
MOMYN ZARAHGADAR ZARE!!!
(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)
~NA~
HAUWA A USMAN
JIDDARH
????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
GARGAD’I
MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA
~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO
BEST FRIEND FOREVER & EVERZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~
80
(THE END)
Dukkan su suna zaune akan dinning table Zarah ta kalle su tace,
” a gaskiya ya kamata muje mu gano Hamza da Muktar fa,
fuska Zaid da Khamal suka b’ata batare da sunce komai ba,
Fateeha da Lubnah suka ce gaskiya kam ya kamata,
kunga nan ma sai muyi umara,
Basma tace ” eh Allah dan nima ina san ganin Hamza da Muktar ido da ido,
Neaseer yace ” gaskiya ya kamata mu gansu kam,
haka dai sukayi ta tattaunawa amma daga Zaid har Khamal babu wanda yake k’ala,
ganin haka yasa sukayi banza dasu,
Abraham da Abdul suka kira pillot,
wanda jet d’in su ke hannunsa, suka sanar masa ya shirya jibi zai kai su Saudi Arabia,
washe gari suka je prison dake Holland domin ganin Muktar,
yadda suka ganshi yayi bala’in basu tausayi,
dan zai da duk suka toshe hancin su ,
saboda tsananin warin dayake,
acan gefe daga k’arshen gidan yarin aka kaishi,
dan warinsa yana iya halaka mutane da dama,
ko magana baya iyawa, sai ido daya k’urawa Zaid da Abraham yana kallan su k’uri,
a hankali ya kalli Lubnah, dake hawaye, kafin yabi sauran da kallo,
cike da takaicin rayuwarsa da nadama,
yayiwa su Zaid alama da hannunsa,
da su yafe masa, murmushi Zaid yayi yana jin tsananin tausayin sa,
yace ” ni ai na dad’e da yafe maka Mukhtar,
kuma Abraham dasu Abba ma sun yafe maka,
da kyar ya d’aga kai alamar ya gode.
Washe gari jirginsu ya d’aga zuwa k’asa mai tsarki su duka har yaransu,
a madina suka fara sauka sukayi ziyarce-ziyarce,
kafin su k’arasa makka suyi umara,
daga nan sukayi Jidda zuwa gidan yarin da Hamza ke zaune,
basu b’ata lokaci ba Hamza ya k’araso cikin electric walk chair,
yadda suka ganshi sunyi tsannain mamaki,
dan kamala da nutsuwa gami da annuri sunyi bala’in bayyana a tattare dashi,
sosai Hamza yaji dad’in ziyarar da d’an uwansa yayi masa,
ga yaran su nan masu kyau gwani ban sha’awa,
shima Khamal duk zafin da zuciyarsa keyi masa sai yaji ya gushe,
ya k’urawa Hamza ido kamar bazai d’auke ba,
kafin daga bisani suka gaisa sosai,
daga Saudia Nigeria suka yi, domin gaida iyayen su da ‘yan uwa,
aiko duk sunyi farin cikin ganin su,
gidan su Zaid suka fara isa, sosai Ammi da Abba sukayi farin cikin ganin yaran nasu,
dama dangin kowa yasan kowa,
dan haka babu wani bak’unta ko kara, duk gidan su wanda aka je d’aya ne, yadda suka ga dama haka suke yi,
daga nan su kaje gidan su Fahad,
sai gidan su Lubnah da Kausar, sai gidan su Yasmeen,
daga nan sai gidan su Naseer wajen Momy da Dady,
har gidan su Abban Zarah da Alhaji Abdullahi ma sunje sun kai gaisuwa,
kafin daga k’arshe suka zube a gidan Zainab da Mannir,
acan sukaci abinci,
ranar Abdul yasha kuka kamar ransa zai fita kasancewar bashi da kowa a duniya bashi da wanda zai kira da nasa,
dakyar suka iya shawo kansa,
dama lokuta da dama hakan tana faruwa dashi idan ya tuna abin.
Haka rayuwa tayi ta tafiya lokaci na shud’ewa,
yayinda SIX STAR’S ke k’ara samun d’auka,
daga wajen al’umma har zuwa ga kan cimpanies d’insu,
dan yanzu duk Nigeria da Holland babu cimpanies d’in da ake ji da su kamar SIX STARS,
sun d’aukaka sosai a fad’in duniya,
sunan su babu inda bai je ba, sun tara dukiya mai tarin yawan da su kan su basu san yawan ta ba,
idan za’a kashe su basu san iyakacin abinda suka mallaka a duniya ba,
shiyasa suke taimakon al’umma,
duk inda sukaje ana neman taimako da gaggawa suke kaiwa tun kan a rok’e su,
suna da tarin gidajen marayu,
masallatai, rijiyoyi da bohol, da asibitoci,
suna shiga k’auyuka suna kai taimako,
suna yin hanyoyi, makarantun boko dana islamiyya a gurare da dama,
Allah yayi su da tsananin tausayi da jin k’ai,
shiyasa a kullum Allah yake k’ara d’aukaka su.
