GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Gyaran murya tayi sannan ta fara,

ASALIN LABARIN MUTUWAR ZARAH

” Tun lokacin da aka kawo Zarah bata da lafiya, sanda ta karye,,
naji a raina ina matsanancin tausayin yarinyar duk da tun a lokacin ni na fahimci cewa ba accident bane,
saboda yadda take kuka had’i da sambatu a cikin sambatun da take yi na fahimci cewa duka ne,,
a lokacin na k’ara jin tausayin ta sosai, musamman dana duba k’ananan shekarunta, da kuma juna biyun dake jikinta,,
na duba girman Family irin naku, wanda your father is former Nigerian president,amma naga yadda yarinya k’arama daga Familyn El-mustapha tana cikin irin wannan mawuyacin halin,,
sai nayi tunanen ko she is a house maid,
sai kuma naga yadda ka rude ka gigice ka fita hayyacinka akanta,
sannan naga kyanta da softy skin d’inta,,
sai na tabbatar she is among da Family’s.

“Babu yadda banyi da Zarah akan ta sanar da ni ainahin abinda ke damunta ba amma fir tak’i,at the end dana dameta da tambaya ma sai ta daina min magana,tun a lokacin ta samu hawan jini jininta ya hau sosai, har yakai tun abin na bani mamaki har ya dawo bani tsoro,
na kuma k’ara jin mugun tausayin ta a rai na,
na rasa meye matsalar yarinya k’arama kamarta ‘yar 17yrs,naga dai ku baku da matsalar kud’i, ko wani nakasu ta wajen jin dad’in rayuwa ko kayan alatun morewa duniya, da jin dad’in ta,,
dan nasan ko mafi k’ask’anci daga cikin ma’aikatan gidan ku yafi k’arfin babu da talauci har k’arshen rayuwarsa,,
saboda El-Mustapha mutum ne na mutane, yana da matuk’ar kirki, da alheri, ga tausayi, jin k’ai da kuma taimakon al’umma, nayi tunnani mai zurfi na kasa gano ainahin matsalarta a lokacin gashi kuma kwata-kwata ta daina bani fuska balle nasa ran jin damuwarta.

” A haka har Allah yasa Zarah ta samu lafiya karayarta ta warke sumul har aka sallameku daga asibitin,
tun daga nan ban k’ara jin labarin Zarah ko na kuma ganinta ba sai ranar da aka kawo ta haihuwa,,
a lokacin da aka kawo ta haihuwa na ganta a galabaice, ta gama fita daga hayyacin ta sosai,,
kuma jininta yayi mugun hawa,,
sannan a lokacin abinda ya hana Zarah haihuwa da kanta zuciyar ta ce ta kumbura, zuciyar ta a kumbure shine dalilin da yasa ta kasa haihuwa da kanta,
a wannan lokacin ne na k’ara tabbatar wa there’s something wrong,
tun daga nan nayi tunanin akwai wani mummunan al’amari dayake faruwa da yarinyar,
na bak’in ciki, ko k’uncin rayuwa to dan haka na sakawa rai na kota halin yaya sai naji labarinta na kuma taimake ta,
a lokacin nayi iya yi na
amma tak’i gaya min komai, haka a wannan lokacin na hak’ura akan dole batare da na samun abinda nake san samu ba.

Haka a wannan lokacin ma aka kuma sallamarku,
har zuwa lokacin da aka kuma kawo Zarah hospital a karo na uku,,
a wannan lokacin zuciyar Zarah ta riga da ta gama tab’uwa sosai dan 60% ta lalace,,
al’amarin da yayi mummunan tsora tani kenan ya d’aga min hankali na,
ganin mummunan halin da yarinya k’arama ke ciki,,
sai lokacin a wannan lokacin naci nasara Zarah ta sanar dani halin da take ciki,
bayan kun kawo Zarah asibiti an shigar da ita emergency.

EMERGENCY ROOM

Ajiyar zuciya Doctor Jennifer ta sauke bayan ta gama kallan scanning report d’in da akayiwa Zarah,,
a hankali Doctor Jennifer ta jawo kujerar ta zauna had’i da zubawa Zarah ido kawai batare data ce mata komai ba,,
sai da tayi kusan 10 minutes sannan ta kuma sauke ajiyar zuciya had’i da kiran sunanta ” Zarah,,
kai Zarah ta juyar daga kallan Doctor Jennifer dan tasan maganar da Doctor Jennifer kesan yi mata,,
bata kula da yadda Zarah tayi mata ba taci gaba da magana.

