, dan haka Naseer ya shirya wani plan,
ya shirya Na’eem sosai yayi masa kwalliya, d’aukar shi yayi yaje wajen siyan gift ya sai duk wani abu da yasan best choice’s d’in Zarah ne har da Dior da chocolate da ice cream ,
sannan ya had’a pics d’inta ita da Zainab da Ikram da Mannir dashi Naseer d’in,
ya siyi wani gift na love wanda akayi bututu kamar haka jiki don’t cheat, betray, in true love, love your husband madly, & true love never end
Ya sa aka saka masa pics d’insu wanda dauka suna dariya su biyu,
sannan ya siyi wani gift wanda uwa ke d’auke da babynta ta k’ura masa ido tana hawaye shima anyi rubutu kamar haka a jiki no one loves you like the way your mother do! She is ur First Love, when she knows she is pregnant she cry because of happiness, and when you come to the world she is going to do the same , when you get pain she will cry, when you get sick she feel like she is sick too that is mother’s true love….
So why dont you love me Mom?
I love you sweet Mom NA’EEM
HAPPY MOTHER’S DAY
Naseer ya had’a gift d’in waje d’aya sannan ya saka mota ya kai shi har wajen da take a paradise island ya nuna mishi ita daga nesa ya bashi flower yace ” idan kaje ka durk’usa a gabanta ka mik’e mata flower da gift d’innan kace I LOVE YOU SO MUCH MOM,
sannan kace mata come back home Mom kana kuka kaji son Naseer ya fad’a yana share hawayen idonsa, yayi kukan ne dan ya saka Na’eem dan yasan matuk’ar yayi kuka shima sai yayi,
aiko take Na’eem ya fara kuka, had’i da nufar wajenta.
Na’eem sarkin wayau beyi mistake ko d’aya acikin abinda Naseer ya koya masa ba,
yana zuwa gabanta yayi kneel down yana kuka yace ” I LOVE YOU SO MUCH MOM, please come back home,
ya fad’a yana mik’e mata flower da gift d’in.
Zumbur ta mik’e tsaye had’i da………..
MOMYN ZARAH
[17/02, 02:54] Atk: GADAR ZARE!!!
(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)
~NA~
HAUWA A USMAN
JIDDARH
????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
GARGAD’I
MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA
~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO
BEST FRIEND FOREVER & EVERZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~
61
Zumbur ta mik’e had’i da kallan Na’eem cike da matsanancin mamakin yadda yaro k’arami kamarsa ya iya yin hakan,murmushi tayi had’i da cewa ” who told you I’m your mother?
Hawayen fuskarsa ya goge cike da shagwab’a yace ” my sweet Dad.
Fuska ta b’ata had’i da cewa ” I’m not your Mother, your Dad has lied to you.
Mik’ewa Na’eem yayi yana kallanta yace ” My sweet Dad has never lied to me,
I know him, I know his habit and characters, he is a good man,
he never lie to anyone !!!
Ganin yaron yana neman b’ata mata rai da lokaci yasa Lisah yin tsaki mtwwwwwwwww,
had’i da juyawa tana niyyar barin wajen,
da sauri Na’eem ya rik’o hannunta cikin nasa yana cigaba da kukansa bil hak’k’i da gaskiya yace, “Please Mom don’t leave us, we need you, most especially me,
Mom ban tab’a sanin dad’in uwa ba,
ban tab’a kwana dake in the same bed ba,
ban tab’a cin abinci dake in the same plate ba,
baki tab’a yin wasa dani ba,
My sweet Dad ne kawai yake min duk wannan, Mom I need more from you please.
Take tausayin yaron yayi mugun kamata, a hankali ta durk’usa a gabansa,
tasa hannu tana share masa hawayen sa dake zubowa tace,
” I’m telling you the truth, am not your Mom,
but I wish to be your Mom,
ta fad’a tana shafa kansa, a hankali ta mik’e tabar wajen,
duk abinda ke faruwa akan idon Naseer,
dan haka yana ganin tabar wajen ya fito daga inda yake b’oye yana goge hawayensa,Na’eem kawai ya d’auka ya juya batare daya tsaya d’aukar gift d’in ba,
ya shiga motar had’i da figarta a 360,
yayi gida.
Kasancewar Naseer ya zama inuwar Lisah yasa yasan duk inda take zuwa da lokacin da take zuwa,k’arfe 8:00pm na dare ya shirya ya nufi new world coffee,
sanye yake cikin d’anyen material boyel na maza fari k’al, ya sanya takalmi, agogo da link golden color, ya sanya hula fara mai kwallaiyar golden ajiki,ya d’auki key d’in motarsa ya fita.
