
A hankali ya bud’e idansa da suka gama komawa jajaye ya sauke su akan su,
yace ” is okey, na yafe mata,
ai da sauri suka mik’e gaba d’ayansu sukayi kansa cike da murna.
Tun daga wannan rana Naseer ya d’an sakarwa Zarah,
duk da ba wani sosai bane,
yana dai zama parlor ta yanzu,
yana kuma zama a dinning tare da ita da yaran suci abinci,
wata mu’alace dai kwata-kwata babu ita,
dan bama taga fuskar yin hakan ba,
to yanzu zaman nasu zamu iya cewa ba laifi,
dan ba yabo ba fallasa,
duk da har yanzu baya barinta ta shiga part d’insa,
magana ma sai ta kama a tsakanin su ko ta zama dole yake mata jefi-jefi,
duk ta rame ta shiga muguwar damuwa ko abinci ba kasafai ta fiye ci ba.
Haka dai suka ci gaba da rayuwa a cikin wannan halin,
ranar Sunday babu aiki Naseer ya kwashi duka yaransa ya fita yawo dasu,
duk da Zarah taso bin su amma ya hana ta dan baima bata fuskar cewa zata bisun ba,
tana zaune ita kad’ai a gidan ta rasa inda zata saka ranta da damuwar ta,
abun duniya ya ishi rayuwata,
Doctor Jennifer tayi sallama,
cike da murna Zarah ta mik’e ta rungume ta, had’i da fasa mata kukan da ita kanta bata san dalilin yin sa ba,
shiru Doctor Jennifer tayi ta rasa abin yi,
a hankali cikin mutuwar jiki ta ja hannun Zarah zuwa bedroom d’in ta,
a bakin bed ta zauna ta zaunar da Zarah a gefenta, sai da ta rarrashi Zarah tayi shiru sannan ta tambaye ta abinda ke faruwa,
ba wani b’oye-b’oye Zarah ta zayyane mata duk abinda ke faruwa tsakanin ta da Naseer.
Shiru Doctor Jennifer tayi na wani lokaci had’i da zubawa Zarah ido,
sai da tayi wajen 7 minutes sannan ta sauke ajiyar zuciya tace ” ke yanzu Zarah duk hannunka mai sandar danayi miki ashe baki fahimci abinda nake nufi?
Kallanta kawai Zarah keyi batare data ce komai ba,
Doctor Jennifer taci gaba ” ai lusarar mace kuma sakaryar mace ce zata tsaya tana gaba da mijinta har na tsawon 3 months,
haba Zarah kamar ba mace ba,
har ki tsaya namiji yana sha miki k’amshi yana basar dake,
akwai hanyoyi da dama wanda Naseer ko dutse ne shi da k’arfe tsabar taurin kai sai ya bada kai bori ya hau,
ke wallahi da kansa ma zai kawo kansa yana gurfane a gabanki yana bada hak’uri koda kece kikayi masa laifin,
haba ni ina mamakin mata irin ki,
da zaku zauna namiji yana rejecting d’inki,
bayan yanzu kai ya waye, ido ya bud’i ilimi yazo mana, akwai hanyoyi da dama dazaki iya shawo kan mijinki kuma ki mallake kayanki batare da asiri ko tsafi ba,
ba kuma sai kinyi shirka ko kin sab’awa Allah ba.
Matuk’ar kika rik’e gaskiya da amana, kika kuma ji tsoran Allah akan lamuranki,
kika dai-dai ta tsakanin ki da Allah da kuma shi Oga,
sannan kika kasance mai hak’uri, juriya da kawar dakai daga abubuwa da dama, kina ganin an cuce ki an kuma zalunce ki amma ki kawar da kanki,
bayan kina da yadda zakiyi, akwai magana ko abinda baya buk’atar martani ko ramuwa ido kawai ya ishe mai hankali,
Idan kika zuba masa ido shi da kansa zai dawo yana jin kunyar ki,
duk iskancinsa da rashin kunyarsa.
Cikin rashin fahimta Zarah tace ” wallahi ban fahimci abinda kike nufi ba.
Murmushi Doctor Jennifer tayi had’i da cewa ” ina nufin bayan wad’anan abunuwan sai kin had’a da abubuwa uku,
KISSA
KARUWANCI da kuma
BARIKI.
Da sauri Zarah ta zaro ido tace ” KARUWANCI da BARIKI kuma?
