GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Da kallan mamaki ya bita “ya naga kin shigo kuma kin rufe k’ofa, kodai jarabar ce ta motsa? yayi maganar yana sakar mata silent killer smile ,
” no ni ba wata jaraba, kawai dai ina san muyi magana ne,
” amma dai ai kinji me yaranki suka ce ko?
dan haka kibar maganar sai sun ci abinci, sun huta tukunna,
yayi maganar yana k’ok’arin barin d’akin,
da sauri ta tari gabansa had’i da cewa ” amma kana ganin su Momy bazasu gane ba?

“Ya danganta da yadda kikayi reaction d’inki, yayi maganar yana barin d’akin,
direct bedroom d’in yaran ya shiga ya iske basa nan har sun koma part d’in su Dady,
da sauri shima yayi part d’in Zarah na biye dashi a baya har suka k’arasa part d’in,
iske su sukayi zaune a dinning gaba d’ayansu har da Momy da Dady,
murmushi Naseer yayi sannan ya k’arasa wajen ya zauna shima,
bayan sun gama cin abinci, Naseer da Zarah suka koma part d’in su, sukayiwa yaran wanka had’i da shiryasu, sai da sukayi bacci sannan Naseer da Zarah sukayi wanka, had’i dayin sallah,
sannan suma suka kwanta dan a gajiye suke lik’is.

Washe gari sai around 9:30am suka fito bayan sun shirya,
basu iske yaran a bedroom d’in su ba dan tuni sun tashi sun fita, har sunyi breakfast Ikram tayi musu wanka,
a parlor suka iske Momy da Dady zaune su biyu kawai suna hira,
tare suka k’arasa wajen su had’i da durk’usawa har k’asa suka gaida su,
fuska a sake Dady da Momy suka amsa kamar ba komai a ransu,
nan ko a k’agare suke ayi musu bayani dan ko bacci basuyi ba,
kwana sukayi suna alhinin abin,
Dady yace ” ga breakfast d’in ku can kan dinning kuje kuci,
ba musu suka mik’e dan wata irin muguwar yunwa suke ji dan kwana akayi ana duty (kashe arna),,
bayan sun gama breakfast d’in parlor suka dawo suka zauna inda Dady da Momy ke zaune,
a hankali Naseer ya d’aga kai yana waige-waige, murmushi Momy tayi dan ta kula da yaran yake nema, tace ” oh su Naseer manyaan gari har an san dad’in ‘ya’ya,
ai tuni sun tashi sunyi breakfast,
tunda naga alamun yaran suna riga iyayen su tashi,
kai ya shafa yana murmushi batare dayace komai ba,
itako Zarah kanta ta sunyar k’asa saboda kunya,
Dady yace ” ai su Naseer an girma an zama manya,
cikin shagwab’a Naseer ya d’ora kansa kan cinyar Momy yana cewa ” Momy ai har yanzu ban girma ba ko? yaro ne still a wajenki har yanzu,
dariya Momy tayi tace ” ka tab’a ganin mutum yayiwa iyayen sa girma duk tsofansa?

” ai duk tsufan mutum matuk’ar yana da iyaye jinsa yake kamar yaro k’arami musamman ma idan yana gaban iyayen nasa,
sai da sukayi wasa da dariya sosai sanann Dady ya kira sunansa “Naseer,
yanayin yadda Dady ya kira sunansa yasa Naseer sanin cewa he is serious about what he want to say,
it’s an important issue, dan haka ya tashi zaune had’i da tattsara gaba d’aya nutsuwarsa ga Dady yace ” na’am,
ajiyar zuciya Dady ya sauke kafin yace ” Naseer ni dai a sani na, yaranka biyu ne, na farko Na’eem sai kuma Nailah,
amma yanzu na ganka da yara har hud’u wanda kallo d’aya zakayi musu asan suna da nasaba da kai,
kuma a iya sani na Zarah ta mutu dan da hannunmu muka saka ta a kabari,
amma yanzu ga Zarah a gaban mu, dan Allah Naseer ka warware mana zare da abawa,
murmushi Naseer yayi sannan yace ” yaran sister Linah ne……. daga nan ya sanar dasu plan d’in da suka shirya akan yaran,
sannan yace ” Dady kai ka haife ni nasan kuma shekarunka sun ninka nawa sau uku,
Dady a iya tsayin rayuwarka ka tab’a ganin wanda ya mutu ya dawo?

Murmushi Dady yayi sannan yace ” a’a ban tab’a gani ko naji labarin mutum yayi mutuwar gaskiya ya dawo ba,,
amma nasha jin labari na kuma sha ganin mutum yayi mutuwar k’arya,
na wani lokacin kafin ya bayya saboda wani dalili,
da k’arfi Naseer ya sauke ajiyar zuciya da har sai da su Dady sukaji sautinta, a ransa yace lalle babba babba ne, wanda kuma ya rigaka zuwa duniya dole ya fika sanin takan rayuwa,
a fili kuma yace ” to kuma Dady har asaka mutum a kabari?

” Sosai ma kuwa, long sleep injection ake yiwa mutum, cewar Dady ya k’arasa maganar yana kallan Naseer,
murmushin yak’e Naseer yayi sannan yace ” to amma Dady kai kana ganin hakan zata iya faruwa da Zarah?

