
“Duk da bata raye bata duniya bazan tab’a iya jurar a wulak’anta koda sunanta bane,
balle kuma ita kanta,dan bazan tab’a iya jure a wulak’anta min rayuwa ta a gaba na ba, saboda Zarah rayuwata ce,
kinsan me yasa nake bibiyar ki?
Ya tamabaye ta, bata iya koda furta kalma d’aya ba, sai ido kawai data zuba masa,
hannunta ya rik’e had’i da janta batare daya lura da yadda take neman fad’uwa ba,
ya dannata a mota, cikin fushi ya figi motar da tsananin gudu,
cikin matsanancin tsoro da fargaba mai tattare da kid’ima Lisah ta fara k’ok’orin bud’e motar,
amma ina ya riga da yasa luck,
a kid’ime take kallansa cikin rawar murya tace ” ina…….. za……. ka…… kai……. ni?
Bai ko kalli inda take ba yaci gaba da driving d’in sa yana hawayen bak’in ciki,
yana yin parking ya fito baiko tsaya motar ta gama tsayawa ba,
ya bud’e murfin motar da k’arfi ya figi hannunta yayi cikin gidan da ita,
yana zuwa parlor yayi wurgi da ita yana kuka yace ” ke tsammanin ki dan kyanki ko k’irar da Allah yayi miki nake binki,
to kalli kiga dalilin dayasa nake binki,
gaba d’aya parlor pictures d’in Zarah ne manya a kowanne b’angare na parlor,
wasu ma tare sukayi da Naseer,
a hankali Lisah ta mik’e tana bin photos d’in da kallo a matuk’ar razane saboda tsananin kamarta da Zarah,
hanunta ya kuma ja ya shiga da ita kitchen, bedroom, bathroom and toilet, ko ina na gidan sai da ya shigar da ita, amma duk bangon data kalla photos d’in Zarah ne manne da kowanne b’angare da bango na gidan.
Parlor ya kuma dawo da ita yana kuka ya shiga bata labarin Zarah tun daga farko har k’arshe,
ya kuma matsowa daf da ita yana kuka yace ” kece Zarah ta, kece ta jikin wannan photos d’in,
Zarah mai yasa zakiyi min haka?
” why Zarah? ya k’ara fashewa da rikitaccen kuka,
“mai nayi miki?
Cikin kuka Lisah tace ” wallahi ni ba Zarah’n ka bace,
mik’ewa yayi a kid’ime duk ya zare ya gama fita daga hayyacin sa, ya yasa hannu ya yaga rigar jikinsa,,
ya fito da saitin zuciyarsa yace ” kalli yadda zuciya ta ke bugawa, kuma tana yin irin wannan bugawar ne lokacin datake tare da Zarah kad’ai,,
koda duk duniya zasu kasa gane ki, ni zan gane ki, koda a halin makanta ne,
Zarah koda zaki iya yiwa duniya alaye, ni bazaki iyayi min alaye akanki ba,,
koda duk duniya zasu taru suce min ke ba Zarah ta bace bazan tab’a yarda ba.
“Saboda zuciya ta bazata tab’a yi min k’arya ba,
ki kalli yadda zuciya ta ke bugawa da k’arfi,
ji yadda gudun bugawar zuciyata ya k’aru Zarah,
sannan kice min wai bake ce Zarah ta ba.
Lisah na kuka tace ” bani ce Zarah’n ka ba, sai dai idan wani sabon bak’on al’amari ne yake son faruwa da zuciyarka,
cak Naseer ya tsaida kukansa yana kallanta,
taci gaba ” ko kuma dan tsananin kamar da muke yi da Zarah ne yasa hakan ke faruwa,
and I wish to be your Zarah for ever and ever,
gaba d’aya jikin Naseer ya d’auki kerrrrrma, murmushi yayi had’i da kallanta ido cikin ido yace ” haba Zarah ni zaki rainawa hankali, ki tuna cewa ni na raine ki da wayo na tarrrrrr aka haife ki ko kin manta ne?
Kallansa Lisah tayi tana kuka ta bud’e baki zatayi magana kenan Na’eem ya shigo yana kiran ” sweet Dad,,
cak Na’eem ya tsaya ganin Naseer na kuka, a hankali ya kalli Lisah da itama kukan take,
direct wajen Naseer ya nufa yasa hannu yana goge masa hawaye had’i da cewa,
” sweet dad who made you cry?
Murmushin k’arfin hali Naseer yayi yana kallan Na’eem,
Na’eem ya fashe da kuka yana ci gaba da tambayar Naseer meya sashi kuka,
kallansa kawai Naseer yake yi ya kasa cewa komai,
sai da yaga kukan Na’eem ya tsananta sannan ya shiga rarrashinsa yana bashi hak’uri,
cikin kuka Na’eem yace ” sweet Dad idan kana can nayi ciyo cai ka faya min waya saka kuka,
Naseer yace ” please help me ask your Mom why she want leave us? ,
why she didn’t stay and live with us? ,
told her how much we love’s and misses her,
we really need her alot, and why did she play the game like this?
