
Ana shiga da Ikram Emergency Doctor ya fito da hanzarinsa,
dai-dai lokacin Mannir da Zainab suka k’araso,
kallan su Doctor yayi yace ” Babyn a bakin mahaifa yake dole sai dai ayi mata CS a ciro abinda ke cikinta,
yayi maganar yana mik’a musu takadar dasu saka hannu,
kasa karb’ar paper Mannir yayi sai Dady ne ya amsa yayi signing,
da hanzari Doctor ya amsa ya koma ciki,
sai da akayi a k’alla 4hrs akafin Doctor ya fito,
sunan zaune a bakin theater room suna ta zarya masu addu’a nayi,
suna ganin Doctor Naseer yayi saurin mik’ewa ya tare shi,
ya bud’e baki zayyi magana Nurse ta fita da Baby a hannunta tana tsala kuka,
da sauri Zarah ta mik’e ta amshi Babyn,
murmushi Doctor yayi sannan yace ” anyi aikin cikin sa’a ga Baby girl nan an samu,
Baby fara sol mai kama da Ikram sak kamar an tsaga kara,
sai kuka take tana wawure-wawuren nono, tana kai hannu bakin ta,
murmushi Zarah tayi tana kallon Babyn hawaye na zubo mata,
Nurse d’ince tace ” muje na kai ku d’akin da aka kai mamanta,
daga bakin tagar d’akin ta nuna musu ita kuma ta koma,
jiki a sanyaye suka shiga suka iske Ikram tana bacci,
Momy ta mik’a hannu ta amshi Baby, ajiyar zuciya ta sauke had’i da cewa ” ikon Allah,
a hankali ta mik’ewa Dady Babyn addu’a Dady yayi mata sannan ya mik’e ma Zainab,
kamar bazata amsa ba, zai kuma ta karb’a, ido ta k’ura mata tana ganin tsananin kamar yarinyar da Ikram sosai,
da yadda kasan lokacin da Ikram tana jaririya, take taji hawaye ya taru a idanta ,
da sauri ta mik’ewa Mannir dake tsaye,
hannunsa na rawa ya amsa shima yayi mata addu’a.
A hankali Ikram ta bud’e idanta ta fara bin jama’ar dake d’akin da kallo,
hannu ta mik’ewa Zarah da sauri Zarah ta k’arasa bakin gadon, had’i da mik’a mata Babyn,
murmushin k’arfin hali Ikram tayi sannan ta amshi Babyn,
ta k’ura mata ido na wani lokaci kafin tace ” Allah ya isan mu tsakanin mu da mahaifinki daya samar dake ta wannan hanyar,
Allah yayi mana sakayya ni dake daya kasance d’an fashi,
Allah ya shiryar dake a bisa turba ta gaskiya, Allah ya baki ikon gane gaskiya,
gaskiya ce ya kuma baki ikon binta,
Allah ya baki ikon gane k’arya,
k’arya ce ya kuma baki ikon kauce mata,
Allah yasa kina cikin salihan bayi wad’anda Annabi zayyi alfahari dasu ranar alk’iya,
Allah yayi miki albarka ya sanya haske a rayuwarki ya tsareki daga dukkan abin k’i,
a hankali ta mik’ewa Zarah Babyn had’i da cewa gata ki kula min da ita,
bazan ce na baki ita amana ba, dan nasan zaki kula da ita kamar yadda zaki kula da rayuwar yaranki,
dan girman Allah kar wanda ya sanar da ita asalinta da kuma hanyar da aka same ta,
ku dai sanar da ita Mamanta ta rasu kodan ta rink’a yi min addu’a,
a hankali ta juya wajen Naseer tayi mishi murmushi tace ” Uncle nasan zaku kular min da ita sosai, kuma nagode Allah yasaka muku da alkhairi, yabar zumunci,
ta juya wajen Zainab da Mannir tana murmushi tace ” Momy, Dady please ku yafe min idan nayi muku wani laifi koda akan rashin sani ne,
ina matuk’ar san ku, ina san ganin ku cikin farin ciki, ta kalli Momy da Dadyn Naseer tace ” grandfa please kuma ku yafe min,
kuma dukkan ku kular da Baby na dan Allah,
ta k’arasa maganar tana hawaye.
Kowa ka gani a d’akin jikinsa yayi mugun yin sanyi,
Zainab, Mannir, Zarah sai kuka suke,
a hankali Zarah da Zainab suka fad’a jikin Ikram, Zainab tace ” ya kika magana irin haka kamar wacce zata bar duniya please ki dai na bada wasiyya keda kanki zaki raini ‘yar ki,
murmushin k’arfin hali Ikram ta kuma yi,
tace ” na sani Momy mutuwa zanyi,
a hankali Mannir ya tako gabanta yasa hannu yana shafa kanta hawaye na zuba daga idansa yace ” bazaki mutu ba Ikram,
kanta ta d’aga a hankali ta kalle shi tayi mishi murmushi tace ” please ni dai Dady kona mutu kar kuyi min kuka,
kar ku d’aga hankalin ku dan Allah.
Ta bud’e baki zata kuma magana, ta fara tari sai jini kafin kace me idanuwanta sun kakkafe,
da gudu Mannir da Zainab suka fita kiran Doctor,
Dady da Momy, Naseer da Zarah suka rirrik’e ta suna kiran sunanta,
a hankali Ikram tayi kalmar shahada,
kafin jikinta ya saki, ido Naseer ya runtse da k’arfi had’i da ja baya a kid’ime,
Dady yasa hannu ya rufe mata idanuwanta dake kallan sama tana murmushi,
a gigice Zarah tace ” Dady meke faruwa?