Haka ma matan su suna da matuk’ar taimako,
sun gina k’ungiyoyi da dama na taimakon mata, da tallafawa marasa galiho,
kan su a had’e yake sosai, babu abinda ke shiga tsakanin su,
kullum suna tare, babu abinda d’aya zayyi a duniya batare da sauran sun sani ba,
dai-dai da kaya iri d’aya suke sawa har hola da agogo,
komai nasu iri d’aya ne sak,
duk inda kaga d’aya to sauran ma suna nan,
dan dai-dai da cinema & shan ice cream tare suke zuwa,
haka ma matan su, yayinda yaran su ke girma sosai, dan tuni manyan yaran su sun wuce 10yrs,
kuma suna da burin a junan su zasu aurar da yaran su,
babu wani daga cikin yaran su da zayyi aure a waje.
A b’angare Zainab ma suna cikin farin ciki da kwanciyar hankali,
yaran su sun girma sosai, haka ma Litle Ikram tayi wayo sosai,
Dady da Momy sun manyanta sosai, hakan ne yasa suka mik’e komai hannun yaran su,
su kuma suka zauna suna ibada,
Mannir kam kullum cikin istigfari yake yana neman yafiyar Allah, akan abubuwan daya aikata a rayuwarsa,
Alhaji Abdullahi shima tsufa ya kama shi sosai, dan haka ya mik’ewa Abban Zarah komai na dunkiyarsa,
shima dan ya huta.
A fannin Ammi da Abba, Muhammmad Bature iyayen Zaid,
ma hakan ce ta kasance dan dama shi tuni ya dad’e da mik’ewa Abraham da Zaid komai,
ya zauna shida matar sa suna d’iban korayen fure, shima ya manyanta sosai,
kullum cikin taimako da idaba suke,
a b’angaren Mukhtar ko sai dai muce Allah ya kyauta,
domin halin dayake ciki ya wuce tunanin mai tunanin, ya zama kamar dodo, abin kyama ga mutane,
ga tsananin cewo dayake fama dashi,
tsotsi da wani irin mugunya ke zuba daga jikinsa,
dangin Abraham na Yola kullum sai san barka saboda yadda yake taimakon su, ya mayar dasu masu arziki,
duk ya kwashe yaran su ya basu aiki.
Hamza kam an zama malami duk da ba hannu ba k’afa,
ya tara gemo da k’asumba, kullum yana cikin nadama da kukan takaicin yadda ya cuci d’an uwansa uwa d’aya uba d’aya akan mace,
yaci amanar sa, ya nemi kashe shi,
sosai Hamza ya duk’ufa neman yafiyar Allah, kullum yana cikin karatun Al’Qur’an,
ya zama mutumin arziki mai cikekkiyar kamala da nutsuwa.
Meenal da Haidar k’annan Kausar da Fahad suna zaune lafiya,
cikin kwanciyar hankali da nutsuwa,
sosai Haidar ya nutsu ya daina duk munanan halayansa, ya tuba zugawa Allah,
suna da yaran hud’u maza biyu mata,
haka ma Sheemah da mijinta Farouk suna zaune lafiya, ta zubar da duk mugauen halayanta, ta zama macen kirki, nutsatstskiyar mace, mai kamun kai, itama kullum cikin istigfari take,
suna da yara uku, mata biyu namiji d’aya,
a fannin su Hajiya Lailah da Hajiya ma haka abin ya kasance sun dai na duk wasu munanan d’abi’un su, sun rabu da k’awayen su na banza,
sun kama kan su, da girman su sosai,
rayuwa suke yi cikin mutunci da kamala,
suna zaune lafiya da juna suna neman yafiyar mahaliccinsu,
Ummi ma tayi aure tana da yara biyu duka mata,
tun abinda ya faru a shekarun baya ta tuba bayan ta koma gidan su,
ta nutsu tayi aurenta tana zaune lafiya, kuma har yanzu suna zumunci dasu Hajiya Lailah,
Sanata Sambo ma ya tuba ya koma na Allah yana zaune da mutane lafiya,
yana kyautata mu’amularsa da kowa,
sosai ya shiga yaimakon Al’umma da dukiyarsa,
koya samu rabauta duniya da lahira a wajen Allah,
yayinda Boka Jimrau ya dad’e da bin kwalta yana tsince-tsince (hauka).