
Allah maji rok’on bayinda dan da su Naseer suka koma bayan wata biyun da mai magani ya basu,
Mannir ya warke sumul yayi garau dashi,
yayi fresh yadda kasan bai tab’a yin wani ciwo ba,
sai ma yafi da yarinta da kyau,
farinsa ya k’ara fitowa sosai, gashin kansa yayi lufluf,
k’arfi da girman zindariya ya k’aru,
dama ba’azo da Zainab ba dan k’in zuwa tayi,
dad’i Daddy da Momy su kaji sosai ganin yadda Mannir ya koma so fresh, & handsome guy kamar d’an 30yrs,
Zainab ma da hankalinta ya kwanta sosai, kuma dama ga kud’i da hutu sai ta koma yarinya ‘yar 30yrs so fresh da ita,
tunda Mannir ya dawo gida kwata-kwata baiga Zainab ba tak’i yarda su had’u ta ganshi,
ta koma zaman bedroom, in banda Mommy da Daddy ma sun hana ta tafiya da tuni ta kama gaban ta,
Mannir sanarwa Daddy yayi akan please yana san su raka shi yabawa Alhaji Abdullahi da Abban Zarah hak’uri ,
ba musu Daddy ya kira amininsa a waya ya sanar dashi zuwansu,
haka ma ya kira Abban Zarah ya sanar dashi su had’u a gidan Alhaji Abdullahi,
dole mommy ta matsawa Zainab ta shirya, motar su Naseer da Zarah ta shiga dan ita duk abinda zai had’a ta da Mannir bata san shi,
shi kuma da mommy da daddy suka shiga mota d’aya,
su Naseer sun riga isa har sun shiga parlor sun zauna, tare da Abban Zarah da Alhaji Abdullahi,
koda Mannir ya shigo ya d’ora idansa akan Zainab yaga yadda ta koma kusan hantsilawa yayi,
ya kafe ta da ido k’uri ya kasa cewa komai,
itako ta had’e girar k’asa data sama, taci magani babu ko alamar fara’a,
sai da Daddy yayi gyaran murya kafin ya dawo hayyacinsa,
murmushi Zarah tayi ganin yadda Mannir yake kallan Zainab,
sai da aka gaggaisa sannan Mannir ya fashe da rikitaccen kuka ‘
Kowa yace ya yafe masa, gaba d’aya parlor aka k’ara neman afuwar juna da ban baki,
sosai jikin kuwa yayi mugun yin sanyi, kuma suka k’ara tsorata da al’amarin mutane da duniya,
bayan an gama komai za’a watse Zarah tayi saurin cewa dan Allah ina san neman alfarma d’aya,
murmushi Zainab tayi had’i da cewa a wajen wa?
Kai tsaye Zarah tace ” a wajenki mommy,
cike da mamaki Zainab tace ” fad’i komai kike so nayi miki alk’awarin zan baki,
murmushi Zarah tayi tace ” ki rantse da Allah komai nake so zaki min,
batare da tunnain komai ba Zainab tace ” wallahi na rantse miki da girman Allah duk abinda kike son nayi miki alk’awari zan miki,
dan yadda Zainab take jin Zarah a ranta, ko ranta tace tana so idan tana da ikon cirowa ta bata to cikin gaggawa zata bata,
musamman yanzu da bata da wata ‘yar sai ita,
ga jinyar datayi sosai har tsawon shekara d’aya da watanni amma bata tab’a gajiya da ita ba,
dai-dai da second d’aya bata tab’a nuna alamar gajiwa da ita ba,
itako me Zarah zata nema a rayuwarta matuk’ar tana dashi ta hana ta,
kai tsaye Zarah tace ” SO NAKE KI KOMA GIDAN DADDY,
da sauri Zainab ta mik’e tsaye a matuk’ar firgice take kallan Zarah ta kasa cewa komai,
Zarah tace ” eh Mommy so nake ki koma gidan Daddy na Mannir da zaman aure………….
MOMYN ZARAHGADAR ZARE!!!
