GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

“Ni na rasa ma da wanne sunan zan kira ki dashi ZARAH KO LISAH?

“Amma tunda naga kinfi san Lisah bari na kira shi dashi,
Miss Lisah ya fad’a idanshi tarrrr akan ta,

” gaskiya Lisah kin cika jarumar gaske, kin cancanci yabo,
kin cancanci a jinjina miki,A kuma tafa miki,
saboda tsananin halaccinki da amanarki sannan da kuma gaskiya da alk’awarin ki.

“Weldon Miss Lisah master planner, ya fad’a yana tafa hannun.

dakewa Zarah tayi had’i da cewa ” ni fa Malam ban fahimci abinda kake nufi ba please waye ka…………..

Tauuuuuuuuuuuu!!!!!
Kauuuuuuuuuuuu!!!!!

Naseer ya yarfa mata lafiyayyun marika kyawawa guda hud’u wanda suka hana ta k’arasa maganar rainin wayon datayi niyya,,
hannayenta tasa ta tallafe duka kuncinta,,
tana ci gaba da kallansa ido cikin ido,,
duk da itama tasan sanin kanta ne zata iya fuskantar fiye da haka daga gare shi,,,
dan tasan Naseer da shegiyar bak’ar zuciya mai zafi,,
cikin matsanancin b’acin rai ya matso daf da ita yana huci yace,,
” karki sake ki kuma neman raina min hankali ko wayau,,
kinyi wasa da hankali da tunanin na,,
bama iya ni kad’ai ba har iyayen mu Zarah.

“Banza d’an iska, kalmar da kika jefe ni da ita kenen,
Zarah na yarda dake amma kin cuce ni, kin ha’ince ni kinci amanata,
kin yaudare ni, lokacin da kika kira ni da BANZA D’AN ISKA sai na tabbatar wa da kai na cewar bake bace,,
saboda nasan Zarah ta kwata-kwata bazata tab’a iya bud’ar baki ko da mutumin daya girmeta da sati d’aya bane,,
amma zuciyata ta tak’i yarda cewar bake ce Zarah ta ba,
ya k’arasa maganar cikin matsanancin kuka,,
sosai itama Zarah ke kuka kamar ranta zai fita,
a hankali ta durk’usa a gabansa bisa gwiwoyinta taci gaba da rusgar kukanta batare data iya cewa komai ba.

” A lokacin da zuciya ta ci gaba da gaskata min cewa ke Zarah ta ce kin san me nayi?

Ajiyar zuciya ya sauke had’i da share hawayensa yace ” kyautata miki zato nayi,
na kuma yi miki uzuri,,
sannan nace nasan tabbas kina da kwakkwaran dalilin dayasa kika aikata haka Zarah,saboda tsananin son da nake miki yasa na kasa ganin laifinki ko sau d’aya,na kasa kallan ki a matsayi wacce ta munafurce ni,
maimakon hakan ma sai nayi miki uzuri na kuma kyautata miki zato,,
Zarah son da nake miki bai tab’a bari ko sau d’aya na tab’a ganin ki da laifi ba a iya tsayin rayuwa ta,
Zarah san da nake miki yasa na kasa kallan ki a matsayin wacce taci amana ko ta gujeni ba,,
a kullum kwanan duniya ina miki kallan mutuniyar kirki wacce tafi kowacce mace a duniya kyawawan halaye na gari,,
kinsan duk mai ya jawo hakan?

“Saboda sanda nake miki na gaskiya ne,
My love for you is a pure and true love,,
Zarah k’arfin soyayyar gaskiyar danake miki ne ya kawo ni Holland,
dan nazo na iskeki,
soyayyar gaskiyar danake miki ne yasa Allah ya bani ikon zuwa Sharaton ranar,
soyayyar gaskiyar danake miki ne yasa duk sanda na ganki zuciya ta ke bugawa da k’arfi,
bugun zuciyata ya k’aru wanda tun asali yana yi ne dan ke kad’ai,,
Zarah kin san halin dana shiga lokacin da kika barni?

“Haukacewa nayi, na rink’a hauka tuburan,,
akanki nabar k’asa ta, garin mu, tushe na, mahaifa ta, dangi na, ‘yan uwa na, ahalina, da kuma iyaye na,,
Zarah akanki babu irin abin da ban yi ba,
amma saboda ke ba mutum bace kika rasa da abinda zaki saka min sai haka,,
har d’anki na tura miki saboda nasan k’arfin soyayya irin ta d’a da mahaifi am……..

