GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Washe gari jirgin su ya d’aga zuwa Holland gaba d’ayan su da yaran su, da Zainab,
cikin ikon Allah satin Zainab d’aya a hospital ta farfad’o, sai da har lokacin b’arin jikinta a shanye yake,
dan ko magana bata iyawa, ko zama da gane mutane bata yi,
haka Zarah ta rink’a jinyar ta a hospital, itace wankan ta, itace aikin kashi da fitsarinta,
had’i da sauran aikace-aikace har sukayi wata uku a hospital kafin akan sallamo su daga hospital suka dawo gida,
dan yanzu ba laifi tana iya gane mutane musamman Zarah da Naseer,
kuma tana iya zama a wheelchair, kwata-kwata bata barin ‘yan aiki su kula da Zainab ita da kanta ke kula da ita,,
haka rayuwa taita tafiya Zarah na kula da Zainab har Allah yasa ta samu sauk’i garau kamar bata tab’a yin ciwo da jinya ba,
ta warke sosai tayi garau, sai lokacin Zainab ta yarda da maganar hausawa da suke cewa

” D’A DA DUKIYA BA’A YI MUSU BAK’IN CIKI KO MUGUNTA DAN BA’A SAN MAI MORAR SU BA

KUMA BA LALLE D’AN DAKA HAIFA DA CIKIN KA NE ZAI TAIMAKE KA KOYA KULA DA KAI BA,
HAKA KOWANNE D’A, D’A NE

Mannir kam ba’a magana dan dashi da tsumma duk d’aya,
ya yargwale, ya k’ek’ashe, ya bushe yadda kasan ba mutum ba ya koma kamar skeleton,
duk wani hospital daka sani a duniya sun k’i karb’arsa saboda warin da yake yi,
ya gama rub’ewa ya lalace ga al’aurarsa data fara tsutsotsi,
saboda yawan complain d’in da jama’a keyi a kansa na ya dame su da wari yasa human right ta shigo cikin maganar babu yadda zayyi dole yana ji yana gani aka mayar dashi daji aka yi masa gida,
shi kad’ai yake rayuwar sa dan babu wani d’an Adam d’in dazai iya yi masa aiki ko nawa za’a bashi saboda d’oyi,
tun abinda yayiwa Zarah Momy da Dady suka cire hannunsu daga kansa,
suka zuba masa ido, babu wanda ya k’ara kula shi acikin su,
balle su shiga harkarsa,
suka cire duk wani tausayi dake tsakanin d’a da mahaifi suka bar shi da halinsa,
dan sun san abinda yayi ne yake binsa,
koda Alhaji Abdullahi da Abban Zarah suka zowa Dady da maganar Mannir fututtukewa yayi yace babu ruwansa,
kuma duk wanda yasa masa hannu bai yafe ba, dole tasa suma suka kyale shi,
sun san Allah ne da kansa yake hukunta shi abisa cin amanar marainiya dayayi,
sosai Naseer, Zarah, Zainab, Momy da Dady suka koma normal kamar babu wani abu daya tab’a faruwa a rayuwar su,
Zainab ce ta matsa musu akan lalle ya kamata su je Nigeria suga iyayen su,
akan dole Naseer ya nema musu visa,
suka yo Nigeria, sai da suka zo Dady yake sanar musu halin da Mannir yake ciki,
aiko Zarah taita rusgar kuka saboda tausayin sa,
Zainab da Naseer kuwa ko a ajikin su,
yadda kasan ma basu san wanda ake magana akan shi ba,
kwata-kwata babu tausayinsa a zuciyar su,
dole Zarah ta matsawa Zainab da Naseer akan dole sai sunje sun dubo shi,
dakyar ta shawo kansu, suka tafi har su Dady.

Tun daga nesa kafin su k’arasa inda Mannir yake suka fara jiyo d’oyinsa,
kuka Zarah ta k’ara fashewa dashi,
koda suka isa dakyar suka rink’a yin numfashi saboda d’oyin da yake yi,
komai rashin imanin mutum yaga yadda Mannir ya koma dole ne ya tausaya masa,
tsakanin d’a da mahaifi sai Allah take zuciyar Dady da Momy ta karye suka shiga zubar da hawaye,
shi kansa Naseer take yaji mugun tausayin d’an uwansa ya kama shi,
bai san sanda ya fara zubar da hawaye ba shima,
Zarah dama uwar kuka balle an samu mai dalili baki ta bud’e tayi ta rusgar kuka kamar ranta zai fita,
da farko Mannir bai gane su ba, sai da yayi musu k’uri da ido sannan ya gane su,
dakyar Mannir ya bud’e baki yace ” kunga yadda Allah ya maida ni ko?

