
Babu wani b’ata lokaci Naseer ya fara k’ok’arin sungumar su,
da sauri Momy ta dakatar dashi had’i da cewa Zarah yi sauri ki d’auko musu kaya,
mik’ewa tayi tana kuka ta d’auko kayan Dady da Naseer suka fita,
Zarah da Momy suka saka musu kayan, sannan akayi hospital dasu,
wajen 2hrs kafin aka fito dasu daga emergency, dukkan su babu wacce ba’ayi d’inki ba,
dan sunji ciwo, Doctor daya fito daga Emergency room d’in Dady yayi saurin tararsa yana tambayarsa abinda ke faruwa,
Doctor yace ” gaskiya fyad’e aka yi musu, kuma ga dukkanin alamu maza da yawa ne suka yi musu fyad’en ,
kuma duk wand’anda sukayi haka basa su da tausayi dan kwata-kwata basu saka imani ko jin k’ai ba,
Doctor yayi maganar yana cire lab cot d’in jikinsa,
daga Dady har Naseer kasa magana sukayi sai Zarah dake ta aikin kuka,
bayan an kai su d’aki an kwantar dasu Doctor ya basu umarnin shiga,
har Doctor zai fita Nasser yace ” shi namijin fa?
Doctor yace ” babu wata matsala shock kawai ya samu daya sa brain d’insa yin hocked,
Sosai Ikaram tasha jinya dan takai wajen 3week a hospital kafin ta warke,
ita Zainab duka-duka bata fi 5days ba ta warke,
Zarah kam an shiga mummunan tashin hankali saboda abinda ya faru,
sai daga baya bayan Mannir ya dawo hayyacinsa ya fad’a musu duk abinda ya faru,
sosai Dady yayi mamakin jin Dauda ne yayi wannan aika aikar,
Mannir bai b’oyewa iyayensa ciwon dayake damunsa ba, ya sanar dasu akan su tayashi da addu’a,
sosai suka shiga matsananciyar damuwa duk gidan kowa ka gani baya cikin walwala,
tun da abin ya faru Ikram ta shiga ciki k’unci, kullum cikin kuka da bak’i ciki take,
babu yadda Zarah bata yi ba, akan tayi hak’uri ta dangana da rumgumi k’addara ba,
amma ina Ikram na cikin tension da matsananciyar damuwa,
duk ta rame ta fige kamar ba ita ba,
Zainab ko ba’a magana, ta zama kamar skeleton tayi mugun bak’i,
itama kullum cikin kuka take.
BAYAN WATA UKU
Sosai ciwo yaci gaba da cin jikin Mannir dan yanzu ciwon har ya gama kama gaba d’aya al’aurarsa har zuwa d’uwawonsa,
ga wani irin ruwa mai yauk’i da tsinannan d’oyi dake zuba daga jikin Mannir,
wanda yafi nada wari da d’oyi,
dan yanzu kwata-kwata ya dai na shiga jama’a ko masallaci baya zuwa,
saboda wari da ruwan gembo, sai da yaje k’asashe har 4, India, Dubai, Germany, China,
amma duk a banza idan ma anyi aikin ba’a samun wata nasara sai rincab’ewa ma da ciwon ke k’ara yi.
Wani irin mugun zazzab’i da matsanancin ciwon kai Zainab ke fama dashi, kwata bata jin dad’in komai,
Mannir yayi taje asibiti tak’i har ya gaji ya kyaleta,
Dady ne ya kira Mannir a waya yake sanar dashi matsananciyar rashin lafiyar da Ikram ke fama da ita,
a kid’ime Mannir ya sanar da Zainab abinda ke faruwa,
itama cikin tashin hankali ta mik’e, jikinta na rawa, ta d’auko hijab sukayi gidan Dady,
dan tun da abin ya faru Zainab bata saka Ikram a idan ta ba.
A harabar gidan suka iske Dady da Naseer, Momy, Zarah sun fito zasu tafi hospital,
da sauri suka fito daga cikin mota,
Dady yace ” mu tafi hospital,
gaba d’ayan su suka d’unguma sukayi hospital,
Cikin hanzari Nurses suka karb’i Ikram aka yi ciki da ita,
ganin gasu a hospital yasa Mannir kallon Zainab yace ” kema sai kiga Doctor ko?
Kai ta girgiza masa had’i da cewa ” a’a,
a d’an hasale Mannir yace ” haba Zainab kefa ba yarinya bace anyi ta fama dake amma kik’i,
kefa ya kamata ki rink’a fad’awa wasu amma ke ayi ta magana d’aya ana fama dake,
a hankali Dady ya juyo yana kallan su kafin yace ” meke faruwa?
