
Da sauri ta mik’e itama ta shiga gidan har tana tuntub’e,
amma bata ko tsaya tabi takan tuntub’en datayi ba,
a parlor ta tsaya tana bin Naseer da ido zaune a tsakiyar yaransa,
a hankali ta zauna akan sofa tana ci gaba da kuka, d’a da mahaifi sai Allah,
a hankali Na’eem ya taso yana sharewa Zarah hawayen ta dake ta faman zuba yace,
” Mom meyasa kike ta kuka?
Murmushin dole Zarah ta k’ak’aro had’i da cewa ” ba kuka nake ba ido na ke ciwo,
ayya Mom sorry kinji,
ya juya ya kalli Naseer yace ” Dad Momy bata lafiya ka kai ta hospital,,
shima murmushin dole yayi had’i da cewa ” daga hospital d’in muke yanzu,
daga nan bai kuma cewa komai ba.
K’arfe 10:30pm na dare gaba d’aya yaran sukayi bacci,, a hankali Naseer ya mik’e ya kwashe yaran ya kai su bedroom d’in sa ya kwantar,
kasancewar 3 bedroom ne a gidan Rose tana cikin d’aya,
d’aya kuma Naseer da suke kwana tare da Na’eem,,
sai d’aya dake cike da kayan wasan Na’eem,
tsaye yabar Zarah ta rasa inda zata shiga, tana nan zaune har around 11:30pm na dare,
ga yunwa da bacci gashi batayi sallah ba,
a hankali ta mik’e ta nufi bedroom d’in Naseer wanda dama ta riga tasan shi,
tunda tana yin satar layi tazo gidan,
tsaye ta iske shi yana safa da marwa a d’akin yana zubar da hawaye,
bata yi mishi magana ba, ta wuce bathroom cikin sanyin jiki tayi wanka had’i d’auro alwala,
wardrobe d’in kayansa ta bud’a ta d’auko jallabiyyarsa ta saka a jikinta, sannan ta sanya hijab ta tada sallah,
duk abinda take yi idan Naseer na kanta,
dan gaba d’aya hankalinsa na kanta,
sai da ta gama rama sallolin da ake binta sannan ta fita ta nufi kitchen kwai ta soya, sannan ta hada tea mai kauri ta sanya bread ta nufi bedroom d’in Naseer dashi.
Yadda ta barshi haka ta dawo ta iske shi, a hankali ta ajeye tray d’in akan table sannan ta koma ta kama hannun Naseer batare datayi mishi magana ba,
da sauri ya fisge hannunwasa a fusace yace ” karki kuskura ki k’ara gigin tab’a ni,
cikin sanyin murya tace ” please ko tea d’in ne kawai kasha, dan Allah.
A k’ufule Naseer yace ” dacan da kika barni har tsayin 4yrs ke kike ci dani?
“Ko da kika dawo kinga alamun yunwa a tattare dani?
Hawayen dake zubo mata ta goge cikin muryar kuka tace ” please Uncle kayi hak’uri ka yafen laifin danayi maka,
ka tuna Allah yana san mutane masu yafiya,
kuma ko Ubangijin daya halicce mu muna yi masa laifi mu tuba ya yafe mana,
dan Allah ka zamo mutum mai yafiya, da saurin manta sharri da tuna alkhairi, ta k’ara maganar hawaye na zubo mata,
bai ce mata komai ba ya bud’e wardrobe ya d’auki plow da blanket yayi ficewarsa,
durk’ushewa Zarah tayi had’i da fasa kuka.
Washe gari wajen k’arfe 2:00pm na rana Doctor Jennifer tazo ta kawo musu kayan su gaba d’aya, yanayin data iske Zarah yasa tasan har lokacin Naseer bai hak’ura ba,
dan haka taja hannun Zarah ta zaunar da ita a gefenta tana kallanya tace ” Zarah kiyi hak’uri,
hak’ik’a mun taru munyiwa Naseer babban laifin da duk wanda akayiwa irinsa zeyi abinda Naseer yayi koma fiye da haka,ki sakawa ranki hak’uri da dauriya, gami da juriya,
ki jajirce ki dage kiyi ta bashi hak’uri,
sannan kin san lagon mijinki,kibi duk hanyar da zaki bi ki shawo kan kayanki,
ki daure karki bari ciwonki ya tashi please,
sosai Doctor Jennifer ta bawa Zarah shawarori sannan tayi mata nasiha sosai gami da k’ara mata kwarin gwiwa.
Ganin gidan yayi musu kad’an yasa Naseer canja musu gida,
mai shegen kyau babba sosai wanda yasha kayan alatun more jin dad’in rayuwar duniya,
sosai gidan ya tsaro, mai d’auke da part 2,
part d’in farko yana d’auke da 4 bedroom sai babban parlor, kitchen & dinning area,
kowanne bedroom akwai toilet & bathroom cikin sa, sannan a parlor ma akwai toilet and bathroom,
part na biyu 1 bedroom 1 parlor and 2 toilet & bathroom,
kun dai san tsarin ginin turawa akwai kyau, girma da tsaruwa,,
Inda nan ne part d’in Naseer.
