
MOMYN ZARAH
[21/01, 04:12] +234 701 517 2910: GADAR ZARE!!!
(IT’S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)
~NA~
HAUWA A USMAN
JIDDARH
????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
GARGAD’I
MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES , SU KARANTA BA
~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO
9
“Bayan anyi min test aka dawo dani, Doctor ya tabbatarwa da alk’ali ina da tab’in hankali, kwakwalwata ta tab’u wanda hakan ya haifar min da ciwon kai me tsanani ,bayan Dr ya gama yiwa alk’ali bayani sannan ya mik’awa alk’ali takardun .
, alk’ali ya duba sosai kuma ya gamsu, bayanin alk’ali ya gama yan duba dubensa da zaiyi ya yanke min hukunci zama a sabitin mahaukata dake kurkuku (prison) na tsawon shekara biyu, tare da shaidawa jama’ar dake kotun cewa idan na gama shekara biyun babu wani sauran hukunci a kaina kotu ta sake ni.
Daga kotu kai tsaye (Prison) aka wuce dani, Yasmeen nata kuka, nazo na wuce ta gabanta ko kallan inda take banyi ba sbd bana ‘cikin natsuwata da haiyacina , bayan an kaini prison, na samu kulawa sosai ban sha wata muguwar wahala ba can , kasancewar ni a hospital din nake.
Ko a gidan yari banida da wani aiki sai kuka, da tunani ahlina dana rasa kona nay ta ihu ina kiran sunan Mama da Ramlat ko Ja’afar da Umar, sosai wani lokacin idan abin ya fad’o masa ko ya tuna yake hauka tuburan, na rame na koje, tsabar tunani da tashin hankali.
gaba d’aya na fita daga hayyacina Sai sambatu iri iri nake a game taskon rayuwa r dana tsinci kaina ciki .
, Na tara k’asumba da gemo, kwata-kwata bana magana idan zaka shekara akaina aka na yi min magana bazai kalle ka bama balle na tanka maka, haka wani lokaci zakajini cikin dare ina ihun Ina buge buge da kira sunan Sanata Sambo ….ka cuceni ka zalinceni karabani da ahlina danafi kauna fiyye da komai ka maidani maraya karfi da yaji mara galihu adoron kasa .
daman Haka fadar gsky zatayi da rayuwata?
Hk son kwatar yanci zatayi sanadin tabarbarwa duniyata da tarwatsa rayuwata ?
Meyasa…?
meyasa zaka min hk ?
Sai km ya fashe da wani matsanancin kuka me tsanani da cin rai tare da taba zuci
BAYAN SHEKARA 2
Cikin ikon Allah Abdul ya fito lafiya lau, ya warke sumul babu abinda ke damunsa, sai matsanancin bak’in ciki da damuwa, da kuma wutar d’aukar fansa dake k’ara ruruwa a zuciyarsa in every second, koda Abdul ya fito bai bayyanawa kowa da duniya fitowarsa ba, ya b’oye kansa, babu abinda yasa gaba sai bincikin inda zai samo Sanata Sambo.
Tsakiyar ‘cikin wata dokar daji Abdul yasamu yayi Buka tare da kebe kasan Daga shiga ‘cikin mutane burinsa bai wuce yaga tagayyara rayuwar Sanata da dansa ba ..cikin wannan mahaukacin daji yacigaba rayuwasa shikadai .
Shiryawa yayi cikin dare, yayi shiga yadda babu mai gane shi, y nufi unguwarsu, a k’ofar gidan su ya tsaya, gaba d’aya an canjawa gidan tsari an mayar dashi gidan zamani sosai harda bene, gizo Mama, Ramlat, suka fara yi masa sosai yake ganin su a cikin idonsa, Ramlat na ihu cikin kuka take kiran sunansa, muryar Mama ya jiyo ta “Abdullahi karka zo, karka zo Abdullahi ko kai kad’ai ne ka rayo danka d’aukar mana fansa.
Sosai Abdul ya kwanta a wajan yana birgima a k’asa yan ihun kuka kamar ransa zai fita, ihu yake sosai yana sambatu kamar mahaukaci, kasancewar tsakar dare ne yasa babu wanda ya ganshi, ko ya gane shi, wani tsoho dake kwance a soron wani gida ya jiyo ihun Abdul, a hankali ya fito da touch light a hannunsa, har ya zo kan Abdul amma bai sai anzo kansa,b a dafa shi tsohon yayi yace ” yaro lafiya? Kasancewar Abdul ya canja kama kuma ya tara k’asumba yasa tsohon bai gane Abdul ba, sai da tsohon yayi magana sosai sannan Abdul ya jishi, ya kuma dawo hayyacinsa, mik’ewa yayi bai yiwa tsohon magana ba yayi tafiyarsa, tsohon ya bishi da kallo me tattare da tausayawa .
