
Ya fad’a yana kallanta ido cikin ido, idan nasa sunyi masifar yin ja, kamar gauta,
ganin yanayinsa da kuma sanin halinsa yasa Zarah cewa ” ni dai nace idan har san da kike ikirarin kana yi min gaskiya ne, ka sakawa ‘yarka suna Zainab,
tana kaiwa nan tayi saurin barin d’akin, dan tasan idan ta tsaya komai yana iya faruwa a yadda taga ransa yayi masifar b’aci,
bango Naseer ya nausa cikin matsanancin zafin zuciya.
Zarah tana shiga bedroom d’inta ta fad’a kan bed,
had’i da sakin nannauyar ajiyar zuciya,
dan yadda taga idanun Naseer sunyi masifar tsorata ta.
Haka suka ci gaba da zama babu mai yiwa wani magana a tsakanin su,
duk da Zarah taso tayi masa magana,
ganin ba fuska ne yasa ta yin shiru ta kame kanta,
dan ta luta rigima yake nema da ita,
ranar da yarinya ta shiga kwana shiga da haihuwa Naseer ya shigo d’akin,,
d’aure da towel ya iske ta agaban mirror tana shafa lotion a soft skin d’inta,,
ko kallanta bayyi ba ya wuce gadon babyn a hankali yasa hannu ya d’auki Babyn had’i da k’ura mata ido,,
yana hango tsantsar kamar Babyn da Zarah,
ajiyar zuciya ya sauke da k’arfi har sai da Zarah ta juyo ta kafe shi da lulu eye’s d’inta,
sanin tana kallansa ne yasa shi cewa “kallan na meye,
yayi maganar batare daya d’ago ya kalle ta,
murmushin yak’e tayi had’i da d’auke idanta daga kansa,,,
jin ya fara yiwa yarinyar hud’uba yasata sake juyowa ta kafe shi da ido,,
har ya gama bai kuma ce mata komai ba,
a hankali ya mik’e ya mayar da Babyn kan Baby bed,,
batare daya kalle ta ba yace ” wannan kallan fa?
Da sauri ta kawar da kanta gefe had’i da cewa ” meye sunanta,
cikin rawar murya tayi maganar,
ko kallan inda take bayyi ba yayi ficewarsa,,
yana fito parlor yaran gaba d’aya sukayo kansa suna cewa our sweet Dad,
murmushi yayi had’i da cewa ” my sweet child’s,,
hannunsa Na’eem ya kama ya nauzar dashi akan sofa had’i da cewa Dady ina Momu ta siyo mana Baby?
Dariya Naseer yayi yace ” a kasuwa mana,
da sauri Noor tace ” Dady nima ina so ka siyo man,
kanta ya shafa yace ” to zan siyo miki,,
yayi maganar yana kallanta fuskarsa d’auke da simple smile,
suna hira da yaran Zarah ta fito bayan ta gama shiryawa cikin doguwar rigar material mai shegen kyau da tsada,,
simple make up kawai tayi, akan sofar dake gefe ta zauna tana kallansu cike da sha’awa tana murmushi,,
Na’eem ya dawo kusa da ita yana cewa ” Momy Dady yace zai siyo mana Baby muma a inda ya siyo miki kema ya fad’a yana nuna Babyn dake kan cinyar Zarah,
dariya tayi batare datace komai ba,
suna haka Doctor Jennifer ta shigo parlor’n bakinta d’auke da sallama,
a parlor ta iske Zarah da yaran suna tayi mata surutu, tana binsu da eh ko a’a kawai dan gaba d’aya hankalinta yana kan Naseer dake zaune a gefe tunda ta shigo parlor’n bai ko kalli inda take ba,,
balle ta iya tantance yanayinsa.
Jin sallamar Doctor Jennifer yasata d’ago da kanta tana kallan bakin k’ofar,,
k’arasa shigowa parlor’n tayi fuskarta d’auke da fara’a tace ” happy family,
cikin d’oki Zarah ta mik’e ta tare ta tana dariya, a sofa Doctor Jennifer ta zauna tana kallan Zarah, itama tana dariya,
hannu ta mik’a ta karb’i Babyn daga hannun Zarah tana cewa ” sannu Zarah ya k’arfin jikin?
Murmushi Zarah tayi had’i da zama a kusa da ita tace ” lafiya lau, Alhamdulalillah,,
fuska a sake Naseer ya kalli Doctor Jennifer yace ” sannu da zuwa, ina wuni?
dan shi Naseer mutum ne mai bak’ar zuciya marasan rai ni da wulak’anci kwata-kwata,
amma bashi da rik’o, kuma duk tsiya Doctor Jennifer ta rik’e masa mata har da ‘ya’yansa har guda biyu,
ita ce cin su da shan su, da kuma karatunsu, da sauran buk’atun rayuwa,
ita tayi musu komai, aiko ta wuce wulak’amci duk girman laifin data yi masa taci wannan darajar da albarkacin yaransa,,
sai lokacin ta kula dashi, fuska a sake tace ” Oga Naseer ana gida kenan?
