GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Doctor Jennifer data saki baki tana kallan Naseer saboda tsabar mamaki tace
” I think you knew this country is not your selfish, rubbish, jobless, homeless craters country bane,
inaga ka d’auka yadda wannan k’azamar wulak’antancciyar k’asar taku (Nigeria) take haka ko’ina ma yake,,
to ka sani mu nan bama sonkai, bama karb’ar cin hanci da rashawa kuma bama a fusace Naseer yayi kan Doctor Jennifer,,
sanin halin Naseer yasa Zarah saurin shiga tsakiyar su, dan tasan ba k’aramin aikin Naseer bane yayi mata mugun duka ba.

Cikin daga murya yace ma Zarah ” stop it please,
I’m Nigerian, so I won’t tolerate any disrespect or disgrace my nation,,
sannan ta kalli Naseer tace ” ni ya kamata ka daka Naseer ba ita ba,,
a kaina ya kamata ka huce fushinka ba’a kanta ba, saboda nice taka, nice kuma wacce nayi maka laifin ba ita,,
tsananin bak’in ciki ne yasa Naseer nausar mirror d’in dake gefensa ya tarwatse batare daya kuma cewa komai ba yaja hannun yaransa suka fita, durk’ushewa Zarah tayi a wajen had’i da fasa mahaukacin kuka, da sauri Doctor Jennifer ta k’arasa inda take had’i da d’agota tace ” yi sauri kibi mijinki,
kiyi fighting akan rayuwarki Zarah yanzu da da yanzu ba d’aya bane,
kin san duk takness d’in da zakibi wajen karkato da hankalinsa shi gareki.

“Nasan kin san lagwansa, kiyi yak’i ki karkato da hankalinsa gare ki,, nasan Naseer yana tsananin sanki kuma da bak’ar zuciya, kuma zuciyar sa tana iya sawa ya hak’ura dake duk tsananin san daya yake miki, ki dage ki kula da mijinki da yaranki,
ki tuna yaranku uku ke dashi dan haka ya zama ke kema kin zama shi,
kin zama dolensa shima ya zama dolenki,
ki bi shi, kije kiyi yak’i akan rayuwarki da farinki,
gobe in sha Allah zanzo na kawo muku kayan ku keda su Nourrr, zanyi missing d’inku sosai Zarah, mun saba 4yrs ba wasa ba,
ta fad’a hawaye na gangaro mata,
itama Zarah kuka take, cikin kukan tace ” nima zanyi kewarki sosai,
murmushi kawai Doctor Jennifer tayi had’i da saurin juya bayanta,
Zarah zata kuma magana Doctor Jennifer tace ” just go,
batare data kuma magana ba ta juya ta fita da gudu tabi bayan Naseer.

Tana zuwa harabar gidan ma ya dad’e da tafiya dan haka tayiwa motarta key tabi bayan sa,,
a gefen motar Naseer tayi parking ta fito da sauri,
a tsaye ta hangoshi a bakin k’ofa yana yin nocking,,
da sauri ta k’arasa wajensa har tana yin tuntub’e,,
dai-dai lokacin da Na’eem ya fito da gudu daga cikin gidan yana kiran,,
” you are welcome sweet Dad yana dariya,,
ganin Zarah yasa shi yin turuss had’i da b’ata rai take.

Yace ” you again?

Durk’usawa Zarah tayi had’i dakai hannu zata tab’a shi,
da sauri Na’eem yaja baya had’i da cewa,

“Ok you come and make my Sweet Dad cry again.

Kai Zarah ta girgiza masa batare data iya cewa komai ba sai hawaye da ke zubo mata,
cikin kuka tace ” no, I Won’t make your Dad cry forever, na dawo nan da zama ne nima,,
” what cewar Na’eem yana kallan Naseer,,
tsaye Naseer yayi hard’e da hannuwa a k’irjinsa yana kallan su,

Na’eem ya kalli Naseer yace ” Sweet Dad is she not the one that made you cry last time?
and she is the one said you are lied to me,
so Dad I really hate her, impact if she is going to stay here I’m leaving now,
ya fad’a yana hankad’a Zarah waje da k’arfi yace ” I really hate you so much, get out from our home,
ta bud’e baki zatayi magana.

Da sauri Na’eem yace ” I don’t want here anything from you, and I said get lost, I hate you I don’t want see you again in my life,
ya k’ara hankad’a ta waje,
ganin bata da niyyar fita ne yasa Na’eem kallan Naseer yace ” sweet Dad if she won’t leave I’m leaving…………

MOMYN ZARAH
[17/02, 02:54] Atk: GADAR ZARE!!!