Shiru Mannir yayi kafin ya sanar da Dady abin da ke faruwa,
murmushi Dady yayi had’i da cewa ” Zainab kije kiga Doctor kinji please,
murmushi tayiwa Dady had’i da d’aga mishi,
Dady da kanshi ya kaita wajen Dactor ya bada umarnin a duba ta itama,
batare da b’ata lokaci ba aka fara duba ta,
bayan kamar 1hr Doctor ya fito had’i da mik’awa Dady hannu yana murmushi yace ” congratulations Sir both of them are pregnant,
a kid’ime Dady ya saki hannun Doctor daya mik’a mishi lokacin dazai sanar dashi,
cikin tashin hankali Mannir, Naseer, Zainab, Momy suka mik’e,
bakin Mannir na rawa yace ” who is pregnant?
Murmushi Doctor yayi yace ” ZAINAB MANNIR & IKRAM MANNIR suna da shigar ciki na wata uku-uku………..
MOMYN ZARAH
GADAR ZARE!!!
(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)
~NA~
HAUWA A USMAN
JIDDARH
????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
GARGAD’I
MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA
~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO
BEST FRIEND FOREVER & EVERZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~
73
Dab’asss Zainab ta zauna a k’asa had’i da sanya hannunta ta toshe bakinta saboda kukan dayake cinta,,
tama rasa meke yi mata dad’i a duniya,
ji tayi gwamma mutuwar ta da ganin wannan mummunar ranar,
shiko Mannir in banda Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un babu abinda yake maimaitawa,
ya kasa yin komai yau ga matar sa da ‘yarsa d’auke da cikin shege,
Dady, Momy da Naseer, Zarah duk sunyi jugum-jugum a tsaye jikinsu yayi mugun sanyi sun rasa ma mai zasu ce,
a hankali Zarah ta taka wajen Zainab ta d’ora hannunta bisa k’afarta tana massaging, batare data ce komai ba,
a hankali hawayen bak’in ciki ya fara zubowa Zainab cikin k’unar zuciya da takaicin rayuwarta,
cikin mutuwar jiki hannunta na kerrrrma
ta d’ora shi akan cikinta,
wata irin razananniyar k’ara Mannir ya saki had’i da buga kansa da bango yana gwarawa,
cikin bak’in ciki yake ihuuun kuka yana wani abu kamar zararre,
a hankali Naseer ya taka inda Mannir yake ya dafa shi had’i da girgiza masa kai,
wani irin kuka Mannir ya kuma saki wanda yayi masifar bawa Naseer tausayi yaji gaba d’aya tausayin d’anuwansa ya kama shi,
cikin mutuwar jiki Naseer ya d’ago Mannir ya rungume yana bubbuga masa bayansa,
cikin kuka Mannir yace ” Bro mai nayi?
” Wanne irin laifi nayiwa Allah dayake jarrabta ta da irin wannan masifun kala-kala?
” Wanne irin mummunan laifi na aikata a rayuwa da nake had’uwa da iftila’i?
” Bro ka duba ciwon danake fama dashi, wanda bayan ku ‘yan uwana da iyaye,
kowa gudu na yake saboda wari da ruwan gembo, wallahi tunda nake a duniya ban tab’a jin sunan cutar PENIS CANCER (GWAIWA) ba sai a kai na,
me nayi haka da nake fuskantar hukunci mai tsakanin gaske?
Mannir ya k’arasa maganar cikin rikitaccan kuka,
k’ara matseshi Naseer yayi a jikinsa, cikin rawar murya yace,,
” please ka daina magana irin haka kamar ba musulmi ba,
kai fa cikekken musulmi ne, makaranci mai tarin ilimin addini,
ya kamata ka d’auki k’addara, ka kuma yarda da ita,
ba sai mutum yayi wani laifi Allah yake jarabtaa ba, Allah yana iya zartar da abinda yaso akan wanda yaso a kuma lokacin daya so,
idan ka tuna duk Annabawan Allah babu wanda wata mummunar jarabawa bata same shi ba,
haka ma sahabai da sauran ‘yan Adam,
babu wani mahaluk’i da zayyi rayuwa cikin zallar farin ciki da walwala,
batare da ‘an tab’a shi an jarrabi imaninsa ba,
kai ka godewa Allah ma da Allah yasa kai kalar taka k’addarar kenan ,
idan kaji k’addarar wani kalar jarabawar wani kai sai kayi sujjada ka godewa Allah saboda taka ba komai bace,
kuma haka suke ci gaba da rayuwar su suna ci masu godewa mahaliccin su,
kai ma kazama d’aya daga cikin masu godewa Allah a duk hali da yanayin rayuwar da ka tsinci kanka please,
kar ka zama d’aya daga cikin masu yiwa Allah butulci dan ya jarrabe imanin ka,
ni dai abu d’aya na sani shine duk abinda kaga Allah yayi,
to akwai dalilin yinsa dan Allah baya tab’a yin abu babu dalili.



