GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin dariya Naseer ya shafa kansa had’i da cewa ” no son, bani bane ku ne,
ya fad’a yana nuna sauran yaran,
Noor tace ” Dad me muka yi mata?

” Sanku ne yayi mata yawa harta manta da kanta tana ‘yan kame-kame,
sosai Zarah ta fara kukan shagwab’a had’i da cewa ” Allah ba haka bane, kawai bana san a raba min kan yara na ne,
kuma gashi sun riga sun saba da junansu, idan aka raba su bazasu ji dad’i ba,
tayi maganar cike da shagwab’a da yarinta,
dariyarsa Naseer ya kanne ganin da gaske kukan takeyi yace ” ayya na fahimce ki, I’m so sorry nine ko?
ya fad’a yana goge mata hawayen fuskarta, had’i da rungume ta a k’irjinsa,
” to yanzu dai meye mafita? tunda naga baki san rabuwa da yaranki abar maganar kai su gidan Asheer,
a sake samo mafita,
da sauri Zarah ta d’aga kanta daga k’irjinsa tace ” yawwa, kasan meya kamata ayi?

“A’a Naseer yace yana kallanta,
” kawai muce yaran sister nace, shine da zamu taho suka mak’ale suka ce sai sun biyo mu,
saboda akwai shak’uwa da sabo sosai a tsakanin su da Na’eem,
kuma ko can Holland yawanci sunfi zama a gidan mu wajen Na’eem ko school d’insu d’aya kuma tare suke zuwa,
ta k’arasa maganar tana kallan kwayar idansa,
ajiyar zuciya Naseer ya sauke had’i da cewa ” wow that is amazing, gaskiya wannan shawarar taki tayi,
kanki yana ja sosai, ya fad’a yana yi mata murmushi,
Zarah ta bud’e baki zatayi magana, Noor tace ” I’m very tired Mom, my legs are shaking and I need to rest,
Nouwaf ma yace ” I’m very hungry Dad,
da sauri Naseer da Zarah suka saki juna had’i da kama hannun yaran suka k’asara inda motar take suka shiga.

Zainab da tun ranar da Mannir ya dawo ya sanar da ita Naseer da Na’eem sun tafi batare daya samu damar d’auko mata Na’eem ba,
ta shiga cikin matsanancin hali da muguwar damuwar da suka haifar mata da ciwo
wanda kusan kullum a kwance take yau da lafiya gobe ba lafiya,
kwata-kwata bata iya cin wani abincin kirki, ta daina kwalliya, wanka kawai take yi, ko mai bata shafawa balle hoda,
dan wani lokacin ma dakyar Mannir ke matsa mata tayi wanka ta canja,
sosai tayi muguwar rama ta k’ek’ashe kallo d’aya zakayi mata ta baka mugun tausayi duk tsananin k’iyayyar da kake mata,
ga gidan ita kad’ai dan har lokacin Ikram tana gidan su Momy da Dady,
idan Mannir ya tafi aiki sai gidan ya zame mata so lonely,
duk kewar yaran ta ya dame ta, taji kamar tayi hauka,
danasani da danama ko tayi su sunfi dubu, dan ba k’aramin hauka da kuka tayi ba, har dai daga k’arshe ta dangana,
tun da Mannir ya sanar da ita Naseer zaizo da matarsa daya aura acan gabanta keta muguwar fad’uwa,
haka nan taji wani mugun tsoro da fargaba sun shigeta a lokaci d’aya.

Sosai taji hankalinta yayi mugun tashi, hankalinta yak’i kwanciya,
ranar da su Zarah zasu iso kuwa ji tai gaba d’aya jikinta ya d’auki rawa da kerrrma gami da muguwar tsuma,
haka nan taji ta shiga mugun tashin hankali, gabanta ya tsananta fad’uwa,
amma duk da haka da Mannir yace mata tazo suje gida taryar Naseer k’iyawa tayi,
saboda yadda take jin jikinta, lokaci d’aya zazzab’i da ciwon kai mai mugun zafi ya shigeta,
ta shiga rawar sanyi tana kerrrma a cikin bargo wanda ita kanta ta rasa taka mai-mai dalilin faruwar hakan,
wannan dalilin ne ya hana Mannir zuwa tarbar su Naseer ya tsaya jinyar matarsa.

Motar su Zarah nayin parking a harabar gidan gabanta yayi muguwar fad’uwa,
take ta shiga zubar da kwalla had’i da sauke ajiyar zuciya da k’arfi,
hannunta Naseer ya rik’e gam cikin nashi had’i da zuba mata idan shi cikin nata,
cikin sanyin murya ya kira sunanta ” Zarah,
a hankali ta d’ago kanta ta kalle batare datace komai ba,
yayinda hawaye keci gaba da zuba daga idanta,
hannu Naseer yasa yana goge mata hawayen yace ” Zarah you have to be very strong until we done our plan,
kika iya jure rashin mijinki dana d’anki na cikin ki wanda kika durk’usa kika haifa da kanki ma,
balle wasu mutane k’alilan, dan Allah ki daure ki kawar da kanki daga kan kowa,
ki jure ki bani had’in kai, kamar yadda kika jure a abaya please,
kai ta d’aga masa had’i da cewa in sha Allah I will try my best,
” yawwa my matar, ya fad’a yana goge mata hawayen ta, sai da ta saita kanta sannan suka fito suka jera rik’e da yaransu,
cike da tsokana Naseer ya kalle ta yace ” yawwa ko kike fa, ai daman nasan zaki iya tunda kika iya jure rashin mijinki da kuma…… ya fad’a yana kanne mata ido d’aya had’i da d’age mata gira d’aya,
basarwa Zarah tayi itama tace ” me kenan?

