GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Haka rayuwa tayi ta tafiya lokaci na wucewa,,
har Allah yasa cikin Zarah ya shiga wata tara,
ranar friday ta tashi da nak’uda, aka kai ta hospital batayi wata doguwar nak’uda ba haifi d’iyarta mace, mai tsananin kama da ita sak kamar an tsaga kara,,
kasancewar ta haihu lafiya ba wata matsala yasa aka sallamo su,,
suka dawo gida cike da matsanancin farin ciki,
suna dawowa Naseer ya sanar dasu Dady Linah ta haihu dan har a lokacin Zarah a matsayin Linah take a wajen su,,
basu san gaskiyar al’amari ba,
bayan sun dawo gida da kwana d’aya Naseer ya iske Zarah a bedroom d’inta tana shiryawa,
a hankali ya rungumo ta ta baya, ya d’ora hab’arsa akan kafad’arta yana kallonta ta cikin mirror,,
yana murmushi yace ” mai jigo kin zab’awa Babyn mu suna?

Cikin murmushi itama take kallansa ta cikin mirror d’in tace ” yes of course,,
“Ok wanne suna kika zab’arwa Babyn mu?

Batare da tunanin komai ba tace “ZAINAB!!!!

A zabure Naseer ya sake ta had’i dayin baya yana kallanta kawai ya kasa magana,
dan shi Naseer har a lokacin bashi da wad’anda yafi tsana a rayuwarsa sama da Mannir da Zainab gani yake kamar duk duniya bashi da wasu mak’iya sama dasu,,
ya tsane su matuk’ar dan ko sunansu baya so a ambata a gabansa balle ace za’a sawa ‘yarsa ta cikinsa sunan Zainab,
Murmushi Zarah tayi had’i da cewa “kayi mata hud’uba da sunan ZAINAB!!!

Da k’arfi Naseer yace what!!!? had’i da juyawa ya firgita a haukace………….

MOMYN ZARAH

GADAR ZARE!!!

(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)

       ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

GARGAD’I

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO

BEST FRIEND FOREVER & EVER
ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~

69

Ya fisgota a haukace yace ” Zainab d’in banza Zainab d’in wofi,,
ita harta isa na sawa ‘yata ta ciki na sunanta?
ashe ma ni ba d’an halak bane,
shiru kawai Zarah tayi had’i da zuba masa ido batare data ce komai ba, har ya gama bambaminsa ya fita,,
bayansa tabi da kallo har ya ya bar d’akin,
ajiyar zuciya ta sauke had’i da girgiza kanta,
kwanciya tayi akan bed tana tunanin irin muguwar k’iyayyar da Naseer ke yiwa Zainab da Mannir wanda ita kuma bazata tab’a yarda ta d’auki hakan ba,,
saboda duk lalacewa dai sune gatanta har yanzu kuma har yau har gobe,
Zainab itace wacce ta shayar da ita da ruwan nononta,
kuma ita ce tayi mata duk wata wahala da d’awainiyar da uwa keyiwa ‘yarya harta girma,,
haihuwarta ne kawai Zainab batayi ba, amma duk wani abu da uwa takewa d’an data durk’usa ta haifa da kanta Zainab tayi mata fiye da haka ma.

Haka ma Mannir shine ubanta dan shi yayi mata komai da uba kewa d’ansa a rayuwa,
sun nuna mata so fiye ma da ‘yar da suka haifa da cikinsu,,
sun bata gata, da kulawa, sun bata ilimi bako da addini,,
dan haka bazata tab’a yarda da raini ko wulak’anci balle kuma k’ask’ancin da Naseer yake yi musu ba,
sai da duk abinda zai faru ya faru dan har gobe suna a mazaunin iyayenta dan bata da iyayen da suka fisu,,
sune gatanta kuma sune rayuwarta,
a haka har bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita.

Bata farka ba sai wajen 8:00pm koda ta tashi ta fita,
iskewa tayi su Warda sun gama komai,
har yaran sunci abinci anyi musu wanka sun kwanta,
ganin ba Naseer ba dalilinsa yasa Zarah ganewa fishi yake da ita,
k’udura tayi matuk’ar akan sunan data zab’awa ‘yarta ne yake wannan fishin sai dai yayi tayi amma zata bashi hak’uri kota janye k’udirinta na sawa ‘yarta sunan Zainab ba,,
dan haka ta mik’e tayi shigawarta bedroom ta fad’a wanka,
wasa-wasa har wajen kwana 4 Zarah bata sanya Naseer a idanta ba,,
tun da akayi abun, dan haka taji ta shiga damuwa sosai, taji kuma tana buk’atar san ganin mijinta,,
dan haka ta fesa wanka ta shirya ta nufi part d’insa, a parlor ta iske shi kwance akan 3 sitter,
da sallama ta shiga, bai d’ago ya kalle ta ba ya amsa sallamar dakyar kamar wanda akayiwa dole,,
murmushi Zarah tayi had’i da zama a kusa da, tsaki yayi mtswwwwwww had’i da kawar da kansa gefe,,
sanin halin kayanta yasa Zarah yin shiru dan tasan Naseer akwai bak’ar zuciya,
harga Allah bata ji dad’in yadda yayi mata ba,
amma ta daure ta kalle shi fuskarta d’auke da murmushi tace ” sweetheart kaci abinci?

