GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

D’an guntun tsaki Naseer yayi had’i da durk’usawa da nufin ya d’auki wayarsa,,
ya kai hannu kan wayar kenan idansa ya sauka akan wani abu dake k’ark’ashin gado,
haka kawai yaji gabansa yayi muguwar fad’uwa,
cikin rawar jiki ya durk’usa sosai had’i da mik’a hannu ya jawo abin,
zaman dirshen Naseer yayi a k’asa had’i da jawo shi gabansa,
gabansa ne ya yaci gaba da tsananta fad’uwa,
jikinsa na tsananin rawa ya bud’e abin,
gabansa ne yayi masifar fad’uwa ganin gift d’in da ya bawa Na’eem yakai mata,
ranar Mother’s day.

Completely gift d’in, shiru yayi na dan lokacin data bar Na’eem, da gift d’in a wajen,
a hankali idan Naseer ya kuma sauka akan Diary hannunsa na rawa ya bud’a Diary d’in yana bud’ewa photos suka zuboo……….

MOMYN ZARAH
[17/02, 02:54] Atk: GADAR ZARE!!!

(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)

       ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

GARGAD’I

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO

BEST FRIEND FOREVER & EVER
ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~

62

Photos suka zubo, jikin Naseer na matsanancin kerrrma had’i da rawa ya durk’usa cikin mutuwar jiki yasa hannunsa dake karkarwa ya d’auki photos din yana dubawa,
take jikin Naseer gaba d’aya yayi collapsing had’e da weak,
ganin picture d’in sa wanda sukayi da Zarah tun kan suyi aure,
jikinsa na tsananin kerrrma yaci gaba da duba pictures din,pictures d’in Na’eem ya gani lokacin yana jariri dai-dai lokacin da Zarah ta mutu,
sai pictures d’in Ikram, Zainab da Mannir.

Jikinsa na muguwar tsuma ya bud’e diary din ya fara karantawa kamar haka….Da fari dai sunana ZARAH MUHAMMAD DAURA,
ni haifaffiyar garin kano ce,ina da yaro d’aya sunansa NA’EEM,,
sai kuma ubana kuma uwata domin shi tamkar mahaifi na dauke shi
ya wuce miji kad’ai a gare ni shi gaba d’aya rayuwa ta ne,
shi kad’ai keda zuciyar Zarah,
NASEER MUSTAPHA!!!

Ai tsayuwar gagarar Naseer tayi, take yaji gwiwoyinsa sun saki,,
k’afafuwansa kuwa kasa d’aukar sa sukayi balle su iya ci gaba da tsayawar saboda tsananin kerrrma da sukeyi,,,
cikin mutuwar jiki Naseer ya zube wanwar a k’asa,,
take numfashinsa ya fara nan d’aukewa,
yayinda Idanuwansa suke neman rufewa dan tuni sun fara gani dishi-dishi,,
lokaci d’aya jin sa ya d’auke kunnensa ya dod’e baya iya jin komai sai shhhhhhhhhhhh,,,
da sauri yasa hannuwansa ya toshe kunnensa dake ta faman yimasa amsa kuwa a cikin dodon kunnensa.

Zube gaba d’aya kayan yayi a k’asa yana bin su da kallon tsoro kamar yaga aljani,,
da sauri ya fara ja da baya yana daga zaunen har yakai ga bango,,
kwata-kwata Naseer baya cikin hankali da nutsuwarsa ya gama fita fit daga hayyacinsa,,
take ya fara tunanin ta yadda akayi hakan ta faru, hannayensa ya d’ago yana kallansa had’i da furta,,
“da wad’annan hannayen na saka ta acikin kabari,
a gaba na akayi mata sutura had’i dayi mata sallah,
ta ya hakan ta faru?

Yayiwa kansa da kansa tambayar,,
shi da kansa ya bawa kansa amsa da cewa lalle akwai wani b’oyayyen abu a k’asa,,
a zabure cikin rashin nutsuwa da hankali Naseer ya mik’e ya dinga neman evidence,,
ko dalilin dayasa Zarah tayi haka,
yana birkita d’akin yana mahaukacin kuka had’i da sambatu shi kad’ai,,
duk yabi d’akin ya hargitsa ya birkita komai,,
had’i da yin jifa da duk abinda yazo hannunsa a matuk’ar haukace Naseer yake yin komai had’i da kukan matuwa kamar za’a zare masa ruhinsa daga gangar jikinsa,,

Gaba d’aya Naseer ya haukace ya zama tantirin mahauci tuburan,,
ya zage ya rink’a tik’ar hauka haik’an,,
ganin ya birkice komai da ko’ina na d’akin amma ya rasa wata hujjar komai yasa Naseer zubewa bisa gwiwoyinsa had’i da sakin uban ihuuuuuuuu da duk gidan sai da ya amsa kuwwa,,
dafe kansa yayi da hannu bibbiyu yana kukan mutuwa tuburan muraran,,
had’i da tsananin mamakin wannan birkitaccen al’amari,,
shi yanzu babban burinsa na farko yana so ya fara gano dalilin dayasa Zarah tayi haka,,
tayi masa wannan mummunan hukuncin akan laifin wasu, laifin daba shi ya aikata ba,,
laifin da kwata-kwata bai kamata ya samu hukuci akansa ba,,
ya rasa dalilin da yasa Zarah tayi masa wannan mugun butulcin.

