
Cikin kwanciyar hankali Khamal yake tuk’in mashin d’insa (lifan) zuwa gida ga uban hadari ya had’o, ga iska na kad’awa a hankali aka fara yayyafi, kamar daga sama Khamal yaga hannun mace tana tsaida shi da farko k’in tsayawa yayi, sai kuma yayi tunanin akoyaushe ruwa yana iya sakkowa, a hankali ya juya baya, saboda iskar da akeyi ne yasata jan mayafi ta rufe fuskarta, bismillah yace mata, a hankali ta dafa kafad’arsa ta hau mashin d’in, wani irin yarrr yaji Khamal, kasancewar wannan ne karo na faro da mace ta tab’a tab’a shi, a hankali suke tafiya, cikin muryarta mai dad’i tace ” nagode! K ‘irjin khamal ne ya buga da k’arfi dajin muryar ta, sosai zuciyarsa taci gaba da bugawa.
Magana taci gaba dayi tace” kasan me? ” a’a ya bata amsa, ” da da farko danaga ka wuce sai naji babu dad’i dan harna fara hango yadda ruwan sama zaiyi min dukan tsiya, gashi bana san sanyi, murmushi Khamal yayi yace ” dana dawo kuma fa? ” ai sosai naji dad’i, kasan me? a’a Khamal ya kuma fad’a ” ina bala’in san irin wannan yanayin sosai, sosai nasha duka a gidan mu saboda wankan ruwa, sosai taci gaba da zuba masa surutu kasancewarta mai shegen surutu har Khamal ya gaji da surutunta, suna cikin tafiya aka tsuge da ruwan sama aiko sosai ta shige and kinsa, ta saka hannuwanta ta rungumo shi ta baya, gaba d’aya Khamal ya fita hayyacinsa cikin k’arfin hali yake tuk’in mashin d’in, kwatance take masa amma sama-sama yake jinta, a bakin titi tace ya sauketa sai da maimaita masa yakai sau biyar sannan Khamal yaji, a hankali ta sake shi, yace ” mai tasa baza ki bari na kai ki har k’ofar gida ba?
“Nan ma ya isa, bana san na b’ata lokaci ne, kaga kuma kaima kana son ka koma ka canja kaya, ta fad’a tana k’ok’arin saukowa aiko tana taka k’asa santsin ruwa ya kwashe ta tayi baya zata fad’i da sauri Khamal ya rik’o ta fad’a jikinta, mayafin data rufe fuskarta ya yayi Fuska ta ta fito, sosai Khamal ya shiga tashin hankali, zuciyarsa ta tsananta bugawa da k’arfi a hankali yace ” kece?
” eh nice ta fad’a tana barin jikinsa, ta juya tana tafiya da sauri Khamal yace ” ba godiya? ” bayan wacce nayi maka wata kuma kake so? tana tafiya tana bashi amsa, yace kin manta baki fad’a min sunanki ba, tana kaiwa dai dai kwana tajiyo tayi mishi wani rikitaccen murmushi, ta wuce aiko suman zaune Khamal yayi dan yakai 10mts bai tafiya, yana kallon k’asa yaga ID card d’inta, a hankali ya d’auka yana dubawa sunanta ya gani FATEEHA ya gani a rubuce, murmushi yayi mai bayyana hak’ora.
D’akinsa ya wuce kai tsaye ya cire kaya ya fad’a bathroom yayi wanka, jallabiya ya zira, waje ya fito ya zauna kusa da Hajiya yana ta faman sakin murmushi, aikinta taci gaba dayi bata kalle shi ba tace ” wacece?
Murmushi ya sake saki yace ” kai Hajiya ya akayi kika gane? Dariya tayi ta maida kallanta kansa tace ” haba khamalu yanzu har yanayinka ya canja na kasa ganewa, nafi kowa sanin waye kai Khamalu, dariya yayi yace ” FATEEHA sunanta, mik’ewa tayi ta koma kusa dashi ta kama kumatunsa ta shafa kansa tace “ja’iri, kayi k’ok’ari ka kawo min ita kona samun sauk’in aiki.
Dariya yayi yace” kai Hajiya aiki zaki rink’a tulata mata, gaskiya ni dai a’a ya fad’a cikin shagwab’a, suna haka Hamza ya shigo, “yawwa bros k’arasu da labari fa! da sauri Hamza ya k’araso yace ” ta samu kenan Yaya? ” sosai ma, ” da alama dai Yaya ka samu yarinyar nan, Khamal yace ” ka canka daidai bros, nan ya kwashe komai ya fad’a masa, ” gud Yaya you are so smart, dama nasan zaka iya.
Dariya Khamal yayi yace” ka daina fada min kai mana, kaga ni dai ya maganar ka da yarinyar nan? Dariya yayi yace” ina nan inayin yadda ka sani.