Banza yayi mata baiko kalli inda take ba,
yaci gaba da harkar gabansa,
murmushi ta kuma yi had’i da cusa hanunta a cikin gashin kansa tace ” ni ce ko?
” ni na b’ata ran haka?

Duk akan sunan Babyn ne kake fushi haka dan na saka mata sunan kakarta Zainab,,
a tsawace yace ” stop Malama, kije ki saka mata duk sunan da kike ganin ya dace da ita,
imma sunan uwar Zainab zaki saka kina iya saka mata,,
cike da mamaki Zarah ta mik’e tsaye tana kallan shi,
take hawaye suka fara zarya a a fuskarta,
cikin muryar kuka tace ” Naseer Kakata fa kenan!
a fusace yace ” sai me kakarta ki,,
cikin kuka tace ” Naseer wacce fa ta haifi mahaifiya ta Naseer kake zage,
Naseer ban tab’a danasanin aurenka ba sai yau,
Naseer tun har ka iya bud’e baki ka zagi mahaifiyar mahaifita to wallahi koda mahaifiya ta na raye zaka iya zaginta,,
tunda nake dakai ban tab’a yiwa koda ‘yan aikin gidan ku kalan banza ba balle d’aya daga cikin ahalinka,,
dan nace kasan sunan wacce ta rik’eni ta shayar dani,
take tamkar uwa a waje na, shine ka had’a su gaba d’aya ka zaga Naseer,
amma dayake Mannir shine d’an uwanka ne kuma jininka ai sunan d’anka na farko ka saka masa,,
ita Zainab dayake bare ce ai kayi haka, kuma shima dai yayi duk irin abinda Zainab tayi dan tare ma sukayi,
koma ince ya fita tunda shi har karya ni yayi, amma saboda kara ta cikakkun fulanin asali babu wanda a cikin ahalina ya kalle shi balle yayi masa magana.

Amma kai…. tsawa Naseer ya daka mata wacce ta sanya ta yin shiru dole,,
cikin fad’a yace ” daga Mannir har Zainab ni duk d’aya suke a waje na kuma ina hukunta sune a bisa laifin da sukayi miki,,
ba wai dan kai na bane,
“to tunda badan kanka bane, danni kake yin komai ka daina,
danni har yanzu bani da kamar su,
bani da wasu iyayen da suka kai min su balle su fisu,,
a fusace yace ” kin kyau ta, amma ba laifinki bane laifin zuciya ta ne datake miki uncontrollable love,
tsananin san danake miki ne yasani tsanar su nake kuma ganin laifin su akan abinda suka yi maki,,
itama cikin fad’a tace ” san me, wannan irin naka san na zagin iyaye na da kakanina?

“Ni fan zagi iyayenki ko kakaninki ba,
idan kuma kince na zage su gaya min sanda na zage su,
hawayenta ta share tace ” ok naji kana yi mun gogun so, to idan har san da kike min gaskiya ne,
kuma kana so na gaske ka sawa yarinyar nan Zainab,
Naseer duk duniya bani da kamar Mannir da Zainab,,
da sauri ya kalle yace ” duk duniya fa kike ce kina nufin harni yayi maganar yana nuna kansa,,
bata bashi amsa ba, taci gaba daba da maganar ta,
“sun rik’e ni tamakar ‘ayarsu ta cikin su, basu tab’a nuna min bambamcin komai tsakanina da ‘yar da suka haifa da kansu,
Zainab ta shayar dani da nononta ta rainane, tayi min duk abinda uwa keyiwa d’iyarta,
haka ma Mannir ya so ni, ya kula da ni yayi min gatan da kowanne uba yake yiwa ‘yarsa,
dame kake san nasaka musu?
bayan kai sanin kanka ne bani da abun saka musun, duk abinda ya faru akan idan magabatan mu ya faru amma babu wanda ya iya cewa komai,,
wannan kad’ai ya isa ya tabbatar maka da suna da martabar rik’o na da sukayi a idan kuwa,
a fusace Naseer yace ” tamabayar ki nayi kuma har yanzu baki bani amsar tambayar dani miki ba,
nace miki har ni sun fi a wajenki?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button