Kasancewar Rose ta d’an manyanta yasa Naseer yi mata kyauta ta kud’i mai yawa yace taje ta dogara da kanta ta kuma kula da kanta, sannan ya sallameta,
bayan yasa ta nemo masa wasu ‘yan Philippines ???????? guda biyu,,
mai suna Rosiline & Warda,
inda aka basu bedroom d’aya, duk da Zarah bata barin su suyi mata girki,
kula da yara da gyaran gida kawai suke mata,
shima banda part d’in Oga Naseer dan ita take gyara masa,
Zarah ta d’auki bedroom d’aya,
Sai Nouwaf & Na’eem bedroom d’aya
sai kuma bedroom d’in Nourr daban,
sai part d’in kayan wasan yara, wanda ya had’a komai kamar a childrens park,
sai gym (wajen motsa jiki),
sai swimming pool and garden.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya tsakanin Naseer da Zarah,
kwata-kwata baya kula ta, baya shiga harkarta,
tayi iya yinta a banza,
dan haka bak’in ciki yasa Zarah shiga bedroom d’in ta had’i da zaman dirshan ta fasa kuka,,
Na’eem ne yaga bata parlor dan haka ya shiga bedroom d’in ta nemanta,,
ganin tana kuka yasa shi fita da sauri ya kira su Nouwaf da Nourr,
a gaba suka saka ta suna tambayarta meke damunta ganin bata basu amsa ba yasa su fashewa da kuka gaba d’ayan su,,
kasancewar Zarah tana cikin matsananciyar damuwa yasata mantawa da wad’anda take tare ta shiga basu labarin komai.
Daga Zarah har yaran kuka suke,
sosai take basu labarin komai kamar suna fahimtar abinda take gaya musu,
kasancewar akwai soyayya da shak’uwa mai k’arfi tsakanin ta da yaranta,
dan tare take kwana dasu, dan koda taje bedroom d’in Naseer ma korota yake, ko ya gaya mata bak’ak’en maganganun da zata kwana tana kuka,
ko kuma kafin taje ya kulle, dan haka ta mai da hankali sosai akan yaran take jan su a jikinta,
komai itake yi musu wanka wani lokacin ma tare suke wasa, da gym and swimming,
sai da ta gama basu labarin kaf sannan Na’eem dayake yana da wayo yace ” to Mom yanzu mai zamuyi mu taimake ki,
dad’i Zarah taji har ranta, cikin kuka ta rungume yaranta tana cewa ” ku taya ni bawa Dadynku hak’uri ya yafe min laifin dana yi,
Na’eem yace ” Momy ki koya mana yadda zamuyi.
Koya musu duk yadda zasuyi tayi sosai,
dukkan su kuka suke sosai sun rungume ta,
suna haka Naseer ya shigo neman yaran dan ya kira phone babu wanda yayi picking,
kai tsaye ya shigo bedroom d’in,
yanayin daya gansu sosai ya tab’a mishi zuciya suka bashi tausayi,
dan ba k’aramin so yake yiwa yaran sa ba,
dan sun tarbiyantu, sosai Zarah ta zage ta bawa su Nouwaf ingantacciyar tarbiyya irin ta addinin musulci,
abinda yasa ya rage masa jin haushinta gami da tsanarta kenan,
ya tabbatar koda baya raye yaran sa sunyi sa’ar uwa ta gari wacce zata tsaya tsayin daka akan tarbiyarsu.
Yakai wajen 15 minutes tsaye yana kallan su kafin hankalin Na’eem yakai kansa,
da sauri Na’eem ya saki jikin Zarah,
sai lokacin duk suka lura dashi,
a hankali Zarah ta mik’e taje gabansa tayi kneel down had’i da kama kunnenta,
tana zubar da hawaye tace ” am sorry Uncle,
banza yayi da ita ya juya yana k’ok’arin fita,
da sauri gaba d’aya yaran suma sukayi kneel down a gabansa had’i da rirrik’e kunnuwansu suma su kace ‘we are sorry Dad,
murmushi Naseer yayi had’i da umarta su dasu tashi,
amma fir yaran suka k’i tashi suka ce har sai ya yafewa Momyn su,
tsawa Naseer ya daka musu had’i cewa I said get off,
gaba d’aya yaran da Zarah suka saka kuka mai rikitarwa a lokaci d’aya,
Ido Naseer ya zaro cike da mamaki,
komawa sigar rarrashi Naseer yayi, cikin wayo Naseer yace ” ok to ku tashi shikenan ya wuce kuzo na kai ku shan ice cream,
mak’e kafad’a yaran suka yi had’i da cewa ” no Dad, we don’t need,
Please Dad forgive our Mom,
dan Allah Dady ka yafewa Momy matuk’ar kana san ganin mu cikin farin ciki da walwala,
idan kuma kak’i yafe mata bazamu tab’a tashi daga kneel down d’in nan ba,
suka fad’a cikin kuka,
babu yadda Naseer bayyi su tashi ba amma suka k’i sai ma matsanancin kukan da suke ci gaba dayi,
a hankali Naseer ya kalli Zarah yaga yadda take kuka, kamar ranta zai fita,
suna had’a ido ta langwab’ar masa da kanta,
da sauri ya kawar da kansa daga gare ta,
ya kalli yadda Na’eem, Nourr, Nouwaf ke kuka,
jin kukan yake yi har cikin ran sa, yana k’ona masa zuciyar sa,
yayinda yake jin zafin kukan nasu sosai kamar ana yankar namar jikinsa,
ido Naseer ya runtse da k’arfi yana tuna irin so da kulawa gami da halaccin daya nunawa Zarah,
sannan ya tuna girman laifin data yi masa, amma babu yadda zayyi dole ya yafe mata kodan albarkacin yaranta.