” yawwa bros, Allah yasa ka shawo kanta da sauri, Hajiya ta wuce su tana dariya tace ” ja’iran yara, Hamza ya mik’e ya rungumo ta baya yace” Hajiya ke kinganta kuwa? fara sol kamar ke, data duguwa ga manyan ido da dogon hanci, duka ta kai mishi tace” ban guri marar kunya kawai, Khamal na gefe yana dariya.
Washe gari da wuri Khamal ya shirya ya fita zuwa gym yana tafiya ya hango ta tare da k’awarta, da sauri yayi parking ya bita yana kira, a hankali ta jiyo, murmushi yayi mata yace ” barka dai?
Bata bashi amsa ba fuskarta babu yabo babu fallasa, tace ” waye kai? Ido ya zaro ya nuna kansa yace ” wai ni? tace ” a’a ni, dariya yayi a ransa yace ” kai mata akwai rainin hankali, ” ok kai kanka baka san kanka ba kenan, ta fad’a tana ci gaba da tafiya, da sauri ya tari gabanta yace ” sunana Khamal Ahmad, ina karantar medicine, sannan ni….. Hannu ta d’aga masa tace ” fad’i , yace ” me kenan? “abunda ke ranka mana, “oh Khamal yace, dama kin manta ID card dinki ne jiya ya fad’a yana mik’a mata card d’in, karb’a tayi ta wuce yace ” haba Fateeha ba godiya kuma? ” bayan wacce nayi maka wata kuma kake san nayi maka, “yaushe kika ce min kin gode? ” baga shi nan ka fad’a yanzu ba, ta fad’a tana tafiya, dariya Khamal yayi, yana tunnin rainin hankalin Fateeha, harta shige gida,k’ofar gidan yabi da kallo yana murmushi, lek’o da kanta tayi ta sakar mishi murmushi, sosai murmushin ya tafiya da Khamal.
Ranar Monday around 5:30pm ya fito daga lectures a gajiye, direct ya wuce cafeteria, a zaune ya gansu su biyu ita da k’awarta ta jiya, murmushi yayi ya nufe su, k’awar ce ta fara ganinsa, a hankali ta rad’a mata ga mayenki nan, ” what? Fateeha tace, kafin ta rufe bakinta ya k’araso inda suke, a hankali ya kalle ya da alamar tausayi yasa babban d’an yatsansa a baki, kallonsa tayi rai a b’ace zatayi magana da sauri ya tare ta yace ” a’a pls karki ce komai ni zance yadda yayi maganar maganar dolo.
Kwaykwayon maganarta ya shiga yi yace ” waye kai? sai yayi maganar normal yace ” ni ne na jiyan nan dana kawo miki ID card, sai kuma ya kuma kwaykwayon maganar ta yace ” oh! to lafiya? cikin maganar sa yace Alhamdulilla……a fusace ta mik’e cikin masifa tace ” wai mai yasa ka takura min me!? haba ka dame ni, ido ya k’ura mata a ranta kuwa yace ” masha Allah, ita komai kyau yake yi mata, yadda ya k’ura mata ido ya k’ara hasala ta, ta kalli k’awarta tace ” Khadija zo mu tafi, da sauri ya sha gabanta, tsaki tayi, ta juya idonta had’i dafe kanta, amalar ta gaji, Khadija ta kalle ta tace ” please ki saurare shi, kiji abinda zai fad’a miki, inba haka ba bazai daina bin mu ba, mu zama abin kallo.
Tsayawa Fateeha tayi ta kalle shi, tace ” fad’i nutsuwarsa ya tattara ya maida hankalinsa jikinsa, with full confidence ya kalle ta yace ” ina sanki, ido ta zaro waje tana kallansa, ” eh Fateeha ina sanki, ina miki mugun so, ta yadda koyaya na motsa sai kin fad’o min, duk numfashin dazan ja dake nake yinsa Fateeha, ina sanki tsakani da Allah, i love you with all my heart, u are my first love please don’t say no, yana fad’a ya juya yayi tafiyarsa, baki bud’e Fateeha tabi bayansa da kallo, cike da mamaki, hannunta Khadija ta kama suka tafi, a k’ofar gida aka sauke Fateeha, Khadija ta dafa kafad’arta tace ” kiyi tunani k’awata karkiyi wasa da damarki, Khamal cikekken namiji ne da kowacce mace zata so ta mallake shi.
Cikin sanyin jiki Fateeha ta kalli Khadija tace” nagode sosai kawata da shawarar ki, tunda Fateeha ta koma gida ta kasa samun nutsuwa gaba d’aya tunanin maganganun Khamal da Khadija ya hana ta sakat, sosai yake fad’o mata arai, tana jin sa a ranta, sannu a hankali san sa ya rink’a shiga jin kinta, batare data yi aune be ya gama mamaye ko’ina nata, burinta kawai ta k’ara ganin sa.