GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Wani irin mugun tausayinsu ne ya kama Dady da Momy, a hankali Dady yaje inda suke,
ya dafa kafad’ar su had’i da rad’awa Naseer ka kai su gida,
ba musu Naseer ya kama hannun Mannir yana yima Zarah alama data kamo Zainab,
tun da suka shiga mota babu mai yiwa wani magana har suka isa gida,
suna isa harabar tun kafin motar ta gama tsayawa Zainab ta bud’e ta fito da gudu tayi cikin gida,
jikin Mannir a sanyaye shima ya fito yabi bayanta,
Zarah tana k’ok’arin bin bayan su Naseer yayi saurin rik’o ta had’i da cewa “ina zaki?

Cikin muryar kuka tace ” binsu cikin gidan zanyi,
kai ya girgiza mata had’i da cewa “no ki bar su suna b’ukatar privacy,
batare data kuma cewa komai ba ta koma ta zauna tana share hawayen dake zubo mata,
ganin yadda take zubar da hawaye yasa hankalin Naseer yayi masifar tashi,
dan bak’aramin d’aga masa hankali kukan nata yake ba,
yana jin kukan ta har cikin k’ok’on ransa da zuciyarsa,
a hankali Naseer ya jawo ta jikinsa ya rungume, yana shafa kanta,
abinka dama damai jiran kad’an sai ta k’ara faahewa da kukan,
yana san ya rarrashe ta amma bai san ta ina zai soma magana ba,
bai san mai zai ce mata ba, shi kan shi zuciyarsa a karya take,
cikin kuka Zarah tace ” mu kuma irin tamu k’adarar kenan haihuwar shegun yara,
ni na fara haifa yanzu gashi nan Momy da Ikram ma,
yanzu haka zamuyi ta haihuwar ‘ya’yan zina?

Wani irin mugun b’acin rai Naseer yaji, take kalar idansa ta canja ta koma red,
gaba d’aya jikinsa ya d’auki rawa da kerrrna,
cikin matsanancin b’acin rai Naseer yayi ma motar key ya fige ta a guje yayi waje,
yadda yake tsala gudu yasa Zarah d’ago kai ta kalle,
ganin yadda idansa da yanayinsa suka canza yasa ta fahimtar ransa ya b’aci abinka dama damai bak’ar zuciya,
yana d’ago ido karaf suka had’a ido da ita, saurin d’auke idansa yayi daga kanta,
cikin sanyin murya Zarah tace ” please kayi hak’uri idan na b’ata maka rai,
murmushi yayi mata batare daya ce komai ya mayar da kansa wajen tuk’i.

Zainab na shiga gidan direct bedroom d’inta ta wuce ta fad’a kan bed,
had’i da sakin kukan bak’in ciki, jikin Mannir a sanyaye ya shigo d’akin,
tsayawa yayi had’i da rungume hannunsa a k’irjinsa yana hawaye,
cikin muryar kuka Zainab tace ” abinda muka shafe shekara da shekaru muna nema bamu samu ba amma sai gashi lokaci d’aya k’addara ta bamu,
a k’alla munkai 18yrs muna rok’on Allah akan ya bamu haihuwa,,
Allah bai nufa ba, bai bamu ba amma….. sai kuma tayi shiru dan batasan abinda zata ce ba,
tsaye kawai yayi yana kallanta ya rasa abinda zaice.

Sai da Ikram tayi wata guda cur a hospital sannan aka sallame ta lokacin cikin ta yakai wata biyar,
gidan Dady ta koma, yayinda da Zarah keta aikin lallab’ata ta rarrashinta had’i da bata hak’uri,
tana kuma k’ara nuna mata ta yarda da k’addara,
to Alhamdulillah dan Ikram akwai tawakkali da dangana,
ta d’auki k’addararta ta runguma hannu bibbiyu,
tana rayuwarta kamar ba komai,
yadda kasan bata cikin d’umbin b’akin ciki mai tarin yawa da nadamar rayuwa,
yayinda Zainab da Mannir suke cikin k’unci da matsanancin bak’in ciki,
kullum cikin kuka suke,
Mannir ya shigo bedroom d’in Zainab ya iske ta kwance tana aikin kuka,
a hankali ya tsuguma a bakin gadon, dan yanzu baya iya zama saboda ciwon dake jikinsa,
“Zainab ya kira sunanta cikin sanyin murya,
bata d’ago ba amma ta tsaida kukanta,
magana yaci gaba da yi ” yanzu Zainab bazaki hak’ura ki d’auki k’addara ba, bazaki sakawa zuciyar ki salama da dangana ba?

” Ki duba Ikram ‘yarki ta cikin ki yadda ta yarda da tata k’addarar amma ke da girmaki da komai sai abu kike irin na yara,
kamar wara k’aramar yarinya,
cikin kuka Zainab tace ” wannan dalilin ne yasa ni nake kukan,
Ikram yarinya ce k’arama bata san ciwon kanta ba har yanzu,
amma ni tsofai-tsofai dani har da jikoki a ganni da ciki,
cikin ma na shege, haba Mannir taya za’ayi hankalina ya kwanta na samu nutsuwa dan Allah?

