
Bayan wasu kwanaki aka sanar dasu Abdul cewa wasu ‘yan iska sun k’ona Umar a gidan yarin wai ya dame su da wari.
Basu samu matsala ba wajen iyayen Yasmeen kai tsaye suka amince aka d’aura auren Yasmeen da Abdul, Sanata Sambo ne ya tsaya akayi bikin shiyayi komai, da taimakon Haidar da Sanata Sambo Abdul da Yasmeen suka tsallake suka bar Nigeria,suka d’aga zuwa Holland, Haidar ne yayi musu komai na tafiyar, sannan ya kawo 1 million ya basu.
Bayan shekara 2 sosai Haidar ya damu Abdul sannan yazo Nigeria, Yasmeen d’auke da kyakkyawan yaron ta mai sunnan Baban Abdul Muhammad suna kiransa da Nabil, shima Haidar yayi aure ya auri KAUSAR, Sanata Sambo shine ya zamewa Abdul uba, ya zama kamar mahaifinsa, duk duniya Abdul baida kamar Haidar da Sanata Sambo idan ka cire Yasmeen da Nabil.
Abdul ya d’ago kai ya kalli sauran jama’a yace ” to kunji labari na, sosai jama’a ke kuka, musamman 6’S STARS Al’amin ya kalli Abdul yace ” to ranka ya dad’e ina HAIDAR & SANATA SAMBO suke yanzu? Kuma naji kace sunan matar Haidar KAUSAR?”
Da k’arfi k’irjin sa ya buga dammmm!! ya juya kalli Yasmeen da Fahad da Kausar…………………
MOMYN ZARA
[21/01, 04:12] +234 701 517 2910: GADAR ZARE!!!
(IT’S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)
~NA~
HAUWA A USMAN
JIDDARH
????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
GARGAD’I
MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES , SU KARANTA BA
~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDU
11
K’orafin ku ya karb’o masoya na, in sha zan ci gaba da posting a WhatsApp, amma sai na fara yi a wattpad.
Da k’arfi k’irjinsa ya buga dammmm! ya kalli Yasmeen, Fahad, Kaudar…
Sai ya maida kallon sa ga Al’amin, murmushi yayi yace ” yana nan , ” to yana ina? cewar Al’amin, a fusace Abdul yace ” yana nan nace mak….. A’a a fad’a musu gaskiyar lamari cewar Fahad, “no Fahad inji Abdul, dafa kafard’ar Abdul Fahad yayi ya k’ura masa ido ya langwab’ar da kai yana yi masa alamar please, murmushi Abdul yayi yace ” Ok.
Fahad ya d’ora da cewa ” ni ne HAIDAR ya b’oye muku ne sakamon maganar fyad’en Aisha, shiyasa ya sakaya sunana, amma magana ta gaskiya nine HAIDAR, kuma ainihin sunana FAHAD ne ba HAIDAR ba, sannan bani kad’ai SANATA SAMBO ya haifa ba mu uku ya haifa, nine babba sai gani na, shine HAIDAR, amma bashi ne na cikin labarin Abdul ba, ni ne acikin labarin Abdul, sai k’anwa ta Zakiyyah, sai Momyn mu, sannan gaba d’ayan mu uwar mu d’aya uban mu d’aya.
” zaku ji sauran labarin dangina idan matata Kausar zata bada labarinta, sannan Sanata Sambo yana nan a raye, yanzu baya komai sai aikin Allah, yana amfani da dukiyar sa ne wajen yiwa musulci da musalmai hidima.
“Ya b’oye sauran yaran nasa ne, saboda yanayin siyasa, hakan ne yasa bai bayyanawa duniya k’anne na ba, sai bayan da komai ya zama dai-dai hankali ya kwanta sannan ya bayyanawa duniya su.
Bayan Fahad ya gama bayanin ne, ya kalli sauran jama’ar yace ” zamu je muyi sallah idan mun dawo sai muci gaba, Khamal ne fara bada nasa labarin.
Duk suka mik’e suka shiga cikin 6’S STARS Hotel, bayan sunci abinci sunyi sallah suka d’an huta sannan suka dawo, bayan komai ya dai-daita Fahad ya kalli Khamal yace ” oya start , murmushi Khamal yayi ya suma.
LABARIN KHAMAL
Ainahin sunana Khamaludden Ahmad, haifaffaan garin Kaduna ne unguwar rimi, mu biyu iyaye na suka haife mu, ni da k’anina HAMZA, tun muna yara iyaye mun suka mutu, a hannun kakarmu muka taso ita ce komai namu, bamusan kowa namu ba sai ita, kakar mu wacce muke kira da Hajiya ta d’auki san duniya ta d’ora mana, kasancewar mahaifin mu ne kawai d’an data haifa a duniya gashi kuma ya rasu.
