GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Zarah wacce tunda Doctor Jennifer ta fara magana ta saki baki kawai tana kallanta sororo kamar wata tab’abb’iya cike da mamaki,,
har ta dasa aya, murmushi Zarah tayi had’i da cewa ” ke a tunaninki yanzu nabar yaro na d’an 6 months da mijina, dangina da iyaye na na biki ko me kike nufi?

“Yes of course cewar Doctor Jennifer,
murmushi Zarah ta kuma sannan tace ” laifi na ne dana biyeki na sanar dake sirrina,
ke yanzu a ganinki da tunanin ki wannan adalci ne nayiwa kaina,
nabar kowa nawa na biki, ke da ban sanki ba, ban San ainahin wacece ke ba,
ban san k’asarku, yaranki, addinin ki ba, kawai sai na biki,
to wai ma duk ba haka ba tayya ma zan yarda dake?

” Nasan dama dole kiyi tantama akan maganata,
kasancewar yanzu kwata-kwata duniya ba yarda da amana ta zama abin tsoro,
dole kiyi shakku akaina,
sannan ni ‘yar k’asar America ce,
cikin garin Holland,
sannan ni musulma ce kamar ki, ana dai kira na ne da Jennifer ko Janny saboda shine ainahin sunana,
a hankali Doctor Jennifer ta rik’o hannun Zarah cikin nata, had’i da kwantar da murya tace ” tun ranar dana fara ganin ki naji ina sanki, with no reasons,
naji kuma ina tsananin tauyawa rayuwar ki, har naji ina san na taimaka miki,
Zarah ki yarda da ni bazan tab’a cutar ki ba,
bazan kuma tab’a cin amanar ki ba,,
kawai dai ina san nayi miki gata ne,
na zame miki uwa kuma ya,,
Zarah ki rufawa kanki asiri ki nisanci wannan family tun kafin su kashe ki ko su illata rayuwar ki,,
wallahi wallahi wallahi Allah, na rantse miki da girman Allah bazan tab’a cutar dake kona ci amanarki ba,
Allah ya sani zanyi miki haka ne dan nayi maki gata sannan na kwatar miki ‘yan cinki.

Haka Doctor Jennifer taita kwad’aitawa Zarah zuwanta Holland da kuma amfanin zuwan nata,,
da kuma fa’idar nisantar ahalinta,
sai da Doctor Jennifer tasha wuya sosai kafin daga k’arshe dakyar Zarah ta yarda ta amince da shirin Doctor Jennifer.

Sai da tayi mata allurar da 10 minutes sannan ta shaidawa su Naseer cewar ta mutu,
bayan an kai Zarah kabarinta an binne Doctor Jennifer tabi dare taje ta hak’o ta,
takai ta gidan ta, ta kwanta, sai da akayi good 7hrs da hak’o Zarah sannan ta farka daga doga dogon suman datayi tana ambaton sunan Naseer.

Da sauri Doctor Jennifer ta isa gare ta,
had’i da bata ruwa tasha, sannan takai ta bathroom tayi wanka ta shirya taci abinci.

Washe garin ranar Doctor Jennifer ta fara yiwa Zarah shirye-shiryen tafiya,,
da neman visa,
bayan sati biyu suka d’aga zuwa Holland,
bayan 2 weeks da zuwan su Doctor Jennifer ta samarwa Zarah Admission a University of Holland ta fara karantar gynecology (likitan mata).

Bayan Doctor Jennifer ta gama bashi labari ta juya ta kuma kallan shi tace ” yanzu Zarah she is gynecologist Doctor dan yanzu haka ma tana aiki a hospital d’in danake aiki,
sannan tana wani course ne a halin yanzu.

Murmushi Naseer yayi had’i da cewa ” you leave me with no reasons Zarah,
anan kwata-kwata babu wani babban dalilin da zai saka ki barni har tsawon 4yrs,,
duk soyayyar danake miki ta tashi a banza kenan,
Zarah you cheat me,
you hurt me and you disappointed me,

Zubewa Zarah tayi a gabansa had’i da fasa rikitaccen kuka tace,
” wallahi nima ina sanka, ban kuma yi haka da nufin na cutar dakai kona ci amanar ka ba,
nayi haka ne danna nemana mafita, dan Allah kayi hak’uri nasan nayi maka laifi mai girma,
but please forgive me, please Naseer ta fad’a tana rik’o k’afafuwansa.