Sosai Abdul ya shiga bincike akan Sanata Sambo da Haidar, Har Allah ya bashi ikon gano komai,da inda zai same su ‘cikin sauki batare daya wata wahala ba sannu a hankali Abdul ya fara bin diddiginsu, tare da bin bayan su duk inda suka shiga, cikin sa’a Haidar ya fito da yammacin shi kad’ai a mota, .
Farinciki yakama Abdul sbd Ga dama tasamu bbu securities bbu kowa shi kadansa sai da Abdul ya bari yaje inda ba jama’a sannan ya jefa masa lemo wanda oready ya caccaka k’usa,ajiki Allah kuma yasa tayar motar Haidar ta taka,take motar taja birki kiiiiiiiiiiiiiii ta tsaya cak.
Shit abinda haidar ya furta kennan tare da daura kanshi akan sitiyarin motar yana takaici.
da sauri Abdul ya fito Daga motarsa ya bude motar haidar ya damki wuyansa ‘cikin mazakunta ya rufe mishi baki yayi cikin kungurumin daji nan dashi.
Kasancewar Abdul mai k’arfi gaske ne, yayinda shi kuma Haidar duk shaye-shaye ya tsotse shi, yasa Haidar d’aukarsa cak aka, sai da Haidar yayi uwar tafiya me nisa dashi sannan ya isa Inda bukkarsa dake tsakiyar daji take wacce yake rayuwa acikin ta, yana zuwa bakin bukkar yayi wurgi da dashi, ya hau dukan Haidar ta ko’ina kamar zai kashe shi, kasancewar gaba d’aya zuciyar Abdul ta k’ek’ashi ta bushe bbu tsoro bbu fargaba ballanantana tsoro .
Yana cikin dukansa Sanata Sambo ya kira wayar Haidar dake aljihunsa, hannu Abdul yasa ya ciro wayar, yana duba screen din wayar yaga sunan Dad,yana yawo .
murmushi mugunta Abdul yayi ya d’aga wayar ya kara a kunne, cikin fad’a Sanata Sambo ya fara magana ” bana ce maka karka sake ka fita ba, dan ubanka, bana hana ka fita kai kad’ai ba escorts ba, kasan fa muna da mak’iya kuma kai koyaushe a buge kake, komai yana iya faruwa dakai.
Wata irin mahaukaciyar dariya Abdul ya saka har da buga kafarsa daya sannan yace ” kaji jaki mutun kai kanka kasan baka da gaskiya, kuma kasan kana da mak’iya musamman ma ni, dan nasan nafi kowa k’inka da ahlinka a hanlin yanzu duk duniya baka da wani mak’iyi daya wuce ni, yadda kamar ni ma bani da kowa haka zan mayar dakai baka da kowa, a duniya yanzu zan aiko maka da gawar tilon d’anka dan kaima ka fara d’and’anar abinda nake ji.
Sosai Sanata Sambo yayi muguwar firgita, hankalinsa yayi kololuwar tashi, saboda tsabar tsorata sai da yayi taga taga ya kusan fad’uwa , cikin rawar murya yace ” Abdul kai ne ?
Yaushe ka fito har da bansani ba ?
kayi hak’uri dan girma Allah kada ka kashe min tilon dana zan gaya maka komai, please karkayiwa Haidar komai, sosai Abdul yayi dariya yace ” ka kashe maciji ka manta baka sare kansa ba, yana fad’ar haka ya kashe wayar, in banda hello babu abinda Sanata Sambo ke ciwon yi duk ya firgita.y asona fita sense dinsa .
Cikin kuka Abdul ya kalli Haidar yace ” mai mukayi muku? Idan ni nayi muku laifi mai ‘yan uwana sukayi muku ni ya kamata ku kashe ba su ba, .
Basu da laifin komai akan lamarin Amman kashe min su .
cikin tsoro Haidar yake magana ” wallahi ni ban san komai akai ba, kallonsa Abdul yayi yace ” bazan kashe ka ba, amma zanci gaba da rik’eka anan har sai mahaifinka ya kawo min kansa, cikin rawar murya Haida yace ” to, amma dan Allah karka cutar dani, ko kallan sa Abdul baiyi ba ya tashi ya d’aure shi sosai,a jikin wata katuwar bishiya sannan ya fita, direct kasuwa ya nufa, risho ya siya da tukunya, bokiti, ludayi, kasko, da dai sauran kasan buk’ata na gida, wajen masu kayan miya ya ya fara siya, jikin shi ne ya bashi ana kallon sa, a hankali ya jiya, dammmm!!! gaban sa yayi wata irin muguwar fad’uwa ganin Yasmeen tsaye ta kafa masa ido ko k’iftawa batayi,.
idonta duk sun cicciko da kwalla, shima ido ya k’ura mata ya kasa kawar da kansa daga kanta, cikin rawar murya, a hankali maganar can k’asan mak’ogwaro tace” Abdul, sai lokacin ya dawo hayyacinsa, kansa ya d’auke daga kallonta ya b’ata fuska, yaci gaba da siyayyarsa, gabansa ta dawo idonta na zubar da ruwan hawaye tace ” Abdul me nayi maka?