” Zarah ki taimaki kanki da rayuwarki ki fitar da abinda ke ranki yana damun rayuwarki,
wanda har ya kai ga yiwa rayuwarki mummunar illa haka,
ya jawo miki ciwon zuciya,
a matuk’ar razane Zarah ta juyo tana kallan Doctor Jennifer,,

“Yes Zarah kalli kiga kiga yadda kaso 60 cikin 100 na zuciyar ki ya lalace,,
cewar Doctor Jennifer tana nunawa Zarah scanning d’in, sannan gaki da ciki, duka-duka yaushe kika haihu amma gaki nan da wani cikin har na 3 months,,
cikin mummunan kid’ima Zarah ta mik’e zaune had’i da cewa ciki?

Kai Doctor Jennifer ta d’aga mata alamar eh,
a razane Zarah taci gaba da kallanta tana hawaye,,
mik’ewa daga kan kujerar Doctor Jennifer tayi ta koma kan bed d’in ta zauna a gefen Zarah had’i da dafa kafad’arta,
cikin sanyin murya Doctor Jennifer tace ” ki daure ki amaryar da abinda ke cikinki ko kya samawa kanki cikakkiyar nutsuwa da kwanciyar hankali,ki yarda dani zan taimaka miki da abinda nasan zan iya, dan Allah ki daure ki sanar dani damuwarki.

Runtse ido Zarah tayi tana zubar da hawaye,,
a hankali tace ” haka kawai na yarda dake har naji zan iya sanar dake damuwa ta,
na kuma ji lokaci d’aya na aminta dana gaya maki sirri na, daga nan Zarah ta sanar da Doctor Jennifer komai na rayuwarta, tun daga zuwan mahaifinta kano, har zuwa auren shi da mamanta,
har zuwa labarin cikin Na’eem, da auren su da Naseer, da labarin Zainab da Mannir,
babu abinda Zarah ta iya b’oye mata, tana maganar tana kuka harta gama.

Doctor Jennifer tun da Zarah ta fara bata labarin rayuwarta take kuka,
sannan matsanancin tausayin Zarah ya k’ara ratsa zuciyar ta da gangar jikinta,
hawayen ta share had’i da janyo Zarah jikinta ta rungume batare data iya furta koda kalma d’aya bace,, taci gaba da kukanta kawai,,
daga ita har Zarah kukan suke babu mai rarrashi wani,,
sai da sukayi kukan su har suka gaji sannan Doctor Jennifer ta d’ago kai ta kalli Zarah,
a hankali ta share mata hawayen ta had’i da cewa,

” kiyi hak’uri duk abinda kika ga ya samu bawa muk’addari ne daga Allah, sannan kuma jarabawarsa ce haka,
dan Allah baya tab’a barin bawa batare da ya jarrabi imanin sa ba,
ki godiya ga Allah abisa jarrabawar da yayi miki,
ki kuma yi addu’ar Allah ya baki ikon cinye jarabawarki,
ke taki kalar jarabawar kenen baki san kalar ta wasu ba,
ina da shawara da mafita d’aya idan zaki yarda da ita.

Da sauri ta tsaida kukanta had’i da k’urawa Doctor Jennifer ido, batare datace komai ba.

Doctor Jennifer taci gaba da magana ” ban sani ba ko zaki yarda ba ki amince da hakan ba,
dan bani da tabbacin zaki yarda,
amma wannan ita kad’ai ce mafita,
da sauri Zarah tace ” fad’i muji ina jinki.

Ajiyar zuciya Doctor Jennifer ta sauke had’i da cewa ” mutuwar k’arya zakiyi,

“Kamar ya? cewar Zarah cikin rashin fahimta,

” kinga yanzu kina da shigar ciki har na 3 months, sannan ga ciwon zuciya,,
to matuk’ar kina san tsira da lafiyarki da kuma rayuwarki dole ne kiyi nesa da Familyn ki,,
har na wani lokaci ta yadda gaba d’ayan su zasu san darajarki da kuma k’imarki,,
ki koyawa kowa hankali,
sannan kiyi nesa da su, ki dage ki nemarwa kanki damarki,,
sannan ki kwatarwa kanki ‘yanci,
kuma ki………..

Zarah ce ta dakatar da ita ta hanyar cewa ” ni fa ban gane abinda kike nufi ba, ki fito sak a mutum kiyi min bayani.

Murmushi Doctor Jennifer ta yi sannan tace ” ai ina kan magana ta ne, kamar yadda kika ji nace kiyi mutuwar k’arya tun farko to haka nake nufi,,
allura zanyi miki wacce take saka mutum suman 24hrs,
idan nayi miki allurar sai na fita na shaidawa Family ki cewar kin mutu,,
bayan anyi miki sutura da jana’iza sai ni kuma naje na tuno ki,
yau dama saura na just 2 weeks na koma Holland,
idan zan tafi sai na tafi dake can ayi miki ingantaccen magani sannan a baki kulawa ta musamman,
hope kin fahimci abinda nake nufi yanzu?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button