Wancakalar da ita yayi gefe had’i da matsawa baya da sauri,
cikin b’acin rai yace ” karki kuskura ki k’ara tab’a ni,
Zarah kwata-kwata bana buk’atar ki a rayuwata ta gaba,
baki da wani abu da zaki gaya min da zai sa na saurare ki,
baki da abinda zaki kare kanki dashi,
babu wani abu da zai sa na saurare ki,
baki da abin cewa Zarah ya fad’a yana share hawayen dake zubo masa,
yace ” abin da matuk’ar ciwo idan makusancinka ya cutar da kai,
amma ba komai.

Yana kaiwa nan ya juya ya nufi hanyar fita,
ya kai bakin k’ofa yana gaf da fita cikin matsanancin kuka da rawar murya Zarah tace ” bazaka saurare ni ba koda nace na haifa maka cikin dana taho dashi, bazaka yafe min ba koda na sanar dakai ina tare da YARANKA (‘YA’YANKA)?………………

MOMYN ZARAH
[17/02, 02:54] Atk: GADAR ZARE!!!

(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)

       ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

GARGAD’I

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO

BEST FRIEND FOREVER & EVER
ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~

64

Cak Naseer ya tsaya batare daya juya ba,,
ganin ya tsaya ne yasa Zarah cikin muryar kuka cewa ” eh Naseer na haifa maka cikin dana taho dashi,,
kuma twins Allah ya bamu mace da namiji,,
na sawa namijin sunan Dadynka MUSTAPHA ana kiransa da NAWAF,,
ita kuma macen na sa mata sunan Momynka MARYAM, ana kiranta da NURR,,
Naseer Allah ne kad’ai yasan meya b’uye a tsakanin mu,,
Allah kad’ai yasan dalilin dayasa ya raba mu har tsawon 4yrs,,
ni dai nasan tabbas Allah baya tab’a yin abu babu dalili,wallahi Naseer nima ba’a san rai na ne, nayi nesa da kai ba sai dan dole,
ta k’arshe maganar cikin matsanancin kuka.

A hankali Doctor Jennifer ta tako gaban Naseer ta kalle shi had’i da sauke ajiyar zuciya kana tace,,
“” Naseer kai kanka kad’ai ka sani, Ita kasan halin bak’in ciki da mawuyacin halin data shiga akan nesa datayi dakai?

” garin Allah bai tab’a wayewa dare ya kuma yi ba tare da Zarah tayi matsanancin kuka akan Ka ba,tun ina rarrashinta har na gaji na hak’ura na dai na,na saka mata ido dan na fuskanci abin nata ya wuce so, so,
ya zama ciwo,,
Ni baturiya ce naga soyayya iri daban-daban amma ban tab’a ganin tsananin so, da alk’awari irin na Zarah ba,tasha wuya sosai kafin ta iya saita kanta,
dan wallahi Allah sai da Zarah ta kusa samun tab’un hankali akan ciwon sanka.

A hankali Doctor Jennifer ta taka izuwa bakin wata wardrobe ta bud’e ta d’auko wani file tazo gaban Naseer ta mik’a masa,,
tace ” karb’i ka gani da idanta irin halin da itama ta shiga akan mahaukacin son da ta keyi maka,
ita da tasan ma kana raye kenan, tasan kuma kana nan cikin koshin lafiya,,
haka ta rink’a bibiyarka.

“Sannan kai a zatonka kai ka ga Zarah?

” To idan ma zaton ka kenan ka dai na,,
domin Zarah ce ta ganka, itace ta kuma bayyanar da kanta a gare ka.

“A zatonka kai ke bibiyarta?

“To nan ma idan zato kake ka daina domin ita ce ke bibiyar rayuwarka.

Kasan ya akayi hakan ta faru?

Shiru kawai Naseer yayi had’i da hard’e hannayensa a k’irjinsa ya zuba mata ido yana kallanta.

Doctor Jennifer taci gaba ” bayan Zarah ta haifi su Nawaf,,
sai tayi masifar tada hankalinta akan ita dole sai ta koma Nigeria wajenka,
babu yadda banyi akan na rarrashe ta na hana ta tafiya amma fafur ta kafe tak’i,,
haka akan dole na hak’ura na fara k’ok’arin naima mata ticket,,
Allah bai sa ta kai ga tafiya ba nasamu labari daga wajen abokanan aiki na hospital cewar tun bayan mutuwa Zarah kabar Nigeria kuma baka kuma komawa,bayan na sanar da ita halin da ake ciki,,
Zarah ta shiga mummunan tashin hankali dan kwata-kwata ta daina ci ta daina sha balle walwala,
hakan dana gani ne yasani tafiya Nigeria dole dan na gano k’asar daka tafi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button