Kasa k’arasa maganar yayi saboda matsanancin kukan daya ci k’arfinsa,,
yana kukan yaci gaba,
“amma saboda tsabar rashin imani kika watsar dashi,
kika gaya masa ke ba Momyn sa bace,
ki duba irin maganganun da Na’eem ya fad’a miki wanda duk uwar da d’anta kamar Na’eem ya fad’a haka dole zuciyar ta ta karye,,
ta tausaya masa, duk girman laifin da akayi mata,,
balle ke da ba laifin zaune bana tsaye, ba’ayi miki laifin komai ba,
amma kika zab’i kibar yaronki d’an 6 months, da mijinki,
duba da k’ananan shekarunsa, ya sanar dake matsalarsa wanda ni danake tare dashi bai tab’a fad’a min ba,,
amma kasancewar ki na uwa rana d’aya ya sanar dake,
amma saboda tsantsar rashin tausayi haka kika juya masa baya,
kika yi tafiyar ki kika barshi a wajen yana kuka,,
har kika cusa k’in ki da k’iyayyarki a zuciyarsa,,
duk da cewar shi yaro ne amma har ya fuskanci kwata-kwata baki san sa, baki k’aunarsa,,
shima yace baya sanki ( he hate you), ya k’arasa maganar hawaye na bin kuncinsa.

Ita dai Zarah tana durkushe ta kasa cewa komai sai tsananin kuka da take yi,,
bata iya furta koda kalma d’aya ba, illa kukan fitar ran da take yi.

Tsananin bak’in ciki ne yasa Naseer durkushewa had’i da fasa ihuuuun mutuwa,,
yana kukan tsananin bak’in ciki da takaicin rayuwa,,
cikin kukan yace cewa.

“Why Zarah?
” mai yasa, menayi miki?

“Why, ya k’ara fashewa da azababban kuka mai cin rai.

Kamar an zabure shi ya mik’e zambur ya shak’i wuyanta,,
had’i da damk’ar gashin kanta,,
kamar zararren mahaukaci,,
a fusace yace ” meyasa Zarah?

” Zarah why?

Daga bayansa Naseer yaji an ce ” leave her, I’m the one that suppose to told you, what is hide in darkness, It’s me that deserve to told you the real secret, and what was happened .

A rikice Naseer ya juya yana kallan inda maganar ke fitowa,
sosai ya kid’ime ganin Doctor JENNIFER a gabansa hard’e da hannuwanta a k’irjinta ……………..

MOMYN ZARAH

[17/02, 02:54] Atk: GADAR ZARE!!!

(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)

       ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

GARGAD’I

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO

BEST FRIEND FOREVER & EVER
ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~

63

Tarrrr Jennifer ke kallan Naseer ido cikin ido ba tare da wani tsoro ko shakkar komai ba,,
cikin mamaki yake binta da kallo bakinsa a bud’e, a hankali ya nunata da d’an tsansa cikin rawar baki yace ” you?

Takowa Jennifer ta fara yi tana nufar Zarah a hankali,batare data kalli inda yake ba tace ” yes Naseer it’s me,,
tsaye kawai Naseer yayi yana kallanta cike da matsanancin mamaki,,
yama rasa abin yi ko abin cewa,gaba d’aya al’amarin ya d’aure masa kansa ya kulle masa kwakwalwar sa,,
sun rikita masa lissafi, had’i da sanya shi a cikin duhu,a hankali Jennifer tasa hannu ta d’aga Zarah daga durkushen data ke,juyawa ta kumayi tayi tattaki zuwa wajen tissue ta d’auko had’i da mik’ewa tace ” wipe up your tears and stop crying,karb’ar tissue d’in Zarah tayi ba tare data iya tsaida kukan datake yi ba.

D’an zaman da Jennifer tayi da Zarah na 4yrs, da kuma zaman da tayi a Nigeria na 3 yrs yasa ta jin hausa sosai kamar yarenta,,Naseer dai kallanta kawai yake cike da mamaki.

Dakyar ya bud’e bakinsa cikin rawar murya yace ” you create all this drama and scenes?

Tsayawa tayi had’i da hard’e hannayenta a k’irjinta tace ” yes Mr Naseer for sure its me, are U’re shock and surprised?

Kallanta kawai Naseer ya cigaba dayi batare daya ce komai ba.

Sai can yace ” but why?

Murmushi Jennifer tayi had’i da cewa ” now you come to the point,
and now you do the right things and good question,
abinda ya kamata ka fara tambaya kenan tun da farko tayi maganar cikin harshen Hausa,,
cike da wani mamakin ya k’ara ci gaba da kallanta,,
murmushi ta kuma sannan tace ” yes, Naseer ina jin Hausa tun a Nigeria,,
kuma cikin harshen Hausa zan baka labarin abinda ya faru.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button