GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan na gano kana nan Holland ne yasani dawowa cike da d’oki na sanar Zarah,,
ranar tayi farin ciki sosai, tun daga ranar ta shiga binciken ka,
da kuma inda kake zaune,
sai da tasha bak’ar wahala sosai na wajen 2yrs sannan ta gano ka, gidan ka komai naka.

” A ranar da Zarah ta fara ganin ka tasha kuka sosai kamar ranta zai fita dan sai da ciwonta ya tashi,
yi tayi kamar zata mutu ta rink’a shid’ewa.

“A lokacin kasan meyasa bata bayyanar maka da kanta ba?

“Saboda akwai rikici matuk’ar ita ta fara bayyanar maka da ita hakan yasa dole muka shirya maka GADAR ZARE,,
ya zama na cewar kai ne ka ganta ka kuma fara yi mata magana.

Tun daga wannan rana kullum Zarah sai taje gidan ka,,
wani lokaci ma acan take kwana,
makarantar daka saka Na’eem can ta saka su Nawaf da Nurr, sannan ta had’a su friendship a tsakanin su,,
kuma kullum sai taje taga Na’eem kuma daga nan take had’a masa lunch box d’in sa,,
kuma ita ke bashi abincin kullum a baki.

Kasan me yasa bai gane ta ba?

Shi dai Naseer ba baka sai kunne,

” Saboda b’adda kama take (basaja) canja kama take,,
sannan taje masa.

” Kasan me yasa take canja kama kafin taje masa?

Ta kuma tambayar Naseer, batare data jira amsarsa ba taci gaba.

” Saboda ta tabbatar da cewa Na’eem yasanta a photos,
ta kuma san Na’eem yana da wayo sosai da shegen surutu matuk’ar ya ganta a kamanninta na gaskiya sai ya gane ta.

” Kana tsammanin duk mafarkin Zarah ko gizonta dakake gani ba itace a zahiri ba?

” To ba mafarki bane ba kuma gizo take yi maka ba,
itace a zahiri take zuwar maka cikin barci,
bayan mutuwar Zarah a Nigeria baka ganta ba?

“Tazo maka kamar gizo, ranar da akayi rigima akan Na’eem,,
to a lokacin ma ba gizo bane ita ce a zahiri,
ranar da jirgin mu zai tashi zuwa Holland ne,
ta tubure akan bazata tab’a iya tafiya batare data je ta ganka ba,
kuma tana san ta d’auko Diary d’inta da photos d’in familyn ta,,
babu yadda banyi na hanata zuwa ba, saboda ina tsoran kar asiri ya tonu amma ta nace dole sai da taje ta ganka.

Haka ma a gidan ka na nan Holland kusan kullum Zarah sai taje ta kwana acan,,
kota kwana a bedroom d’in ka kota kwana da Na’eem.

“Ranar da Na’eem ya kai mata gift ranar Mother’s day nasha wuya sosai kafin na samu kanta dan kusan mutuwa tayi saboda tsananin kuka,,
Naseer Zarah na tsananin sanka, da k’aunarka,
itama tana sanka da zuciya d’aya,
her love to you it’s pure and true love,
she really love you so much Naseer,
Wallahi Zarah zata iya sadaukar da komai akanka da kuma farin cikinka Naseer.

Shiru Naseer yayi kawai yana sauraren Doctor Jennifer dan shi kwata-kwata wannan surutun nata ba shigar shi suke ba,
dan wannan bai isa hujjar da Zarah zata iya kare kanta dashi ba,,
sai lokacin Naseer ya tuna abubuwa da dama, wannan dalilin ne yake sa kullum Na’eem baya cin abincin lunch box d’insa kenan,,
kenan duk mafarkan da yake yi da Zarah a gaske suke faruwa,
zahiri ne, shiru yayi yana tunani sosai sai can ya sauke ajiyar zuciya,
Batare daya kalli ko d’aya daga cikin su ba,
Naseer yace ” ina ‘ya’yana (yara na)?

Kafin d’aya daga cikin su ta bud’i baki tayi magana ta bashi amsa,,
su Nawaf da Nourr sun shigo da gudu,,
ganin yanayin Doctor Jennifer da Momyn su yasa su yin turussss,,
a hankali suka nufi wajen Zarah,
Nawaf yace ” Momy what wrong with you?

Nourr tace ” Sweet Mom who make you cry?

Bata basu amsoshin tambayoyin su ba, illa nuna musu Naseer da tun shigowar su yayi kneeling down yana kallan su,,
gaba d’aya yaran da Cindo a hannayen su suma,
sannan ga tsananin kamar da macen (Nourr) keyi da Momynsa,,
Namijin ma (Nawaf) kamar an tsaga kara shi da El-Mustapha Dadynsa, sosai yaran ke tsananin kama da iyayensa.