Cikin rawar baki yace ” ta rasu,
wata irin k’ara Zarah tayi had’i da sulalewa k’asa sumammiya,
dai-dai lokacin Mannir da Zainab suka dawo daga kiran Doctor,
da sauri Doctor ya k’arasa yayi ‘yan dube-dubensa,
ganin ta mutu yasa shi ja mata bed shirt ya rufe ta, cikin mutuwar jiki,
wani mahaukacin kuka Zainab ta saka tana jijjiga Ikram had’i da kiran sunanta,
taimakon gaggawa aka bawa Zarah,
sannan ta farfad’o cikin matsanancin kuka,
Mannir yayi kuka sosai kamar ransa zai fita,
yana ji yana gani aka shirya Ikram aka kaita makwancinta,
yayinda Zarah ke rungume da Babyn tana faman kukan,
bayan andawo daga kai Ikram Naseer yayiwa Babyn hudubaa da sunan Mamanta Hafsat ana kiranta IKRAM d’in,
sosai Mannir ya shiga dawo hankali shi yayi mugun nadama,
ranar sadakar bayan an gama zaman makoki,
yace yana san magana da Abban Zarah, Naseer, Zainab, Alhaji Abdullahi, Momyn sa da Dadynsa.
A babban parlor’n gidan dake sama aka hallara, yayinda Mannir keta aikin kukan cike da matsananciyar nadama,
bayan duk kowa ya zauna akayi shiru ana jiran Mannir, ganin bashi da niyyar magana ne yasa Dady cewa ” Mannir kayi magana ka tara mutane kuma kayi shiru kak’i cewa komai,
a hankali Mannir ya mik’e yaje gaban Zarah ya zube, ya durk’usa ya kasa cewa komai sai kukan dayake kamar ransa zai fita,
Momy tace ” Mannir kayi magana mana,
kasa magana yayi illa kallan Zarah da yaci gaba dayi yana kuka,
tsawa Dady ya daka masa cikin b’acin rai yace ” karka mai da mutane sakarkaru mana,
idan bazakayi magana ba mu tashi,
still shiru Mannir yayi yana ci gaba da kallan Zarah yana kuka,
tsaki Dady yayi ya mik’e a fusace yana k’ok’arin barin wajen,
da sauri Mannir yace ” kayi hak’uri Dady zanyi magana,
komawa Dady yayi ya zauna cike da tausayin Mannir,
k’ara fashewa Mannir yayi da kuka mai tsanani,
yana kallan Zarah, cikin kuka yace “………….
MOMYN ZARAHGADAR ZARE!!!
(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)
~NA~
HAUWA A USMAN
JIDDARH
????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
GARGAD’I
MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA
~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO
BEST FRIEND FOREVER & EVERZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~
74
Cikin matsanancin kuka yace ” please…. sai kuma yayi shiru, ya kasa cewa komai,
sosai Dady ya hasala, cikin b’acin rai Dady ya daka mishi tsawa had’iwa cewa ” Mannir karka kuma bari na kuma yin magana,
bai kalli inda Dady yake ba, ya kalli Zarah cikin ido na kamar seconds 15 sannan ya duk’ar da kansa k’asa,
ita dai Zarah shiru tayi tana kallansa batare data ce komai ba, duk ilahirin jikinta rawa yake kamar mazari,
k’asa da kai Mannir ya k’ara,sannan cikin rawar muryar yace ” nasan duk wad’an nan abubuwan da suke samu na a rayuwa yana da nasaba da abinda nayi miki ne,
na tabbatar iftila’in da suke fad’a min, ni da iyali nasaboda ke ne Zarah,
dan nasan babu wani abu da nayi marar kyau a rayuwata da Allah zai azabtar dani,
azabtarwa mai tsanani face abinda nayi miki, kuma wallahi nasan kad’an na gani, ban ga komai ba, matuk’ar ban rok’ek’i yafiya ba,
wannan ya tabbatar min da yanzu tun a duniya ake yin hisabi ba sai anje ko’ina ba (lahira),
idan kayi abin alkhairi tun a duniya zaka gani, haka ma idan kayi sharran,
saboda abinda ni kad’ai nayi miki, iyalai na sai had’uwa suke da iftila,
a gaban ido na akayiwa matata da ‘yata fyad’e, kuma duk suka d’auki ciki,
Ikram ta haifi shege kamar yadda kema kika haifa,saboda kema ‘yar wani ce, kuma matar wani ce, k’anwar wani ce,
yayar wani ce, sannan mahaifiyar wani ce,
sannan daga k’arshe ta mutu kamar yadda na buk’ata akan ki,
tabbas zancen Allah baya tashi dayace ” duk wanda yayi ZINA da ‘yar wani, sai shima anyi da ‘yarsa
idan kuma bashi da ‘ya ayi da matarsa,
idan bashi da mata ayi da mahaifiyarsa,
idan bashi da mahaifiya sai anyi da k’anwarsa,
saboda itama wacce yayi da ita matar wani ce, ‘yar wani ce, mahaifiyar wani ce, sannan k’anwar wani ce.