
Ranar da aka d’aura auren Naseer da Zarah, wallahi ji nayi dama ai tashi duniya ranar kowa ya huta,
haka naje d’ayan gidan da nake zama nayi ta hauka ina fashe-fashen glasses,
sannan duk da Zarah tayi aure ban kyale taba ban hak’ura da ita ba,
sai da nabita gidan Dady, ranar naci sa’a Naseer baya d’akin na shiga,
na kashe duk room light, na fara hot romance da ita wanda ita a tunaninta kai ne Naseer,
ta saki jiki sosai da ni dan ta d’auka mijinta ne, tunda a cikin duhu ne, hakan yasa bata gane ni ba ne,,
Ina gaf da shigarta hannunta ya fad’a kan bed side lamp aiko haske ya gauraye d’akin,
nayi saurin kawar da fuskarta ban bari ta ganni ba, na bar d’akin.
Da Zarah ta tashi haihuwa sai Allah ya bata abinda nafi k’aunar samu a duniya sama da komai,
wato d’a Namiji dan Allah ya sani ina matuk’ar san na haifi d’a namiji,
amma Allah bai bani ba, tun daga ranar dana d’ora ido na akan abinda Zarah ta haifa sai Allah ya d’ora min matsanancin so da k’aunar sa,
naji akansa babu abinda bazan iyayi ba, sosai na rink’a jinsa a raina da duk wata gaba dake jiki na,
naji babu abinda nake so a duniya kamar kasancewa tare da yaro na,
har gidan su Dady kawai nake zuwa dan na ganshi,
dan haka na fara tunanin……… ya d’anyi jimmmm had’i da sauke nannauyan ajiyar zuciya.
Sannan yaci gaba ” na fara tunanin kashe Naseer ko Zarah,
amma har Zarah ta mutu sannan Naseer ya bar k’asar ban samu na cimma buri na,
lokacin da suka dawo naga yadda Na’eem ya koma sai naji sanshi ya k’aru a raina,
ina shirin d’aukar mataki
Allah ya fara jarabta ta,
ya k’arasa maganar cikin rikitaccen kuka kamar ransa zai fita.
Wannan bak’in ‘kudirin nawa, da mummunar manufa ta akan Zarah yasa ni cewa a raba musu bedroom ita da Ikram,
bayan tun da suka taso tare komai nasu d’aya ne,,
cikin rikitaccen kuka ya k’ara zubewa a gaban Zarah yace ” ki dubi girman Allah, da dajarar Annabi ki yafe min,
nasan ban cancanci yafiya daga gare ki ba amma ki dubi…..
bai k’asara ba yaji tauuuuu an kifa mishi mari, yana juyawa yaga Zainab tana huci kamar macijiya,
ya bud’e baki zayyi magana ta k’ara kifa masa wani marin,
sannan taci kwalar rigarsa da duka hanuwanta biyu
ta zaro idanta waje da suka gama yin ja tace,,
tsinannan Allah, munafuki fasik’i, macuci, ka cuce ni ka cuci kanka da rayuwarka,
kayi asarar duniya da lahira,
ashe kai ne bak’in mugun dakayiwa Zarah ciki,
amma dan tsabar rashin imani da tsoran Allah ka zage iya k’arfin ka kayi mata dukan mutuwa har da karaya biyu kayi mata,
dayake kai cikekken tsinanne ne,
wallahi da Allah da mala’iku suna gajiya da tsinewa mutum kai ne mutum na farko dazasu fara gajiya da la’antarsa,
Mannir kasa na tsani kaina da rayuwa ta, kasa ina jin kunyar kai na,
yauce rana ta farko da uwa tayi murna da farin cikin mutuwar ‘yarta ta cikinta,
Allah ya taimaki Ikram da bata rayu taji kuma taga wannan mummunan abin kunyar ba.