A kanta babu abinda bayyi ba, babu irin wulak’anci da k’ask’ancin da bayyiwa jama’a ba,,
shi yana san Zarah tsakani da Allah ne badan komai nata da kowa nata ba,,
true love yake mata, wanda shi da kansa ya rasa wanne irin makahon so yake mata,,
wanda akan ta zai iya rufe ido ya tatawa kowa tijara,amma shi Zarah zata guda, shi zata yiwa haka,
akan me tayi masa?
akan wanne dalili?

Hannu Naseer yasa ya dafe kansa had’i da d’aga kansa sama cikin d’aga murya yace ” why Zarah? I don’t deserve all this punishment from you!!!
I didn’t cheat on you, and I didn’t hurt you,,
but why do you cheat me?
why do you hurt me and betrayed me?

” why all this?

” why do you create this drama and scene?

“Why Zarah?

Ya k’arasa maganar cikin rikitaccen kuka mai ban tausayi.

Zarah na school haka kawai taji gabanta yana fad’uwa,kirjinta ya shiga bugawa take tsoro da fargaba suka shigeta lokaci d’aya,,
a hanzarce ta mik’e ta fito da wayar ta kira ta sanar da abokiyar zamanta halin da take ciki,sannan ta kashe wayar, kwata-kwata ji tayi yau bata iya zaman school d’in balle harta iya fahimtar lactures din,
dan haka ta mik’e tayi waje,
direct wajen motarta tayi ta bud’e ta jefa hand bag d’inta sannan ta zagaya ta shiga had’i da yiwa motar key ta nufi gida,,
tana tuk’in gabanta na ci gaba da fad’uwa yayinda zuciyar ta ke bugawa da saurin bala’i,,
tana shiga harabar gidan ta fito,,
ji tayi gabanta yana tsananta bugawa da k’arfi, yayinda matsanancin tsoro da fargabarta suka k’aru.

Cikin mutuwar jiki ta shiga gidan,
tana isa parlor ta tsaya cak, gabanta yayi mummunan fad’uwa ganin duk illahirin gidan an hargitsa shi,,
take zuciyar ta tashiga tsalle tana tsuma kamar zata tsaga k’irjinta ta fito,,
da sauri ta saki hand bag d’inta ta fad’i k’asa,,
da gudu ta nufi secret bedroom d’in ta,
tana ganin k’ofar a bud’e taji mummunan tashin hankali had’i da matsananciyar fargaba,
a kid’ime ta shiga bedroom d’in da gudu, bata lura da Naseer ba, direct ta nufi k’ark’ashin gadon ta durk’usa had’i da lek’awa,,
ganin babu abinda take nema ne yasa ta yin baya da sauri a matuk’ar razane.

Idon Naseer ya sauka akanta,kamar daga sama Zarah taji muryar da ko gigin mutuwa take taji ta zata gane ta,,
dan har abada bazata tab’a mance muryarsa ba.

” Wannan kike nema?
cewar Naseer yana yi mata nuni da diary d’in dake hannunsa.

Iya kid’ima da mummunan razana Zarah tayi,
cikin matsanancin tashin hankali ta kalli inda taji maganar,,
zaune ta ganshi diary da photos d’in a gabansa,,
da k’arfi ta runtse idanuwanta had’i da sauke razananiyar ajiyar zuciya,,
take duk ilahirin jikinta ya d’auki kerrrrrma had’i da tsuma,,
ta zaro gaba d’aya Idanuwanta waje kamar zasu fad’o k’asa,,
tashin hankalin data shiga kuwa bazai tab’a fad’uwa ba,
dan tayi muguwar razana,
a kid’ime ta mik’e tsaye had’i da zuba masa idanuwanta, shi kansa Naseer jikinsa yana rawa ya mik’e tsaye had’i da zuba mata nashi idon,,
wanda yasa ta dole yin k’asa da nata idon,,
hannunshi ya tafa had’i da cewa ” wonderful miss…… sai yayi shiru had’i dayin murmushi yace ” Lisah ko?
“Ko Zarah zan kira ki?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button