” Dan girman Allah ku yafe min idan baku yafe min ba, Allah kad’ai yasan me zan gani gaba,
yayi maganar cikin matsanancin rashin lafiya, da sauri Zarah ta zube a gabansa cikin kuka tace ” na yafe maka Dady duniya da lahira, wallahi na yafe maka, kuma ina fatan Allah ma ya yafe maka,
indai hak’k’i nane ke wahalar dakai haka, na yafe maka, Allah ya rangwanta maka,
dakyar yayi murmushin k’arfin hali yace ” nagode Zarah, Allah ya saka miki da alkhairi,
ya juya ya kalli Daddy da Momy, suma cikin kuka suka ce sun yafe masa duniya da lahira,
haka ma Naseer ya yafe masa,
ya juya wajen Zainab dake tsaye ko gezau, kwata-kwata babu alamar tausayi ko jin k’ansa a tattare da ita,
kanta da kawar gefe dakayar da bud’e baki murya can k’asa tace ” na yafe maka, Allah ya yafe mana baki d’aya,
ido ya lumshe yana hawaye, da sauri Zarah tace ” dan Allah Daddy da Naseer ku taimaki Daddy na dan Allah karku bari yayi mutuwar wulank’anta,
ganin yadda take rusgar kuka tana neman a taimakawa wanda ya cutar da ita da rayuwarta yasa gaba d’ayan su suka k’ura mata ido,
musamman Naseer ya kafe ta da ido, a hankali ya furta Fatimatul Zarah kenan mai sanyin hali,
da tattsausar zuciya, kwata-kwata baki da rik’o mummunan nufi akan mutum koda wanda ya azabtar dake ne,
kina da tsarkakekkiyar zuciya mai taushi, kina da hak’uri da saurin yafiya, kina da saurin manta sharri kina da rik’o da alkhairi,
kina da manyan halaye masu kyau, kina da halaye na gari irin wad’anda Annabi (S.A.W) yake so, yake kuma alfahari dasu,
halayen dake wuyar samu a zamanin nan, dan sai ka shekara dubu kana yiwa mutum alkhairi,
amma rana d’aya idan ka kuskure shikenan ka shiga uku sai ya mance da alkhairai daka yi masa.

A hankaki Daddy ya dafa shi yace ” kwarai kuwa Naseer samun mutum mai irin halayen Zarah sai an tona,
sai lokacin Naseer yasan a fili yayi maganar ba kamar yadda yake zaton yayi a zuciyarsa ba,
murmushi yayi had’i da duk’ar da kansa k’asa, a hankali ya saci kallan inda Zarah take,
ganin itama shi take kallan yasa shi fahimtar itama taji abinda yace,
a hankali Zarah tace ” please Daddy a taimaki Daddy, dan Allah, wallahi mu bar ganin yayi laifi,
idan muka barshi a wulank’ance muma sai Allah ya kamamu da laifin watsi da zumuncin Allah,
dan Allah Naseer, kar muyi abinda zamu dawo daga baya muna nadama,
tsaki Zainab tayi had’i da fita daga wajen ta koma mota ta zauna,
tana jin yadda zuciyarta ke tsananin yi mata zafi da rad’ad’i gami da k’una,
ba musu Naseer ya sunkusa ya d’auki Mannir,
da farko k’in yarda Mannir yayi, dan shi a ganinsa bai cancanci taimako daga wajen kowa ba,
sai da kyar Zarah ta shawo kansa ya yarda,
Daddy da Momy da Zainab da yaran suka shiga mota d’aya,
Naseer da Zarah da Mannir suka shiga mota d’aya,
BQ Naseer ya fara wucewa da Mannir yayi masa wanka sosai,
ya canja masa kaya ya fesa masa turare, sannan ya kamo hannunsa suka shiga cikin gidan,
Zarah ce ta sanar dasu akan taji labarin wani mai maganin gargajiya na Islamic kuma ance maganinsa yana yi sosai.

Washe gari suka d’unguma gaba d’aya suka tafi amma banda Zainab dan rufe idanuwanta tayi tace bata zuwa,
kuma ta hana a tafi da yaran har Nailah da an yaye ta tuni, Ikram ma an yaye ta tun suna Holland,
koda sukaje sukayiwa mutumin bayani, cewa yayi ba komai zasu gwada suga mai Allah zayyi amma subar Mannir anan har tsawon wata biyu,
kuma duk sati kawai zasu rink’a zuwa ganin shi ranar Friday,
haka suka bar shi anan bayan sun gama biyan duk abinda ya dace,
bayan sun dawo gida Zarah ta cewa Daddy bafa zama za’ayi ba,
dole a dage da addu’a ana rok’on Allah, kuma a saka da saukar Al-Qur’an a masallatai,
ana bada sadaka ko Allah zaiji k’ansu ya amsa rok’on su,
kamar yadda Zarah tace haka akayi Daddy ya zuba malamai akayi ta rok’on Allah ana saukar Al-Qur’ani,
suma kuma suka dage da addu’a.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button