Dariya yayi sannan ya kalle ta yace ” ai nasan kinyi mugun missing d’inta,,
“ni fa bangane abinda kake nufi ba, Zarah ta fad’a tana kallanshi ido cikin ido,
hantsar wandonsa ya kalla had’i dayi mata nuni da hannunsa yace ” nan!
baki ta tab’e had’i dayin rolling lulu eye’s d’inta tace ” still am don’t understand what you mean,
kai tsaye Naseer yace “Buret!
wani guntun murmushi Zarah tayi had’i da dafe k’irjita tace ” abin amaii, ni bana so akai kasuwa,
dariya Naseer yayi sosai sannan yace ” ah wallahi k’arya ne, tunda har akan bani maganin k’arfin maza saboda tsabar jaraba da kuma missing d’in buret, kina so a ci ki takai miki karo kiji ta har wuya,
aiko kin ciyu, kin had’u da jarumin jarumai,,
, zakin zakuna, ingarmar maza, gwarzon namiji tayi miki fata-fata,,
har da su zuwa hospital jinya,
cikin shagwab’a Zarah ta kai masa duka Naseer ya goce yana dariya,
dai-dai loakcin Dady da Momy suka fito.

Momy na d’ora idanta akan Zarah tayi baya zata fad’i saboda tsabar kid’ima da tsananin rud’ewa,
cikin firgici Dady ya taro ta, duk da shima kad’an ya rage ya zube k”asa wanwar, dan hankalinsa yayi mugun tashi,
daga Zarah har Naseer sun lura da yanayin dasu Dady suke ciki amma sukayi fuska kamar ba wani abu,
cikin fara’a Naseer ya nufe su Dady amma Momy tayi sauran ja da baya had’i da rik’e hannun Dady gammm cikin nata,
ganin haka yasa Naseer yin dariya had’i da cewa Momy yau kuma tsoron Naseerun ake yi?

Cikin wani irin yanayi na rashin yadda ta d’ago idanta tana kallan Naseer,
idanta cike da tuhuma, shima Dady kallan rashin yadda yake yi masa, da kwata-kwata bai yarda da shi ba,
ganin kallan da suke yi masa yasa shi yin murmushi had’i da nuna Zarah yace ” Linah this is my home an my family, they’re my parent,
murmushi tayi wanda ya k’ara bayyanar da ainahin kamarta ta zahiri tace ” nice to meet you,
tayi maganar tana kallan Dady da Momy,
daga Dady har Momy babu wanda yace k’ala sai ido kawai da suka zuba musu suna kallan wasan kwaikwayon had’i da zunzurutun rainin hankalin da suka zo musu dashi,
cikin shagwab’a Naseer yace ” Momy no missing hug, ya fad’a yana ware hannuwansa,
har lokacin babu wanda yace komai tsakanin Dady da Momy kallan Naseer da Zarah kawai suke yi,
cikin muryar kuka Nouwaf yace ” Dady I’m very hungry,
da sauri Na’eem yace ” me too Dad,
ita kuma Noor tace ” me am so tired, ta fad’a tana dafe kanta kamar wata babba.

Sai a lokacin Dady da Momy suka lura da yaran,
fafare tass b’ul-b’ul dasu abin sha’awa,
kallan yaran Dady yayi sannan ya mayar da kallansa ga Naseer batare dayace komai ba,
Naseer ya gane kallan tambaya Dady yayi masa amma sai basar yace ” oh am so sorry dears muje ciki kuyi wanka lunch sai kuyi bacci,
Nouwaf yace ” no Dad is better to take our lunch first, then bath and sleep,
ok Naseer yace, had’i da rik’e hannun su yayi cikin gidan dasu,
bayansu Momy da Dady suka bi da kallo had’i da sauke nannauyar ajiyar zuciya,
direct part d’insa suka wuce dan yasan an gyara, kamar yadda ya zata hakan ne ya kasance an gyara part d’in tass an canja komai, even paint sai da aka sake,
Furniture ko sabo aka saka, even spoon sabo ne,
3 bedrooms including toilet an bathroom, an 1 parlor with kitchen an dinning area,
inda yaga an saka gadan yara da wardrobes d’in su, yakai kayan su Nouwaf & Noor da Na’eem,
bedroom d’in kusa da yaran Zarah ta kai kayanta,
shi kuma ya d’auki bedroom d’in dake can gefe,
komai na gidan neat, Zarah ta ajiye kayanta a bedroom d’inta bata ko zauna ba ta yi bedroom d’in Naseer,
iske shi tayi shima yana k’ok’arin fitowa, da sauri Zarah tasa hannu ta tura shi baya, had’i da rufe k’ofar.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button