(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)

       ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

GARGAD’I

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO

BEST FRIEND FOREVER & EVER
ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~

65

Da sauri Zarah ta k’arasa wajen Na’eem tana kuka ta rungume shi tsam a jikinta,
ta yadda bazai iya kwacewa ba,
aiko yayi ta mutsu-mutsun kwacewa amma ya kasa,
cikin kuka Zarah tace ” am so sorry Na’eem,
I know I hurt you, but am so sorry dear,
shiru Na’eem yayi ya kasa k’ok’arin barin jikin Zarah,
had’i da kwantawa lufffff a jikinta, cikin kuka Zarah taci gaba ” I’m your beloved mother, your sweet Dad has not lied to you, jin tace itace Mom d’insa yasa shi saurin barin jikin ta had’i da zuba mata ido kawai yana kallanta.

“Yes Na’eem nice mahaifiyarka, nice mamanka, halak malak.

“To Momy me yasa kika bar mu ni da Dady na, mu kad’ai?

Shiru Zarah tayi ta kasa cewa komai, ci gaba Na’eem yayi ” Momy meyasa baki zo mun kwana tare a the same bed ba?

“Meyasa baki bani abinci a baki na kinyi wasa dani ba?

“Momy meyasa kika ce ke ba Momy na bace, ko bakya san mu ni da Dady na?

Gaba d’aya tambayoyin Na’eem k’ara rud’a Zarah sukayi,ta rasa abincewa kuka kawai take yi duk jikinta na kerrrma.

Naseer na tsaye sak’ale da hannayensa a k’irjinsa ya zuba musu ido kawai,,
yana mamakin wayon Na’eem kamar ba yaro k’arami ba, ganin Zarah bata da abincewa yasa Naseer durk’usawa a gaban Na’eem had’i da rik’o hannayensa cikin nasa yana kallansa,
fuskarsa d’auke da murmushi yace,
” ba san mu ne bata yi ba, kasawa ranka Momynka na sanka fiye da kowa da komai a duniya,, sannan ka sawa ranka cewar duk uwa ta gari bazata tab’a yin nesa da yaranta haka nan ba,,
sai dai idan akwai wani kwakkwaran dalilin kaji,
kuma daga yau karna kuma jin kace you hate her, she is your real beloved mother,,
so love her so much until your last breath,
kai Na’eem ya d’agawa Naseer yana dariya, murmushi Naseer yayi had’i da mik’a masa hannu yace ” promised me you u’ll love her dearly,,
dariya Na’eem yayi had’i da cewa ” yes Sweet Dad I promise you,,
dariya Naseer yayi had’i da ja masa hanci yace ” dats my boy,
go an say sorry for her,
ba musu Na’eem ya tafi wajen Zarah had’i da kama kunnansa dan haka Naseer ya koya masa yace.

” Am so sorry sweet Mom, rungume shi Zarah tayi tana kuka tace ” am so sorry too dear,
I’m really sorry for what I did to you,
and I promise I will never repeat it again,
dariya yayi had’i dacewa ” apologize accepted Mom,
komawa wajen Naseer yayi yace ” Sweet Dad na bata hak’urin,
kansa Naseer ya shafa yana murmushi yace ” good boy.

Nourrr da Nouwaf na gefe tsaye sun yi sororo suna ganin ikon Allah,
dan su basu kai Na’eem wayo sosai ba,
ya fi su wayo duk da ba wata tazara ce sosai a tsakanin su ba, just 10 months ya basu,
sai lokacin Naseer ya juya ya kalli su Nouwaf da Nourr dake tsaye a nutse,
dan yaran sun samu ingantacciyar tarbiyya duk da kasancewar a turai aka haife su kuma suke rayuwa da yaran turawa,amma a nutse suke cikin kamala da tarbiyya.

Naseer ya nunawa Na’eem su yace ” another surprise,,
cikin matsanancin mamaki Na’eem ya bud’e baki yana kalan su,
had’i dayi musu dariya, yace ” friends are you here?

Kafin su bashi amsa Naseer yayi saurin cewa ” they’re not just a Friends to you,
they’re your beloves sister and brother,
they’re your junior bro & sister,,
suma ‘ya’yana ne kamar kai,kuma suma Momynka ce ta haifesu, uwarku d’aya ubanku d’aya kai da su,
ya fad’a yana jawo su Nouwaf jikinsa,
” wow this is amazing Dad, gaskiya am very happy to day,
Momy na da ‘yan uwa na sun dawo gida,,
da sauri ya saki Naseer yaja hannun su Nouwaf cikin gidan,,
Naseer ya bi su da kallo yana murmushi,
yana k’ok’arin mik’ewa Zarah ta rik’o k’afafunsa da sauri ta zube a gabansa ta shiga bashi hak’uri,
k’afa Naseer yasa ya tsallake ta yayi shigewarsa cikin gidan ya barta anan.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button