Dady ya bud’e baki zayyi magana yaran suka fito da gudu, daga bedroom d’in Ikram,
jikin Zarah suka fad’a suna cewa ” we missed you sweet Mom, kafin
Zarah tayi magana Dady yace ” they are her niece and they call her Sweet Mom,
da sauri Naseer yace ” eh Dady haka suka ji Na’eem na kiranta, kuma sunfi zama a gidan mu fiye da gidan su shiyasa suke kiran mu,
sweet Mom & sweet Dad,
Noor tace ” sweet Dad Aunty tayi mana wanka,
cikin rashin fahimtar wacece Aunty ya kalli Momy,
murmushi Momy tayi had’i da cewa ” oh Ikram suke nufi, da sauri Zarah ta d’ago idanuwanta,
Naseer yace ” tana nan ne?

“Eh tana nan tun bayan mutuwar Zarah take fushi da iyayen tak’i zuwa gidan ko sau d’aya,
ko nan suka zo iyakacinta dasu gaisuwa, ko parlor bata fitowa kullum tana bedroom,
rana d’ai-d’ai ne bata kukan rashin ‘yar uwarta Zarah,
ta hanawa kanta duk wani jin dad’i ta takure kanta,
tayi maganar idanta yana kan Zarah,
shiru kawai Zarah tayi, dan ita kad’ai tasan me take ji a zuciyarta,
Naseer yace ” to su iyayen nata fa?

Ajiyar zuciya Momy ta sauke cike da jimami tace ” hmmm Naseer ai idan kaga Zainab yanzu sai kayi mata kuka,
ta goje, ta kod’e, ta rame, ta k’ek’ashe, tayi muguwar rama,
tun bayan mutuwar da Zarah da tafiyarka da Na’eem ta shiga mummunan tashin hankali had’i da matsananciyar damuwa,
har hawan jini ta kamu dashi, tanan yau da lafiya gobe ba lafiya,
baka ga yadda ta koma, ta takura kanta da rayuwarta had’i da k’untata duniyarta, ta hana kanta farin ciki da walwala,
tana ta azabtar da kanta, ta hanawa kanta jin dad’in duniya,
kuma tana cikin k’uncin rayuwa,
Momy tayi maganar cikin mutuwar jiki, idanta nakan Zarah,
aiko take Zarah taji hankalinta yayi mugun tashi, jikinta ya d’auki rawa da kerrma,
launin idanuwanta suka canja daga farare zuwa ja,
ta rink’a jin zafi gami da k’una a k’irjinta yayinda zuciyarta take tafasa, mak’ogwaranta na tiriri saboda jin halin da Momynta Zainab ke ciki,
Naseer ko baki ya tab’a had’i da cewa ” hisabi ta fara yiwa kanta kenan?

Jin abinda yace yasa Zarah yunk’urawa zata tashi,
da sauri Naseer yasa hannunsa ya danne hannunta batare daya kalle ta ba,
dole tasa Zarah ta zauna, amma Allah kad’ai yasan zugi da azabar da zuciyar ta keyi mata.

Washe gari jikin Zainab yayi d’an sauk’i yasa Mannir cewa Zainab ta tashi suje gida kar su Dady suyi fushi dasu kan basu je taryar Naseer ba,
da farko k’in zuwa tayi sai da Mannir yace mata kodan Na’eem ai taje,
jin abinda yace yasata mik’ewa zumbur had’i da surar hijabinta tayi gaba,
murmushi Mannir yayi sannan yabi bayanta,
tunda suka nufi gidan gabanta yake muguwar fad’uwa had’i da bugawa da tsananin k’arfin gaske,
suna shiga harabar gidan gabanta ya kuma fad’uwa da k’arfi,
koda sukayi parking kasa fitowa tayi, tayi shiru a mota tana sauraren yadda k’irjinta ke bugawa da k’arfi,
har sai da Mannir yayi mata magana sannan ta fito cikin sanyin jiki, suka shiga main parlor gidan.

A parlor ta iske yaran suna wasa, da sauri ta k’arasa inda suke had’i da rungume Na’eem gamm a jikinta had’i da sakin kuka,
tana d’aga kai ta hango Naseer yana k’ok’arin barin wajen, da sauri ta mik’e had’i da nufar wajen,
tsaiwarsa Naseer ya gyara yana jiran ta k’oraso dan dakowacce tazo yana dai-dai da ita,
tana zuwa ta rungume shi had’i da sakin rikitaccen kuka mai cin rai tana cewa ” Naseer I made a mistake, I’ll never forgive me self, ever Naseer,
munyi rashin da har abada bavzamu tab’a mayar da kamar shi ba,
na cuci kai na, nayiwa kai na illar da har in mutu bazan manta ba,
Ikram dake bedroom jin maganar Momynta yasa ta fitowa,
yadda take kuka ya tab’a zuciyar Ikram sosai, ta fara zubar da kwalla batare data sani ba,
Naseer ji yayi zuciyar sa tayi mugun yin sanyi har yaji mugun tausayinta ya shige shi,
a hankali ya cireta daga jikinsa ya zuba mata ido, sai lokacin ya kula da yadda ta koma,
tayi mugun bak’i ta rame, kamar wacce ta shekara tana jinyar HIV & blood cancer,
gaba d’aya ta yarkwale ta lalace,
ji yayi duk wannan zafin zuciyar da k’iyayyar da yake yi mata sun gushe,
lokaci d’aya kuma tsananin tausayinta ya mamaye duk wata gab’a da jijiya had’i da gangar jikinsa,
a hankali ya shiga goge mata hawayen dake zubowa yana girgiza mata kansa alamar ta daina,
dai-dai lokacin idan Ikram ya sauka akan Zarah dake shigowa part din,
ji tayi kanta yayi dum durum dum,
cikin tsananin tashin hankali bakinta na wara tace ” Z… A… R… A… H!!! had’i da sulalewa k’asa sumammiya,
da sauri Zainab ta juya had’i da sauke idanta akan ZARAH…………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button