Ya k’arasa maganar yana goge hawayen dake ci gaba da zubo masa,
ganin hawaye na zubowa Naseer yasa Na’eem fasa kuka had’i da nufar Lisah ya shiga hankad’a ta waje yana cewa ” we don’t love and need you, I really HATE YOU, I HATE YOU,
Please go and leave us alone, yana gama fad’a ya hankad’a ta waje ya rufe k’afar parlon,
komawa cikin parlor yayi ya kwanta a jikin Naseer yana ci gaba da goge masa hawayen sa.
A hankali Naseer ya lallab’a Na’eem har yayi bacci,
yaje ya kwantar dashi akan bed d’in sa,
zama Naseer yayi a gefen gadon had’i da k’urawa Na’eem ido yana hawaye, sai daya d’auki lokaci mai tsayi sannan ya tofa masa addu’o’in tsari ya fita ya nufi bedroom d’insa,,
akan bed ya kwanta had’i dayin rigingine fuskarsa tana kallan pop ya tsunduma duniyar tunanin abinda yasa Zarah tayi masa haka a rayuwa,,
yayi tuanani mai zurfi amma ya rasa gano takamaiman dalili kwakkwara koda guda d’aya wanda zai iya saka ta juya masa baya kamar haka,
ganin ya rasa gano dalili koda guda d’aya ne yasa Nasser yi mata uzuri had’i da hak’ik’ancewa a ransa cewar yasan Zarah bazata tab’a yi masa hakanan ba,
tabbas ya tabbatar tana da dalilin daya sata yin haka, dan yasan Zarah bata da munanan halayen dazata iya yin haka, sai dai idan akwai wani dalili ko wata k’unlalliyar a k’asa, da wannan tunanin bacci ya d’auki Naseer.
BAYAN SATI D’AYA
Tunda abun nan ya faru Naseer bai kuma bin Lisah koya mata magana ba,,
ya rigada ya gama k’ulla duk wani abu, ya kuma gama shirya komai,
shi kad’ai yasan me ya tsara,
tun 4:00am na dare Naseer ya shirya ya nufi gidan su Lisah,
a d’an nesa d gidan su yayi parking motarsa, ya zauna zaman jiran fitowar Lisah,,
basu fito ba sai around 7:30am na safe,
sannan Naseer yaga sun fito daga cikin gidan acikin mota su biyu,
amma ya kasa ganin fuskar d’ayar,
Naseer na ganin sun fita, ya fito daga inda yake b’oye ya nufi gidan.
Cikin sand’a ya shiga cikin harabar gidan,
ta window Naseer ya haura ya shiga cikin main house d’in,
parlor ya fara bincikawa ya hargitsa ko’ina ko zaiga wata shaida ko alamar da zata tabbatar masa ta tunaninsa,,
amma baiga komai ba, daga nan yayi kitchen ya shiga duba ko’ina da ina, nan ma ba komai,,
bedrooms d’in gidan ya shiga yayi nema iya nema kamar ransa zai fita amma babu komai.
Dawowa parlor Naseer yayi ya zauna had’i dayin tagumi hannu bibbiyu,,
ya rasa abinda yake yi masa dad’i a rayuwarsa take yaji ciwon kai ya saukar masa, d’aga kansa sama yayi yace “
ya Allah ka taimake ni dan isarka, dan girmanka ya Allah ,
ya Ubangijin kowa da komai ka nuna min gaskiyar al’amarin nan ko zuciya ta zata huta,
ya Ubangijin al’arshe, ya Ubangijin sammai da k’assai, ya Ubangiji samman bakwai da k’asan bakwai ka haskawa zuciya ta idanunwa na, da gangar jikina hasken gaskiya,,
yana gama addu’ar ya mik’e had’i da k’ok’arin fita.
Yana gaf da fita idansa ya sauka akan wata ‘yar wardrobe da akayi kwalliyar flowers ajiki,
a hankali ya nufe ta gabansa na fad’uwa, yana isa gareta ya k’ura mata ido yana tunani,,
a hankali yakai hannunsa jikin books din da aka jera ajikin wardrobe d’in,,
yana tab’a yaga ta fara motsi, wardrobe d’in yaga ta juyi had’i da komaw gefe,
sannan yaga k’ofar bedroom ta bud’e, wani k’ayataccen bedroom mai shegen kyau ya bayyana,
kai tsaye batare da wani tsoro ko fargabar komai ba Naseer ya danna kai cikin bedroom d’in,,
dudduba ko’ina ya fara, amma baiga komai ba,
juyawa yayi yana shirin fita, a hankali wayarsa dake hannunsa ta sub’uce ta fad’i k’asa.