“Ni wallahi na gwamci mutuwa ta da wannan bak’ar rayuwar,
cikin kuka ta d’aga hannu sama tace ” ya Allah ya Ubangijin al’arshe, ya Ubangijin sammai da k’assai Allah na rok’e dan darajar fiyayyan halitta ka kawo sadaniyyar rabuwata da cikin nan,
Allah idan abinda nayiwa Zarah ne Allah na tuba, Allah dan darajar fiyayyan halitta ka rabani da cikin nan kar ka bani ikon haihuwar sa ya Ubangiji ta k’arasa maganar cikin kuka,
can k’asan mak’ogwaro Mannir yace ” Amin,
sosai Mannir ya rarrashe ta ya bata hak’uri, sannan ya lallab’a ta shiga wanka shi kuma ya koma parlor,
bayan Zainab ta gama wankan tazo fitowa tana taka step santsin tail ya kwashe ta,
tayi sama sannan ta fad’o akan cikin, wata irin gigitacciyar k’ara ta saki had’i da zubewa k’asa a sume,
da guda Mannir dake parlor ya nufo bedroom d’in, a kid’ime ya sure ta yayi hospital da ita,
da sauri Nurses suka karb’e ta suka yi Emergency da ita,
sai da akayi wajen 2hrs sannan Doctor ya fito,
da sauri Mannir ya tare shi yana tambayarsa abinda ke faruwa,
d’an b’ata fuska Doctor d’in yayi kafin yace ” I’m so sorry cikin dake jikinta ya zube har ma munyi mata wankin ciki,
suman tsaye Mannir yayi saboda tsananin murna da farin ciki,
Doctor dayaga haka tsammanin sa ko shock Mannir yayi saboda bak’in ciki,
a hankali ya dafa kafad’arsa had’i da cewa ” am so sorry, ga d’akin da aka kai ta can yayi maganar yana nuna masa wani d’aki,
da sauri Mannir ya shiga d’akin, ido biyu ya samu Zainab, yana isa gareta ya rungume had’i da fad’in ” Alhamdulillah Allah maji rok’on bawan sane, Allah ya amshi addu’ar mu,
murmushi Zainab tayi ,
sosai sukayi farin ciki da zamubewa cikin,
sai dare Mannir ya sanarwa Dady da Momy, Naseer Zainab na hospital kuma cikin ya zube har ma anyi mata wankin ciki,
kowa yayi murna da zubewar cikin musamman Zarah da Ikram.

Haka dai rayuwa taita tafiya har cikin Ikram ya shiga watan haihuwa,
duk wanda ya ganta yasan ta canja gaba d’aya kamanninta sun sauya ta zama wata iri kalar tausayi,
kullum cikin addu’a take Allah ya raba ta da abinda ke cikinta lafiya dan wani irin yanayi take ji a jikinta,
jikinta yana bata kamar lokacin ta yayi, kamar bazata rayu da abinda zata haifa,
tun da cikin Ikram ya shiga watan haihuwa Zarah ta koma kwana a bedroom d’in ta,
kuma iya k’ok’arin ta wajen kwantar mata da hankali,
yayinda ciwo ya gama cin jikin Mannir sosai har ya kai ga ya kwantar dashi,
gaba d’aya al’aurarsa ta gama rub’ewa,
babu yadda bayyi da Zainab ta koma gidan su momy ko gidan su,
amma fir tak’i tace idan mutuwa ce sai dai tazo ta d’auke su tare,
amma matsawar yana raye bata tab’a barinsa duk irin mawuyacin halin dazai shiga,
tana tare dashi rai da rai mutuwa ce kawai zata raba su,
saboda warin da Mannir yake yi duk ma’aikatan gidan sun gudu,
har sabon mai gadi da su kayi ya kasa zama dan warin yana kaiwa har bakin get,
yanzu idan babu kowa daga shi sai matarsa Zainab.

Cikin dare Ikram ta tashi da matsananciyar nak’uda ganin ta fara zubar da jini yasa tayi muguwar tsorata,
a kid’ime ta tada Zarah daga bacci, itama Zarah tana farkawa taga jini hankalinta yayi mugun tashi,
da gudu ta fita daga bedroom d’in tama mantataga ita sai rigar bacci kanta ko d’an kwalli babu,
tun daga parlor take kwalawa Naseer kira,
duk gidan suka fito a kid’ime da gudu Dady da Naseer su kayi bedroom d’in,
da sauri Dady ya sungumi Ikram yayi habarar gidan wajen motor park,
Zarah na niyyar fita harabar gidan a haka Naseer yayi sauri rik’o ya danna a bedroom yace ” baki da hankaline ji fa a yadda kike amma kina k’ok’arin fita a haka,
sai loakcin ta tuna a yadda take, da sauri ta canja kayan jikinta ta zura doguwar rigar atamfa,
ta sungumi Nailah tayi waje da gudu har tana tuntub’e zata fad’i,
cikin zafin nama Naseer ya rik’e ta had’i cewa ” control mana Mrs Naseer,
Naseer ya ja motar, tun a mota Dady ya kira Mannir da Zainab ya sanar dasu,
suma cikin tashin hankali suka nufo asibitin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button