” Allah ya rufa mata asiri, dan sai ta gwamci mutuwarta da ganin wannan mummunar ranar a rayuwarta,
ranar da zata ga ubanta mahaifi yayiwa k’anwarta da suka sha nono da ita ciki,
mahaifiyarta da mahaifiyar ta suka sha nono d’aya,
yarinyar datake tamkar ‘ya a wajenka, wallahi tunda kayiwa Zarah haka zaka iya kusantar ‘yarka ta cikinka,
wama ya sani ko itama ka keta mata haddin tunda kai d’an akuya ne,
ta k’arasa maganar cikin rikitaccen kuka, hannuwanta tasa ta fara dukan k’irjinsa da iya k’arfinta,
Mannir bai hana ta ba, illa kallanta daya tsaya yana yi hawaye na zubo masa,
sosai take dukansa tana hankad’a shi, tana cewa ” ban tab’a dana sanin rayuwa ta da zuwa na duniya ba sai yau,
yau nayi nadamar gaba d’aya rayuwa ta, nayi dana sanin saninka a rayuwa ta,
balle har yakai dana had’a jini dakai, na kuma godewa Allah da yasa babbar alak’ar dake tsakanin mu ta yanke ta hanyar mutuwar Ikram,
baice mata komai ba,
a hankali cikin mutuwar jiki ya rik’e hannuwansa da take dukan k’irjinsa,
da sauri ta kwace hannunta daga nasa ta nuna sa da yatsa tace ” daga yau anan take a wannan rana a dai-dai wannan lokacin duk wata alak’a dake tsakani na da kai ta yanke har abada,
daga nan har k’arshen rayuwa ta bana fatan ko burin sake ganinka a rayuwa,
a hankali ya sake ta ya kuma komawa gaban Zarah ya zube ya k’ara fashewa da matsanancin kuka yace ” please Zarah ki yaf……..
Ganin yadda duk jikinta yake kerrrrma da tsananin rawa yasa shi kasa k’arasawa abinda yayi niyyar fad’a,
a matuk’ar tsorace take kallan sa dan ganin shi take tamkar wani moster,
a razane cike da tsoro take kallansa,
jikinta sai rawa yake yana kerrrma gami da tsuma, kamar wacce taga mutuwarta,
cikin sanyin jiki Mannir ya matso kusa da Zarah had’i da mik’a hannu zai tab’a ta,,
a tsorace tayi saurin ja da baya, hannu ya mik’a zai kai jikinta, tana ganin haka saki rikitacciyar k’ara,
Naseer da tunda Mannir ya fara magana kwakwalsa tayi hook ya kasa cewa komai,
koda motsi ma kasawa yayi mamaki, tsoro da fargaba sun gama cika shi,
gaba d’aya baya cikin hayyacisa da nutsuwarsa,
jin k’arar Zarah ne yasa shi dawowa cikin hayyacinsa,
da sauri ya mik’e yaje inda Zarah ke zaune duk ta k’udundune jikinta saboda tsoro,
Naseer ya tsungunna a gabanta had’i da rungume ta jikinsa,
da sauri ta fad’a jikinsa had’i da k’ank’ame shi sosai, jikinta sai kerrrrma yake yana b’ari,
ga wani uban gumi dake zubo mata, gaba d’aya ta zare, kallo d’aya zakayi mata kasan bata cikin hankalinta.
A hankali Mannir ya kuma mik’a hannu zai tab’a ta, aiko Nasser ya zabura…………
MOMYN ZARAHGADAR ZARE!!!
(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)
~NA~
HAUWA A USMAN
JIDDARH
????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
GARGAD’I
MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA
~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO
BEST FRIEND FOREVER & EVERZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~
75
Cikin mutuwar jiki Naseer ya d’aga masa hannu had’i da matsar da ita gefe,
ba tare da yace masa komai ba,
ita ko duk ta rirrik’e Naseer kamar wacce za’a kashe,
Zainab dake durk’ushe a k’asa tana kuka ta mik’e cikin zafin nama taje gabansa,,
tace ” da kake mik’a hannu me zaka kuma yi mata?
Ko….. shiru tayi saboda yadda take jin yanayin jikinta ya canja,
k’irjinta na sama da k’asa da kyar tace ” tsakani na da kai Mannir Allah ya isa, Ubangiji yayi mana sakayya ni da Zarah, da Ikram,
a hankali numfashinta datake iyakar k’ok’arin fisgowa ya d’auke gaba d’aya ta zube k’asa a sume,
mik’ewa Naseer yayi da Zarah tsaye a jikinsa, ya fita ba tare daya furta koda kalma d’aya ba,
da sauri Mannir ya bi su suna gaf da barin parlorn ya durk’ushe had’i da rik’o k’afafuwan su,
cikin matsanancin kuka yace ” please ku yafe min, idan baku yafe min ba wallahi na shiga uku, yanzu ma kuna ganin yadda Allah yayi dani da rayuwa ta,
a hankaki Nasser ya durk’usa yasa hannunsa ya zame rik’on da Mannir yayiwa k’afuwansu,
Dady da Momy kasa motsi su kayi saboda kunya da tashin hankali,
Alhaji Abdullahi da Abban Zarah sauran mutane suka mik’e jiki a sanyaye,
a hankali Abban Zarah ya sunkuya ya sungumi Zainab dake kwance a sume yayi waje da ita ba tare da kowa yayiwa kowa magana ba,
suka fita ko a mota babu wanda yayi magana har suka k’arasa hospital da Zainab.