” ni kuma na d’auki san duniya na d’orawa Hamza, dan gani nake kamar shine gata na, kasancewar bamu da kowa, duk abinda Hamza ke so to nima ina sanshi, haka duk abinda baya so nima bana sanshi, haka duk abinda ya gani yana so hankali na baya kwanciya sai naga ya mallake shi, idan da abinda nafi tsana a rayuwa ta shine b’acin ran Hamza.
“Kamar yadda nake san Hamza haka shima abin yake a b’angaren sa, koma ince yafi so na, fiye da yadda nake sanshi, dan ko ciwo na kwanta to shima sai yayi rashin lafiya ba k’aramar shakuwa ce a tsakanin mu, daga ni harshi babu mai aboki, mu biyu ne kawai muke rayuwar mu, har Allah yasa muka shiga jami’a, ni ina level 4 Hamza yana level 2.
” tun ina yaro Allah ya d’ora min masifar san ball, hakan ya sani nacewa ball, dan haka na zama cikekken d’an ball, nayi zarra sosai, harta an fara fita outing garuwan mu na nan gida Nigeria dani.
” haka kuma a jami’a nake ta karatu na, sosai na dage nake karatuna, dayake Medicine nake karanta, dan duk class din mu nayi fice, babu kamata,
Khamal na zaune yana duba wasu handouts, kansa a k’asa yaji ance “sannu ko, bai d’ago kan sa ba, yace ” yawwa, jin wata siriyar murya mai zak’i yayi tace ” please aron biro zaka bani yanzu zan maido maka, kai ya d’ago had’e da cewa ” ok…. a mak’ogwaro maganar ta tsaya masa kasancewar wata dalliyar yarinya daya gani, tuni Khamal ya tsunduma duniyar tunani, ka kafe ta da ido, sai magana take amma ina hankalin sa ya tafi baima san tana yi ba.
D’an guntun tsaki taja a ranta tace ” maye, k’afarta ta saka da taka k’afarsa da k’arfi, aiko yayi firgigit yace ” hmmm ga biron ya mik’a mata asuwakin dake hannunsa dariya tayi tace ” biro nace ba asuwaki ba, aiko tuni dariyar ta ta k’ara tafiya da imanin Abdul.
Ganin bai ma san me take ba yasata yin tsaki da k’arfi ta juya zata tafi, tsakin ne ya maido da Khamal hankalin sa, da sauri ya mik’e yace ” sorry gashi ya mik’a mata biro, in banda dole babu abinda zai sata karb’ar biron, warta tayi had’i da watsa mai uwar harara tayi gaba.
Hannu yasa ya shafo sumar kansa had’i da sakin murmushi, tun daga ranar Khamal ya kamu da mugun san yarinyar gashi bai k’ara ganin ta ba, ko karatu ya kasa dan daya kalli Handouts d’in furkarta yake gani, shi kad’ai zaka ga ya zauna yana sakin murmushi.
Shima Hamza tuni ya dad’e da kamuwa da mahaukacin son wata yarinya kamar yayi hauka, dan ko numfashi zai ja da yarinyar yake yi, sosai yake jinta a ransa, suna zaune a d’aki Hamza ya kalli Khamal yace ” Yaya ina cikin damuwa fa, da sauri Khamal ya daina abinda yake ya maida hankalinsa ga Hamza yace ” meye matsalarka bros?
Cikin yanayin tausayi Hamza yake kallon Yayan nasa yace ” wallahi Yaya wata yarinya nake bala’in so amma kwata-kwata tak’i kulani, babu yadda banyi ba amma tak’i ji nake kamar nayi hauka, ya k’arashe maganar kwalla na zubo masa, da sauri Khamal yasa hannu yana goge masa hawayen dake zuba ya jawo shi jikinsa ya rungume yana shafa bayan sa, yace ” karka damu bro in sha Allah zata so ka, sai ma tayi hauka a kanka, zan koya maka yadda zaka b’ollo mata, k’ara rungume Khamal yayi yace ” nagode bros.
A hankali Khamal ya zame jikinsa daga nasa ya kalle shi ya kanne masa ido d’aya yace ” bros nima fa na kamu, ido Hamza ya zaro waje yace ” da gaske Yaya? Cikin murmushi Khamal yace ” da gaske amma kusan matsalar mu d’aya, nan Khamal ya fad’awa Hamza komai, ya k’ara da cewa, tun daga ranar ban kuma ganin ta ba, da tausayawa Hamza yake duban Khamal yace ” ayya Yaya karka damu kaji in sha Allah zaka ganta, kuma cikin sauk’i zaka shawo kanta, ” Amin bros ngd kaji.