
BAYAN SHEKARA D’AYA
Sosai Nailah tayi, dan har ta fara tafiya da magana irin ta yara,,
yayinda sosai Dady ya matsawa Naseer akan ya dawo Nigeria,
sosai Dady da Momy suka yi masifar matsa masa lamba akan lalle sai ya dawo Nigeria,
a rana Dady da Momy sai su kira shi yakai sai 10 suna nanata mishi maganar lalle ya dawo Nigeria,
yauwa suna zaune wayar Naseer tayi ringing, a hankali ya kalli wayar sannan ya kalli Zarah,
murmushi tayi dan tasa kowaye, itama a ranta tana maaifar san komawa Nigeria musamman ma yanzu data tara iyali,
kuma tasan ganin Ikram, Momy, Dadynta, da kuma Abbanta,
da sallama a bakinsa ya d’aga wayar,
jin muryar Momy na kuka yasa Naseer saurin mik’ewa had’i da cewa ” Momy lafiya dai?
Cikin kuka tace ” Naseer Dadynka bashi da lafiya sosai,
sai dai a kwantar dashi a taya, ko hannunsa baya iya motsawa,
Naseer ko wanda ke kansa Alhaji baya iya ganewa ta k’ara fashewa da kuka,
ai take hankalin Naseer yayi mugun tashi, gaba d’aya jikinsa ya d’auki muguwar tsuma da kerrrma,,
ganin haka yasa Zarah mik’ewa itama tana kallansa dan tasan ba lafiya,
gabanta ya shiga fad’uwa yana dukan uku-uku addu’arta d’aya Allah yasa ba wani mummunan abun ne ya faru ba,,
cikin tashin hankali Naseer yace” Momy bashi wayar, k’ara fashewa da kuka tayi tace ” tayaya zai iya amsar wayar bayan bai ma san inda kansa ba,
balle yasan wanda ke kansa, cikin kuka ta kuma cewa ” dama last week da muna magana yace wata k’ila rabon ganawar mu da Naseer ne ya k’are,,
bamu da rabon sake ganin juna ido da ido,
idan na mutu ya ai dolensa yazo, Momy ta k’arasa maganar cikin rikitaccen kuka.
Cikin tashin hankali Naseer ya kashe wayar dan bazai iya jure sauraren kukan Momyn sa,
a firgice Zarah ta kalle shi tace ” lafiya kuwa?
Idansa wanda ya gama yin ja ya kalle ta dasu had’i da cewa ” Dady ne ba lafiya sosai, yayi maganar muryarsa na cracking,,
da hanzari yace “had’a mana kayan mu, yayi maganar yana saka kayansa,
yana gamawa ya d’auki wayarsa da key d’in mota yayi waje.
Momy na kashe wayar ta kalli Dady dake zaune gefe yana shan fruits,,
tace ” nasan acikin satin nan zakaga shi, dariya Dady yayi had’i da cewa MATA!!! kenan akwai basira,,
kinga ni ai nayi na gaji amma ke kina gwadawa gashi anyi nasara,
murmushi kawai Momy tayiwa Dady batare data k’ara cewa komai ba.
Kasancewar a kwai kud’i a ranar Naseer ya gama musu komai na tafiya,,
ba shi ya dawo gida ba sai wajen 1:30am,
a parlor ya iske ta tana ta safa da marwa tana tunnin ko yana lafiya, dan bai tab’a kaiwa wannan lokacin a waje ba, gashi dama a birkice ya fita,,
ko had’a kayan ma su Warda da Rosling tasa suka shirya musu gaba d’aya kayan su dana yaran,
kayan Naseer kawai ta iya shiryawa da kanta, a waya ta kira Doctor Jennifer ta sanar da ita halin sa ake ciki,
tana ganin shi ta k’arasa da sauri tana sauke ajiyar zuciya,
sannu da zuwa tayi masa had’i da kai shi bedroom yayi wanka ya shirya, sannan ta kai mishi abinci yad’an ci kad’an,
kallanta yayi cikin sanyin murya yace ” gobe around 11:00am jirgin mu zai tashi,
kai kawai ta d’aga masa,,
sai can kuma tace ” ya zamuyi da su Warda?
Shiru yayi yana d’an nazari kafin yace ” dole sallamar su zamuyi dan bamu san lokacin da zamu dawo ba,
tace ” nima dai haka nake ganin yafi sauk’i.