Murmushi yayi yace ” wallahi,
tace ” kullum kai kana cikin iyalinka, kana basu farin ciki da kulawa, Allah dai ya had’e maka kan zuri’arka,
sosai Naseer yaji dad’in addu’ar data yo masa, dan haka yace ” Amin da sauri, sosai suka shiga hira da Naseer,
kafin ta kalli Zarah da ko sau d’aya bata saka musu baki ba sai dai tayi gutun murmushi kawai idan anyi abin dariya,,
tace ” Zarah ya sunan Babyn ne?
Ido Zarah ta k’urawa Naseer na tsawon lokaci,
shima ita ya kalla, aiko karaf suka had’a ido,,
fuska ya b’ata had’i da kawar da kansa
ganin haka yasa Doctor Jennifer kallan Naseer tace ” Oga ya sunan Babyn tamu ne?
Murmushi yayi had’i da cewa ZAINAB!!! amma za’a rink’a kiranta da NAILAH,,
ya k’ara maganar yana kallan Zarah,
aiko a zabure Zarah ta d’ago idanuwanta ta zuba su cikin nashi,
take kwallah ta taru a idanuwanta, tana kok’arin zubowa,
kai ya girgiza mata alamar a’a,
duk abinda suke yi idan Doctor Jennifer nakai,
Naseer ne ya kula da haka dan haka mik’e yayi part d’insa,
babu yadda Doctor Jennifer batayi dan taji abinda ke faruwa tsakanin su ba amma Zarah tak’i sanar da ita,
sai cewa tayi kawai ya tuno mata da Momynta Zainab ne,
sama-sama sukayi hira da Doctor Jennifer, dan ba sosai Zarah ke bata amsa ba,
dan hankalita gaba d’aya baya jikinta,,
ganin da da Doctor Jennifer tayi ne yasata mik’ewa had’i dayi mata sallama.
bedroom Zarah ta shiga ta fad’a kan bed ta fasa kuka mai cin rai,,
tana tunnin abinda tayiwa Naseer akan Zainab bata kyauta ba,
shi saboda ita ya hak’ura da zafin zuciyarsa, ya kuma danne k’in dayake yiwa Zainab yasa sunanta saboda farin cikinta,,
meyasa itama bata bi zab’insa dan farin cikinsa?
meyasa bata fara tambayar shi zab’in ransa akan sunan daya san sawa yarinyar sa ba?
meyasa tayi haka?
Ta k’ara fashewa da kuka, sai da tayi kukan harta gaji sannan ta mik’e ta nufi bedroom d’insa idanuwanta duk sun kumbura sunyi ja,
a parlor ta iske shi, ya kwanta akan sofa had’i da lumshe idanuwansa yana sauraran karanta Qurani,,
a hankali ta zube a gabansa bisa gwiwoyinsa had’i da fashewa da kuka,
da sauri ya bud’e idanuwansa yace ” Zarah lafiya meke damunki?
baki da lafiya ne?
Yayi maganar a lokaci d’aya, cikin kid’ima,
ta kasa yin magana sai kukan datake yi, a hankali ya d’ogota ganin idanuwanta sunyi masifar yin ja sun kumbura ne ya k’ara d’aga mai hankali,,
a rud’e ya shiga tambayarta abinda ke damunta,
a hankali cikin muryar kuka tace ” I really sorry, am so sorry,
“da kikayi min me? kike bani hak’uri,
cikin kuka tace ” ni dai dan girman Allah kayi hak’uri ka yafe min,
idan baka san sunan ka canja dan Allah,
rungume yayi a k’irjinsa yana sauke ajiyar zuciya had’i da bubbuga mata bayanta yana rarrashinta, kawai batare dayace komai ba,
a hankali ta d’ago kai cikin kuka tace ” ka tamabayi ni har kai sun fi ka,,
wallahi duk duniya bani da kamar ka,
kai ne, uwata, kai ne ubana, ka so ni a lokacin da kowa ya k’ini,
baka tab’a juya min baya ba, kai haske ne a rayuwata, kaine, rayuwata, duniyata, farin ciki da walwala ta kai ne komai nawa,
ina sanka fiye da komai da kowa,
you are my everythings, I love you more most,
ban iya had’a ka da kowa a rayuwata,
ban iya had’a sanka da komai a duniya,
ta k’arashe maganar cikin kuka,
a hankali Naseer ya maida ita jikinsa yana murmushin jin dad’i,
cike da matsanancin farin ciki ya shiga rarrashinta,
dan shi dama a maganar babu abinda yafi b’ata masa rai sai cewa datayi bata da Mannir da Zainab a duniya,
tun da nan Zarah da Naseer suka shirya suka d’inke suka koma fiye da baya,,
suka shiga nunawa junan su tsantsar so da kulawa,
babu mai b’ata ran wani, kowa burinsa ya farantawa d’an uwansa.