GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Da sauri aka karb’e ta aka shigar da ita emergency an d’auki lokaci mai tsayi kafin Doctor ya fito ya sanar da su,
ta samu mutuwar b’arin jiki saboda tsananin tashin hankalin data shiga,
sosai hankalin su yayi masifar tashi, Abban Zarah yayi kuka a b’oye har ya godewa Allah,
bak’in cikinsa biyu na farko halin da Zainab ke ciki,
na biyu abinda mannir yayiwa Zarah,
lalle Mannir ya cika cikkekken maci amana butulu, mugu macuci azzalumi,
amma ba komai shida Allah, tunda gashi nan tun yanzu ya fara girbar abinda ya shuka,
bedroom Nasser yakai Zarah, ya ajiye ta akan bed sannan ya d’auko mata ruwa a fridge ya bata tasha jikinta sai rawa yake yana tsuma, a hankali Naseer ya zauna a kusa da ita ya jawo ta jikinsa ya rungume ba tare dayace komai ba,
sai ajiyar zuciya da yake ta faman saukewa, ya k’i yin magana ne tun a parlor saboda yasan halinsa da bak’ar zuciya,
muddin yace zayyi magana to komai ma b’aci zaiyi, dan ba’a k’are lafiya ba,
dan haka ya zab’i yayi shirun dan shi ya fiye masa sauk’i.

A gigice Zarah ta d’ago kai ta kalli Naseer tace ” dama na fad’a maka Na’eem ba d’anka bane,
ko sau d’aya ban tab’a alak’anta ka dashi ba, kwata-kwata zuciya ta tak’i yarda shi d’anka ne,
dan nasan bazaka tab’a yi min haka ba, ina da cikekken yak’ini akan ka Uncle,
na yarda dakai d’ari bisa d’ari, nasan bazaka tab’a cutar da ni da rayuwa ta ba,
dan Allah Uncle ka d’auke mu bar nan, muma tafi ko’ina ne, Uncle bazan iya ci gaba da zama anan ba,
na tsani garin nan, na tsani kowa da yake ciki, ni kai na ma na tsani kai na,
ganin yadda take magana a burkice duk ta fita daga hayyacinta yasa Naseer mai da ita k’irjinsa ya rungume,
had’i da runtse idansa da k’arfen tsiya, yana shafa kanta,
yana tunanin yadda rayuwa da duniya ta canja,
da yadda mutanen cikin duniya suka zama marasa amana, da alk’awari,
ashe duk yadda kake da mutum yana iya cin amanar ka,
duk kusancinka da d’an Adam da alak’ar dake tsakanin ku yana iya cutar dakai,
to kau idai haka ne duniya da mutum ba abin yarda bane,
Dady da Momy sun kai magrib anan babu wanda iya furta koda kalma d’aya a cikin su,
kowanne yayi jugum yana sak’a abubuwa da dama a ransa,
kiran sallar magrib da akayi ne yasa dukkan su mik’ewa jiki a matuk’ar sanyaye suka bar parlor’n.

Bayan kwana biyu Naseer ya gama duk wani shirin komawar su holland,
dan shi kansa ya tsani Nigeria da abinda ke cikinta jinsa yake kamar acikin wuta,
haka tunda abin ya faru Dady da Momy suke wasan b’oya da Zarah da Naseer dan muguwar kunyar su suke ji,
musamman ma ita Zarah, dan sunfi jin kunyarta akan kowa,
itama tunda abin ya faru bata fito ko parlor ba, kullum tana bedroom tana faman kuka,
ji take dama itace ta mutu ta huta ba Ikram ba, sai yanzu tayiwa Allah godiya da mutuwar Ikram,
dan tasan mutuwarta ta fiye mata data rayu taga tarin abin kunyar da mahaifinta yayi,
babban burinta a duniya bai wuce su bar k’asar ba, kwata-kwata ko yaran ma ta daina shiga harkar su,
ta daina kula su, dan ji take ta tsani kowa da komai, ji take gwamma mutuwa tazo ta d’auke ta,
haka yaran zasu zo su hau kanta su k’araci surutun su amma a banza ko kallan inda suke bata yi,
a parlor Nasser ya iske Dady da Momy zaune kallo d’aya yayi musu ya kauda kansa gefe da bazai iya jurar kallan mahaifansa a cikin matsananciyar damuwa ba,
duk sun rame sosai kamar ba su, duk wannan walwalar dake fuskar su yanzu kwata-kwata babu ita,
sai tulin bak’in ciki da damuwa.

Suma kallansa su kayi cike da tausayawa dan shima yayi muguwar rama acikin kwana biyu kawai,
ya rame ya kod’e sosai, Momy na shirin tashi Naseer yayi saurin cewa ” no please Momy ki tsaya bana san ki tafi magana zanyi daku gaba d’aya,
cikin sanyin jiki ta koma ta zauna, sai da Naseer ya d’an numfasa kafin yace,,
” please kuyi min izini ina san barin k’asar nan ni da iyalai na,
zamu d’anyi nesa da nan kafin komai ya lafa, hankula su kwanta,
in yaso sai mu dawo daga baya,
daga Momy har Dady babu wanda yaso haka a ransa amma dan sama musu sauk’i duk suka amince batare da nuna masa alamar komai ba,
zai mik’e Dady yace ” kuje kai da Zarah ku dubo Zainab a hospital kafin ku wuce,
cikin sanyin murya Naseer yace ” bata da lafiya ne Dady?