Cikin muryar kuka Zarah ta nuna musu NASEER tace ” This is your Father,
da sauri Nawaf yace ” what Sweet Mom u mean he is our Dad?

Kai ta gyad’a musu kawai, batare data iya furta koda kalma d’aya ba, Nour tace ” I know him, he’s our Father’s friend Na’eem .

” Yes, and I’m Na’eem’s mother,
I’m his Mom like you,
he’s my blood son.

“What, but Sweet Mom are you kidding and us?

Kafin Zarah ta kuma cewa wani abu,,
Doctor Jennifer tayi saurin cewa ” its not kidding or joke,
he is your real Dad, let me show you evidence,
ta fad’a tana d’auko Diary da photos d’in da Naseer ya zubar, tana nuna musu pictures d’in Naseer da Zarah a tare, sannan ta nuna musu Diary d’in,
shiko Naseer kukan bak’in ciki da takaici ya saka, wai ace ‘ya’yansa na cikinsa halak malak,
amma basu san shi ba, suna doubting akan cewar he is there real blood Father,,
ai suna gama gani da gudu suka nufi Naseer suka fad’a jikinsa suna murna,,
tsam-tsam Naseer ya rungume su a jikinsa kamar za’a kwace masa su yana kuka.

Nourr tace ” Dad ina Na’eem?

Kanta ya shafa yana zubar da kwalla had’i da kallanta yace ” yana gida,
“Dad ka kaimu wajen sa please Nouwaf ya fad’a cike da shagwab’a yana langwab’ar da kai gefe,
shafa kansa Naseer yayi yana murmushi yace ” dama ai kun gama zama a nan, dan bazan barku ku k’ara koda 1 second ba nan, a razane Zarah ta d’ago kai had’i da tsaida kukanta ta kalle shi,
dan tasan halin Naseer da kafiya, taurin kai da kuma bak’ar zuciya,,
kenan duk abinda Doctor Jennifer ta fad’a masa bai sa zuciyar sa tayi sanyi ba.

Ganin Naseer ya mik’e yana k’ok’arin fita rik’e da hannun yaran yasa Doctor Jennifer cewa,,
” wai ku maza mai yasa kwata-kwata baku da adalci da tausayi ne kanku kawai kuka sani?

” Naseer yadda fa kake tak’amar kana san Zarah itama haka take sanka,,
haka yadda kake tak’amar kasha wuya a kanta haka itama tasha bak’ar wuya akanka,
yadda kake tak’amar tabar ku kai da Na’eem, kuma kayi rainansa,,
haka itama ta zauna ta haifa maka twins ta kuma yi maka rainan su,
amma dan rashin tausayi da imani da tsabar rashin adalc…………….

Kauuuuuuuuuuuu!!!!!!!!!!!!!!
Tauuuuuuuuuuuu!!!!!!!!!!!!!!

Naseer ya watsawa Doctor Jennifer gigitattun marika kyawawan gaske,,
a zuciye cikin matsanancin b’acin rai ya nuna ta da yatsansa yace ” tunda na shigo gidan nan kinji nayi miki magana kona kulaki?

“Ko kinji na tanka miki?

” Jennifer babu wanda ke da alhalin duk wannan laifin sai ke,duk ke ce kika ja komai, kika kuma k’irk’iri komai,,
saboda badan ke ba nasan babu yaddan za’ayi kwakwalwar Zarah, ko tunaninta ya bata ta barni,ke kika jawo komai, duk wannan tarin d’umbin laifin da kika yi min amma ki zo gaba na ki tsaya min kina min surutan banza,,
har ke zakiyin maganar adalci, da san kai?

” Ke kina da bakin da zaki maganar rashin imani da tausayi?

“Ke ki duba girman laifin da kikayi,,
kin raba ma’aurata, kin raba uwa da d’anta, kin raba uba da ‘ya’yansa, sannan ita kanta Zarah kin rabata da kowa nata harna tsayin 4yrs,,
duk wanda yaji maganar nan ke zai d’orawa laifi,
saboda kin haifi Zarah,
kuma sannan kin fita wayo, hankali da tunani.

” Duk da cewar ita ma da laifinta tunda ba zarga mata igiya kikayi kika jawo ta ba,,
ba kuma rufe mata bakin dazata sanar da wanda ya cancanci hakan kikayi ba,sannan ba rufe mata tunani da kwakwalwar ta da zatayi tunani kikayi ba,
ya k’arsa maganar yana kallan Zarah datayi tsaye sororo had’i da rufe bakinta da hannayenta dan ganin marin da yayiwa Doctor Jennifer,
yaci gaba ” Jennifer you’re behind of all this drama,
and you are the one who was created the scenes,
wallahi sa’a ma kika ci daban ci ubanki nayi miki mugun duka ba,
kuma zan tafi da yara na naga uban daya isa ya hanani tafiya dasu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button