(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)
~NA~
HAUWA A USMAN
JIDDARH
????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
GARGAD’I
MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA
~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO
BEST FRIEND FOREVER & EVERZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~
76
Kowa dake parlor’n shiru yayi, dan jin abinda Zainab za tace,
Zainab za tayi magana Zarah tayi saurin cewa Momy ki tuna fa kinyi min alk’awari kuma kin rantse min da girman Allah, a d’an hasale Zainab tace ” ai ban san irin wannan sakarcin da shirmen zakiyi min ba,
ke ni da aure har abada balle na koma gidan Mannir, Allah yayi, koda ma zanyi aure badai gidan Mannir ba,
shi dai Mannir shiru yayi had’i da sunkuyar da kansa k’asa,
dan yasan Zarah da Naseer zasu yi masa k’ok’arin shawo kan Zainab,
alama Zarah tayiwa Naseer daya saka baki, yi mata yayi alamar shima bai gane abinda take nufi ba,
hak’ora ta cije da k’arfi had’i da zaro masa ido ta kalle shi ta kalli Zainab,
kana tace ” kayi magana, ta yadda babu wanda zaiji sai shi, baki ya motsa alamar auho da bakinsa,
d’an zungurarsa Mannir yayi ya zaro masa ido shima had’i da nuna masa Zainab,
dariya Naseer yayi kafin ya mik’e ya nufi Zainab,
a hankaki yasa hannunsa ya zaunar da Zainab had’i da mik’a mata ruwan sanyi yace “sha,
ba musu ta amsa tasha tana goge gumin dake zubo mata,
sai data gama shan ruwan kana Naseer yace,,
” wai yama za’ayi ace ki koma gidan wani Mannir, kawai kici gaba da rayuwarki haka babu aure,
dai-dai lokacin Mannir ya kurb’i ruwa, jin abinda Naseer yace ” yasa shi kwarewa, had’i da sakar masa muguwar harara,
Zarah ko ido ta zaro waje,
sauran jama’ar dake parlorn duk kallan Naseer su kayi cike da matsanancin mamaki,
ita kuma Zainab sosai taji dad’in abinda Naseer yace dan haka tace,,
” to kai ma dai Naseer ka fad’a amma da yake waccan yarinyar sakarya ce bata da wayou take neman bin bayansa,
ta fad’a tana hararar Zarah.
Dariya dake shirin kwace masa ya danne,
shiru Naseer yayi nad’an wani lokaci kafin yace ” to amma wani hanzari ba gudu ba,
kallansa Zainab tayi ba tare data ce komai ba,
Naseer yaci gaba ” to mutunci kanki fa dana ahalinki, adai shekarunki ba wuce aure da haihuwa kikayi ba,
tunda har yanzu baki wuce 40yrs ba, wanne irin kallon kike ganin duniya zata miki?
“Wanne irin kallo duniya zata yiwa mahaifanki da ahalinki,
a hankali Alhaji Abdullahi ya kalli Abban Zarah dashi ma shi yake kallo,
suka had’a, ganin maganar sa tafara shiga jikin magabatan Zainab yasa Naseer ci gaba,
” kinga za’a rink’a yi musu kallan basu isa dake ba, daga nan za’a fara yiwa zuri’arki baki d’aya wani irin kallo,
tunda ba kowa ne yasan ainahin abinda ya faru ba,
kuma ki tuna girman alk’awarin da kika yiwa ‘yarki, da kuma rantsuwar da kika yi mata da girman Allah,
ita a zatonta kinsan girman Allah da alk’awari shi yasa ta saki ki fara yi mata kafin ta fara yi miki magana,
a hankaki Zarah ta k’ara durk’usawa a gaban Zainab tace ” mommy kefa kike mana wa’azi akan girman alk’awari,
kuma kin fa rantse da girman Allah, please mommy, kafin
Zainab tayi magana Abban Zarah yace ” kai Mannir,
a hankali Mannir ya d’ago kai, Abban Zarah yace ” ka sake ta ne ko da aure a tsananin ku?
Cikin sanyin murya yace ” Abba ban tab’a sakin Zainab ba tunda mukayi aure har yanzu,
har yanzu giyoyi uku ne a tsananin mu,
ajiyar zuciya ya sauke kafin yace ” ok , to ta shirya acikin satin nan ta koma d’akinta,
dad’i kamar zai kashe Mannir, farin cikinsa har ya kasa b’oyuwa,
Zainab kuwa dan dai babu yadda zatayi ne, yasa ta yin shiru,
tasan bakin Abban Zarah d’aya dana Alhaji Abdullahi, duk abinda d’aya ya yanke shikenan,
kwata-kwata basu yiwa junansu musu,
sosai iyayen nasu sukayi musu nasiha mai ratsa jiki da zuciya, hakan yasa jikin su yin sanyi.
A cikin satin aka matsawa Zainab dolen ta sai ta koma gidan Mannir,
sosai Daddy ya kashe kud’i wajen gyara gidan Mannir yadda kasan sabon aure zasuyi, aka gyara gidan tsaf ,
aka saka sabbin Furniture,
sosai gidan yayi kyau, Abba da Zarah ne suka raka ta gidan,
sosai Abba yayi mata nasiha, kafin suka tafi, ya mayar da Zarah gida,
Zainab na ganinta a gidan komai ya dawo mata sabo, take ta kuma jin k’iyayyar Mannir ta dirar ma a ranta,
zama tayi tana kuka sosai kamar ranta zai fita,
Naseer ne ya rako Mannir yasha gayu kamar sabon ango hannunsa rik’e da ledoji,
dariya Naseer yayi yana kallansa kafin yace ” sabon ango ni bari nayi nan, tun kafin amarya tayi jifa dakai ka fad’o min,
yayi maganar yana barin harabar gidan da mota, gaban Mannir ne yayi mugun fad’uwa,
dan yasan yau akwai artabu tsakaninsa da Zainab, gashi yana cikin muguwar sha’awa tun da ya samu lafiya zandariyarsa ta dame shi kamar zata fasa wandonsa ta fito,
dan ji yake a yau idan bai samu mace yaci ba komai yana iya faruwa dashi.