Murmushi Doctor Jennifer ta kuma sannan tace ” eh Zarah,
matuk’ar kina san ki tsira ki kuma yi fice a gidan mijinki dole sai kin had’a da wad’annan abubuwan,
da farko sai kin cire kunya kin zama tantiriyar mara kunya karuwa kuma ‘yar bariki a gidan mijinki,
karki sake kunya ta cuce ki ta hana ki kwatarwa kanki ‘yanci a gidan auren ki,
wannan shine babban k’alubalen dake damun matan Hausawa,
shiyasa duk duniya da kuma k’abilar duniya babu inda aka fi sakin aure da yawan ZAWARAWA kamar a Hausa,
da wuya kaga, bayerabiya, inyamura, banufiya, Igbo, Indian Arabian da sauran k’abilun aure ya mutu ko kaga bazawara,
wannan ya samu asali ne saboda dalilai biyu zuwa uku,
na farko k’addara,
na biyu rashin hak’uri, fahimta, juriya da kawar da kai,
na uku sakacin mu, shiyasa matan waje da matan banza ke kwace mata mazajen mu a waje,
kiga miji idan yana k’aunar mutuwarsa yana k’aunar ya dawo gidansa, yafi san zaman waje da wata akan zama dake matarsa,
so muma mu zage dantse mu zama irin su fitsararru a gidan auren mu,
dan mu kwaci ‘yancin mu, mu rink’a sakin towel intentionally, sannan mu rink’a wawan zama, mu rink’a sakin layi, muna daty talk (batsa) da mazajen mu,
mu rink’a bank’ara k’irji muna juya k’ugu had’i da lasar leb’e muna d’an cije shi,
a fagen kwanciyar aure ma mu zage mu bada gudummawa sosai,
ba wai mu kwanta kamar ruwa ba sai yadda yayi damu,
ki rink’a k’ok’arin neman mijinki da kanki,
sannan ki kasance mai tsafta da kwalliya da k’amshi a kowanne lokaci.
“Kuma idan kunyi fad’a kirink’a using maganin k’arfin maza dan shawo kansa,
batare da saninsa ba zaki zuba masa a abin shan sa,
ke kuma idan yazo karki wani b’ata lokaci ko ki ja aji ki bada kai kawai buri yahau da mazan yanzu sai da cuwa-cuwa, kissa, bairiki, da karuwanci,
shiyasa nake yi miki hannunka mai sanda ina ce miki,
ki shawo kan mijinki dan kifi kowa sanin halinsa da kuma abinda yafi so,
to ai abinda nake nufi kenan.
Shiru Zarah tayi tana d’aukar darasi, kuma sosai darasin ke shigar ta tana fahimta sosai,
Murmushin mugunta Zarah tayi had’i da cewa ” sorry NASEER yanzu aka fara wasan,
dan sai na zama fiye da tunanin Doctor Jennifer, sai na zama cikekkiya kuma tantiriyar karuwa cikin kissa a gare ka,
gani nan gare ka Naseer………………
MOMYN ZARAH
[17/02, 02:54] Atk: GADAR ZARE!!!
(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)
~NA~
HAUWA A USMAN
JIDDARH
????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
GARGAD’I
MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA
~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO
BEST FRIEND FOREVER & EVERZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~
66
Tab’a ta Doctor Jennifer tayi tace ” ya naga kinyi shiru?
Murmushi Zarah tayi had’i da cewa ” bakomai kawai ina tunanin ta inda zan fara ne,,
murmushi Doctor Jennifer tayi sannan tace ” yanzu ki kirashi a waya kice masa zaki fita.
“Fita kuma, ina zamu?
Zarah tayi maganar cikin rashin fahimta,
Doctor Jennifer tace ” eh fita zamuyi yanzu muje mall mu siyo maganin k’arfin maza,,
da fitsararrun kaya(naked English wears),,
cikin kame-kame Zarah tace ” to… ai…. bani…. da… num…… ber….. sa,,
cikin mamaki Doctor Jennifer tace ” what, you don’t have your husband phone number?
“Tab lalle Zarah kina nema kiyi sake gaskiya,
inma zaki gyara tun wuri gwara ki d’auri d’ammarar gyarawa,
tayi maganar tana mik’ewa, da sauri Zarah ta mik’e tana cewa ” am sorry please karki yi fishi da ‘yarki,, dan a zaton Zarah fishi Doctor Jennifer tayi,
dariya tayi had’i da cewa ” ba fishi nayi ba Zarah zanje mall ne na siyo miki kayayyakin da kuma strong man tab,
dariya Zarah tayi had’i da rungume tana cewa ” yawwa good Mom, thank you so much,
fita Doctor Jennifer tayi tana dariya, batare data ce komai ba.
Bayan kamar 20 minutes da fitar Doctor Jennifer ta kira Zarah a waya,,
da hanzari Zarah ta d’aga wayar tace ” good Mom like no other,
murmushi kawai Doctor Jennifer tayi tace ” na bawa mai saloon da gyara jiki number ki za suzo nan da 15 minutes so ki tura musu location,,
ihuuuuuuuu Zarah tayi tace ” uwa dai ta dage sai ta gyara ‘yarta,
tana san mijin ‘yar yaji zan-zan,
murmushi Doctor Jennifer ta kuma yi had’i da dropping phone d’in.