GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

MOMYN ZARAH

GADAR ZARE!!!

(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)

       ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

GARGAD’I

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO

BEST FRIEND FOREVER & EVER
ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~

72

Wani mahaukacin bugu suka yiwa k’ofar dayasa ta b’alle,
babban cikin su yasa yaransa su shiga ciki su yo masa waje da mutanen gidan,
su Zainab na k’ok’arin b’uya aka banko k’ofar d’akin da k’arfin tsiya,
zagaye su ‘yan fashin sukayi da bindigogi suka tusa k’eyarsu zuwa parlor inda babban su yake zaune ya d’ora k’afa d’aya kan d’aya,
da k’arfi aka durk’usar da su Mannir a gabansa,
sai da ya gama k’are musu kallo kafin yace ” ina kud’in daka shigo dasu jiya?

Yayi maganar cikin izza da wulak’anci,
cikin rawar baki Mannir yace ” ni ban shigo da wani kud’i jiya ba,
gyara zamansa yayi sannan yace ” kaga ba wani abu ne ya kawo mu ba,
ba kuma b’ata lokaci ne ya kawo mu ba, bana san raina ya b’aci,
kuma bana san nayi loosing control d’ina dan idan nayi komai yana iya faruwa,
amma idan ka bamu salin alin zamu tafi batare da munyi muku komai ba,
da ka bamu da tuni munyi tafiyar mu, amma idan kace zaka tsaya b’ata mana lokaci kayi mana gardama wallahi sai nayi maka hukunci mai tsananin gaske,
ta yadda har ka mutu kana nadama da dana sani,
cikin kuka Zainab ta kalle shi tace ” dan girman Allah ka rufa mana asiri ka basu duk abinda suke so,
koma nawane ka basu su tafi kamar yadda suka ce please tayi maganar cikin rikitaccan kuka,
cikin tsuma Mannir yace ” wallahi babu kud’i a gidan nan,
sai dai idan check zan rubuta muku,
ko kuma nayi muku transfer ta Bank,,
wani mahaukacin mari shugaban ‘yan fashin ya maka masa,
cikin matsanancin fushi yace ” kama rai na mana hankali, to ka shiga hankalinka dan kaga ina binka cikin sauk’i da lallashi,
zan baka dama ta k’arshe, na kuma yi maka tambaya ta k’arshe wacce daga ita komai yana iya faruwa,
ina kud’in daka shigo dasu gida?

Sugaban ‘yan fashin ya kuma tambayar Mannir,,
cikin tsuma Mannir yace ” wallahi tallahi ba kud’i a gidan nan,
amma ku cake gidan kaf idan har kun gani ku d’auka,
kallan d’aya daga cikin ‘yan fashin babban su yayi sannan yace ” jeka kira shi,
ba musu ya fita, bai dad’e da fita ba suka dawo tare da mai gadin gidan,
kai Mannir ya d’aga yana kallan maigadin gidan,
shugaban ‘yan fashi ya kalli Mannir yace ” waye wannan?

” A tunaninka shi mutumin kirki ne?

“Ko kana tsammanin aikin gadi kawai yake?

” To idan baka sani ba, yau ka sani shi d’an fashi ne, kuma duk gidajan da akayiwa fashi a unguwar nan shi ne,,
da sauri Mannir ya d’ago kai yana kallan mai gadinsa da suka shafe 20yrs tare,
tun da yayi aure yake masa aikin gadi bai kuma tab’a canza shi ba,
cike da mamaki Mannir ke kallansa, cikin rawar murya yace ” Dauda kai ne?

“Dama kai mugu ne mai fuska biyu azzalumi maci ama…… tauuuuuuu,
Mannir yaji an kuma maka masa wani gigitaccan marin , take hancinsa da bakinsa suka fashe,
wanda ya mari Mannir yace ” kai ka isa ka tsaya a gaban mu kana zagin Ogan mu,
idan baka sani ba, ka sani shine leader mu, (Oga) kuma shine Master dan haka ka kama kanka,
murmushi Dauda mai gadi yayi sannan ya zauna akan sofa had’i da hard’e k’afa d’aya kan d’aya,
ya kalli Mannir yace ” Mannir nine shugaban gaba d’aya ‘yan fashin dake Kano State,
ko lokacin daka d’auke ni aiki, a fashi da makami na nake,
kuma abinda yasa nazo gadi gidan nan saboda nayi fashi a gidan,
kasan meya hanani duk tsayin shekarun nan?