Washe gari tun asuba Zarah ta tashi ta fara shi, tana k’ara kintsa komai,,
k’ara kiran Doctor Jennifer tayi ta sanar mata time d’in dazasu tashi,
itama da wuri ta shirya ta zo gidan,
tare suka gama shirya kayan,
around 10:00am Naseer ya fito bayan ya gama shirinsa sannan yasa su Warda suka kai musu gaba d’aya kayan su mota,,
bayan sun gama shirya kayan a mota ne, Naseer ya basu kud’i masu yawan gaske sannan ya sallame su,
sukayi godiya sosai had’i da bak’in cikin rabuwa da iyayen gida adalai na gari,
key d’in gidan Naseer ya bawa Doctor Jennifer yace” mata please kiyiwa mai gidan bayani sannan kice masa na saki gidan,
dan Allah kad’ai yasan ranar dawowarmu,
amsar key d’in tayi had’i da cewa “okey,
a Airport sosai Doctor Jennifer da Zarah suka sha kukan rabuwa, kamar ransu zai fita haka suka rink’a risgar kuka,
gwanin ban tausayi, har suka shiga jirga, jirgin ya d’aga Doctor Jennifer na nan tsaye tana sharar kwalla,
haka Zarah acikin jirgin taita kuka,
sai da yaran suka dameta da tambayar abinda ke damunta sannan tayi shiru.
Dama hausawa sunce sabo turken wawa
NIGERIA ???????? (K’ASAR MU TA GADO)
K’arfe 5:40 jirgin su yayi landing a Aminu Kano International Airport,
Zarah na fitowa daga cikin jirgin ta shak’i daddad’an iskar k’asarta abin alfaharinta,
ta lumshe ido had’i da sauke ajiyar zuciya mai k’arfi wacce har sai da Naseer ya kalle ta,,
murmushi tayi masa, shima ya mayar mata da martanin murmushin batare da kowa yace komai ba,
sai yaran dake ta faman surutu, Naseer ya rik’e hannun Noor da Nouwaf, Zarah na rik’e da Na’eem da Nailah,
suna fita harabar Airport d’in Naseer ya hango driver’n su,
da sauri ya nufe.
Cak Zarah ta tsaya had’i da rik’o hannunsa cikin nata tana kallansa,
shima tsayawar yayi had’i da kallanta,
cikin rawar murya tace ” Sweetheart ya zamuyi dasu Noor da Nouwaf? kasan fa ba’a san dasu ba,
tun da har yanzu babu wanda yasan ni ainahin Zarah………..
MOMYN ZARAH
GADAR ZARE!!!
(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)
~NA~
HAUWA A USMAN
JIDDARH
????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
GARGAD’I
MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA
~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO
BEST FRIEND FOREVER & EVERZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~
70
Shiru Naseer yayi na d’an wani lokaci,
kafin yace ” cikin biyu dole ayi d’aya ya k’arasa maganar yana kallan ta,
itama shi take kallo idanta cike da alamar tambaya,
tace ” uhnnnn ina jinka,
ajiyar zuciya Naseer ya sauke sannan yace ” ko dai mu sanar dasu Momy gaskiyar al’amari ko kuma mukai su Nouwaf da Noor gidan Asheer abokina,
kallansa Zarah taci gaba dayi batare datace komai ba,
“ya kuma kika yi shiru? cewar Naseer yana kallan ta,
ajiyar zuciya itama ta sauke had’i da kallan yaran tace ” hmmmm kana ganin kai su gidan Asheer d’in shine mafita?
Murmushi Naseer yayi wanda ya k’ara fito da tsantsar kyan fuskarsa gami da yarintarsa,
sannan ya kalle ta yace ” ni fa zab’i na baki dan ma karna yanke hukunci kai tsaye kiga kamar banyi maki adalci ba,
“to amma dai kasan halin Na’eem da shegen surutun tsiya kana ganin bazai fad’a ba?
shiru Naseer yayi yana ci gaba da kallanta,
dan ya gano manufarta, san rabuwa da yaranta ne batayi shine take ta wannan ‘yan kame-kamen,
cigaba da magana Zarah tayi ” kuma kasan a yadda suka saba a tsakaninsu ma babu yadda za’ayi a raba su kasan bazasu tab’a jin dad’i ba matuk’ar basa tare da junan su,
shi dai Naseer ido kawai ya zuba mata yana kallan yadda take ta faman rirrik’e su kamar wani zai kwace mata yaran.
Kwata-kwata Zarah bata kula da yadda Naseer ya zuba mata ido ba,
ta cigaba da magana ” kuma ma ni banga wani amfanin b’oyewa ahalin mu gaskiyar al’amari ba,
tun da dai mai afkuwa ta rigada ta afku,
kawai mu sanar dasu gaskiya dan ina ganin hakan ne kad’ai mafita,
dan…….. d’ago kanta datayi taga yadda Naseer ya zuba mata idonunsa ne ya hana ta k’arasa fad’ar abinda tayi niyya,,
hannuwanta ta hard’e a k’irjinta, ta zuba masa idanuwanta itama had’i da d’aga masa gira d’aya,
murmushi yayi had’i da cewa ” oh ikon Allah wai su Zarah har an san dad’in ‘ya’ya,
Oh ni Naseer yau naga ikon Allah, ya fad’a yana dariya,
cikin shagwab’a ta tab’e baki had’i da fara diddira k’afarta a k’asa,
dariya Naseer yake sosai yama kasa magana, sai Na’eem ne yace ” sorry sweet Mom, Dady ne ko?