Dan shi bai ma san ta fad’i ba a lokacin,
bayani Dady yayi mishi na rashin lafiyar Zainab, aiko sosai hankalin Naseer yayi mugun tashi dan yasan hakan yana da nasaba da tsananin so da k’aunar da Zainab keyiwa Zarah,
haka ma yasan idan Zarah taji abinda yake damun Zainab d’in hankalinta zai k’ara tashi,
amma dai koma meye dole ne suje su dubo ta kafin su wuce, dan ba’a san me Allah zayyi gaba ba,
jiki a sanyaye Naseer ya fita ya shaidawa Zarah ta shirya ita da yaran zasuje hospital,
ba musu ta amsa da to, bata wani b’ata lokaci ba ta fito ita da yaran,
a parlor ta iske Naseer zaune rik’e da Nailah, kallanta Naseer yayi yaga duk ta zama wani iri,
dan ya sani bata cin komai, ko ruwan tea dak’er take sha, shima sai ya matsa mata,
haka ma bata bacci yadda taga rana haka take ganin dare,
bata runtsuwa, tayi bak’i ta rame sosai kamar ba ita ba,
batare dayace mata komai ba ya mik’e yayi waje,
bin bayansa su kayi ita da yaran,
har suka isa asibitin babu wanda yacewa kowa komai a tsakanin su,
sai yaran dake ta faman damun su da surutu,
a harabar asibitin yayi parking ya fito d’auke da Nailah da Noor,
ita dai Zarah bin bayansa kawai take dan bata san wanda bai da lafiya ba,
bata tambaye shi bane dan bata san yawan magana yanzu.

Suna shiga d’akin taga Zainab kwance bata motsi sai na’ura dake aiki,
ko numfashi bata iyawa sai da oxygen,
da k’arfi ta saki k’ara had’i da fashewa da rikitaccen kuka ta fad’a kanta tana jijjiga ta,
cikin kuka ta kalli Naseer tace ” Uncle ka taimake ni ka d’auke ni dani da Momy na mubar k’asar nan,
dan Allah mu tafi mubar kowa, ku biyu kad’ai kuka rage min a duniya da nake su,
idan wani abu ya samu d’aya daga cikin ku bazan iya jurewa ba, dan Allah ka taimaka min kar Momy ta mutu,
itama ni kad’ai na rage mata a duniya wacce zata kira tata dan Allah please,
ta k’arasa maganar cikin matsanancin kuka,
kanta Naseer ya shafa had’i da rungumo ta jikinsa,
yama rasa abinda zayyi sai kawai shima ya saki kukan,
dan dama ya dad’e yana rok’on Allah yasa yayi kukan ko zai samu sassauci a zuciyarsa,
Alhaji Abdullahi da Abban Zarah dake gafe, tsaye sukayi suna kallan su cikin tausayawa,
dan su Naseer basu san da su ba,
sosai da k’arfi Naseer ya rungume Zarah yana rusgar kuka kamar ransa zai fita,
sun ma manta da yaran su dake tsaye,
itama Zarah kukan take sosai tana sambatun da bata san me take cewa ba,,
yaran tsaye sukayi sororo suna kallan Dad & Mom d’in su dake kuka,
a hankaki Na’eem yaje kusa dasu yana share musu hawaye, shima yana kukan,
sai Noor da Nauwaf ma suka nufe su,
gaba d’aya suka saka hannu suna share musu hawaye,
cikin kuka Na’eem yace ” Dad nine na saka ka kuka?

Yayi maganar yana nuna kansa,
cak Naseer da Zarah suka tsaida kukan su had’i da zuba masa ido,
a hankali Naseer ya shiga girgiza masa kai alamar a’a,
Alhaji Abdullahi da Abban Zarah dake tsaye sukayi gyaran murya dan sun lura daba susan suna wajen ba,
da sauri suka d’ago kai ganin Abban Zarah da Alhaji Abdullahi dake tsaye yasa su saurin sakin juna, cike da jin kunya,
sosai suka yiwa su Zarah nasiha mai ratsa jiki da zuciya, wanda a take duk suka ji zuciyoyin su sunyi musu sanyi,
Abban Zarah ya rink’a kawo musu misalai akan Annabawan Allah, da salihan bayi na gari,
ya rink’a jawo musu ayoyin Al-Qur’an,
daga k’arshe kuma ya basu hak’uri on belf of Mannir,
shiru duk sukayi babu wanda yace komai,
sai Naseer daya nemi izinin tafiya da Zainab Holland, batare da gardamar komai ba suka amince.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button