Mannir dai kallansa kawai yake batare daya ce komai ba,
Dauda yaci gaba, “saboda halinku na kirki da sanin darajar d’an Adam,
hakanne ya hana ni aiwatar da manufa ta akan ku, danaga unguwar masu hannu da shuni ce sai nayi zamana a matsayin mai gadi, yayinda na addabi gaba d’aya unguwar da fashi, nasan ka riga da kasan haka tunda kai ba bak’o bane a unguwar,
nayi niyyar idan na gama da unguwar nan nayi tafiya ta,
amma sai naga kai ba kamar yadda nayi tsammani bane,
shiyasa nake san d’and’ana maka kai ma kaji idan da dad’i,
Mannir kai har zaka kalli wani kace masa maci amana, azzalumi,
bayan kai ne asalin mugun, tarrrr nake kallanka duk abinda ke faruwa a gidan nan tafin hannuna yake,
duk abinda kake aiwatarwa ina sane dakai,
dan haka ka bani kud’in daka shigo dasu jiya nayi tafiya idan kuma kak’i komai yana iya faruwa,
dan ni kai na ban san mezai iya biyo baya ba.

Jin abinda Dauda yace ” yasa gaba d’aya jikin Mannir ya d’auki rawa da tsuma had’i da kerrma,
cikin tsuma da rawar murya yace ” wallahi tallahi ba kud’i bane,
kayan yara ne na shigo dasu kuma kaje ka duba ka gani,
d’aya daga cikin ‘yan fashin yace ” tabb aiko dole yaran nan su bak’unci lahira dan sun tab’a mana lokaci da target d’in mu,
mari Dauda ya kaima mai yin maganar yace ” ka iya bakinka akan Zarah da duk wani daya shafeta,
dan zan iya sadaukar da rayuwata akan ta,
yarinyar mutum ce, mai saurin manta shirri da rik’o da alkhairi,
yarinyar taga iftila’i da jarabawa iri-iri a rayuwarta,
mugayen mutane da azzalumai sunyi wasa da rayuwarta,
a barta haka ta huta taji dad’in duniya da rayuwarta,
gata da tausayin nak’asata da ita, tana da bala’in jin k’ai da taimako,
dan ko ni tasha taimakamin, haka nan take zuwa waje na musha hirar rayuwa,
tun tana yarinya k’arama muka saba sosai, in banda ni ba mutumin kirki bane da babu abinda zai hana na aure ta,
sai dai ina bala’in tausayin ta, ta yadda aka wulak’anta mata rayuwa, aka cuce ta, aka wargaza mata duniyarta,
amma dayake Allah mai sakayya ne gashi cikin k’ank’anin lokaci ya maye mata gurbin komai,
ya musanya mata bak’in cikinta zuwa dawwamammen farin ciki,,
amma sai da mugu kuma azzalumi ya nakkasa mata rayuwa,
Dauda ya mayar da kallansa kan Mannir yace ” ka fara cin albarkacin Zarah tun yanzu,
dan wallahi badan nasan inna kashe ka zatayi bak’in ciki da matsanancin kuka ba,
da wallahi yau a lahira zaka kwana,
shege kawai Dauda ya fad’a cike da bak’in ciki,
wani daga cikin yaran Dauda yayi dariya yace “Oga dama kasan Allah, kasan tausayi da jin k’an?

Dariya Dauda yayi sannan yace ” nima ita ta koyar da ni, kuma nasan komai daren dad’ewa muma namu k’arshen na nan zuwa,
d’aya daga cikin ‘yan fashin yayi tsaki had’i da cewa “amma Oga kasan bama fita Operation mu koma haka batare da komai ba?

Kallansa Dauda yayi had’i da cewa ” anything for guy’s, kuyi duk abinda kuke so,
dai-dai lokacin Ikram ta fito sanye da slink night gown,
kanta babu d’ankwali gashin kanta ya zuba har gadon bayanta,
hanyar kitchen tayi batare data lura da mutane a parlor’n ba,
gaba d’aya ‘yan fashin suka mayar da hankalin su kanta, suka zuba mata ido,
wani irin muguwar razana Zainab da Mannir sukayi lokacin da suga inda ‘yan fashin suke kallo,
a kid’ime Zainab ta mik’e ta nufi inda Ikram take had’i da rik’e hannunta ta nufi bedroom da ita,
binta kawai Ikram keyi a baya batare data sani ba, dan cikin bacci take,
wata iri gigitacciyar tsawa aka dakawa Zainab had’i da cewa zo nan,
tsawar ce tayi sanadiyyar dawowar Ikram cikin hayyacinta,
aiko tana arba da k’attin ta saki ihuuu,
tsawa aka daka mata had’i da cewa shut up, a tsorace Ikram ta rufe bakinta had’i da k’ank’ame Zainab suna kuka su dukkan su.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button