Zaune ya hango ta sanye da doguwar riga ta atamfa red color ta sanya bag & shoe black,
ta d’ora k’afa d’aya kan d’aya tana shan coffee d’in dake gabanta,,
bakinsa d’auke da sallama ya k’arasa gare ta,batare data d’ago kanta ba ta amsa sallamar,
bai damu da yadda tayi ba, dan haka yaja d’aya daga cikin kujerun ya zaune had’i da k’ura mata ido.
Jin an zauna, an kuma k’i yin magana yasata d’ago kai cike da tsiwa dan Lisah akwai tsiwa,
a fusace tace ” how dare yo……………
maganar ce ta mak’ale mata a mak’ogwaronta ganin wanda ke gabanta,
dan sosai Lisah ke tsananin tsoran Naseer,,,
take tsoro ya kamata gaba d’aya jikinta ya d’auki kerrrrrma gami da tsuma,
cikin rawar jiki ta mik’e tana shirin barin wajen,
shiko Naseer hankalinsa kwance ya d’ora k’afa d’aya kan d’aya had’i da k’ura mata ido,,,
ganin yadda jikinta ya d’auki kerrrrrma had’i da tsuma, ga alamun tsoro k’arara a fuskarta ya bawa Naseer dariya.
Bayyi dariyar ba saboda tsabar aji, da kuma tsananin ji da kansa dayake yi,a hankali ya d’an murmusa had’i da cewa ” zauna ki nutsu muyi magana dan nima yau a nutse nazo,
ko kallansa ba tayi ba taci gaba da tafiyarta,
gefe Naseer ya kalla had’i da taune hakoransa da k’arfi, sannan ya mik’e yabi bayanta,da sauri yasha gabanta had’i da cewa ” please Zarah ki saurare ni mana ko sau d’aya ne.
A fusace Lisah ta dake tace ” to hell with you and your Zarah,
take zuciyarsa ta harzuk’o ta fara tafasa tana azalzala,
ta nuna shi da yatsanta tana kallan shi ido cikin ido had’i da cewa ” kasan meyasa ban kai ka k’ara ko na shigar da report akan ba?
“Saboda kai d’an k’asata ne, kuma yaranmu da addininmu d’aya ne,,
abun kunya ne na kai ka k’ara,amma na fahimci kai kwata-kwata baka san haka ba,
baka kula da karar da nake maka ba,
na lura kwakwalwar ka akwai matsala da damuwa a cikin ta,
sannan kanka ba dai-dai yake ba, duk inda nayi kana biye dani, ka matsa min ka takurawa rayuwata,
ka dame ni akan ni matarka ce, wai kuma har mun haihu,
jiya ka turo min yaro, abin tausayi nayi matuk’ar tausayawa yaron harnaji inasan nasan labarinsa,
naji kuma ina sha’awar zama Maman shi I want be his real Mom.
“But gaba d’aya ka hayyace ni ka takura min duk inda nake kana nan,
kana tara mun mutane har kasa ina zargin kai na,
kasa naje ina tuhumar iyaye na akan kona tab’a yin wata rayuwar kafin wannan,
har hospitals naje aka duba min kai na da kwakwalwa ta,
akan kona tab’a samun matsala a baya ko cutar mantau, amma komai normal, naje university d’in danake karatu duk nayi bincike nan ma babu komai,kasan saboda kai duk nayi haka?
Ta fad’a tana ci gaba da kallan kwayar idansa data gama rikid’ewa ta koma red,,
tace ” saboda tsan-tsan gaskiyar danake hangowa a kwayar idanka, ta fad’a tana nuna shi,,
hakan yasani kwata-kwata nak’i yarda da kai na da kuma iyaye na,
da kai na na tsumduma binciken kai na da kai na, but everythings is absolutely fine,,
amma ka dameni ka hanani sakat akan wata banzar Zar………..
tauuuuuuuuu!!! -tauuuuuuu!!!!! Naseer ya d’auke ta da lafiyayyun marika.
Da sauri Lisah ta dafe kuncinta da duka hannayenta,,
tana kallansa cike da matsanancin mamaki, ta kasa cewa komai illa ido kawai data zuba mishi,,,
cikin fushi ya matso daf da ita ta yadda duk suna jiyo numfashin junansu,
ya nuna ta da yatsansa yace ” zan iya jure duk wani cin fuska ko cin mutuncin da zakiyi min,
amma bazan tab’a iya jurar koda d’igon muzanta Zarah bane,
duk abinda zakiyi min ni kiyi min, amma karki sake ki tab’a Zarah,
idan har kuwa kikayi kuskuren tab’a ta anan zaki gane ainshin waye NASEER MUSTAPHA.