
Washe gari sun safe ta shirya kasancewar tana da lactures da safe, sai da kammala komai sannan ta fita, sai yamma sosai suka fito, a bus stop ta tsaya duk ta gaji Allah Allah take ta koma gida, ga rana na dukanta, duk bayan minti d’aya sai tayi tsaki, a gabanta yazo ya faka, had’i dayi mata sallama, a hankali ta d’ago kai ta kalle shi, sanye yake da light blue d’in shadda tasha simple aiki, ya saka hula, hunnan sa manne da agogo, sosai yayi mata kyau, sosai taji dad’in ganinsa, b’ata face tayi, ta kauda kai had’i dayin tsaki, murmushi yayi, ya kafe mashin d’in yazo kusa da ita ya zauna, mik’ewa tayi ta fara tafiya, murmushi ya kuma yi sannan ya mik’e ya hau mashin d’insa a gabanta yaje ya tsaya yace ” mu tafi ko?
Kallansa tayi tace ” ce maka akayi kai nake jira? “A’a yace, please ki hau mu tafi, kinga yamma tayi, tafiyar ta taci gaba da tafiya, binta ya rink’a yi yana daga kan mashin d’in, sai da lallab’a ta sosai sannan ta hau ya kaita gida, sosai Khamal yayi mamakin ganin gidan su, saboda babban gida ne, da gane kasan ‘yar masu hali ce, sauka tayi bata ce masa komai ta shige gida, da sauri ya kalle ta yace ” haba ke kuwa ya ba godiya, juyowa tayi ta sakar masa k’ayataccen murmushi, suman tsaye Khamal, harta shege gida bai sani ba.
MOMYN ZARA
[21/01, 04:12] +234 701 517 2910: GADAR ZARE!!!
(IT’S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)
~NA~
HAUWA A USMAN
JIDDARH
????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
GARGAD’I
MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES , SU KARANTA BA
~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO
12
Da yamma Khamal ya shirya ya d’au fitinannan wanka ya nufi gidan su Fateeha a bakin get yayi faki ya kwankwasa mai gadi ya lek’o yace ” lafiya Malam? ” lafiya dan Allah yimin magana da Fateeha, kallansa mai gadin yayi cike da mamaki yace ” kunyi da ita zaka zo ne? “Eh cewar Khamal, ” ita Fateeha ce da kanta ta baka izinin? Cike da k’osawa Khamal yace ” nace maka eh, kai mai gadin ya jinjina sannan yace ” ikon Allah, da mamaki Khamal ya kalle shi yace ” ya akayi ne?
Murmushi mai gadin yayi yace ” abin ne ya bani mamaki, ” mamaki kuma? cewar Khamal, ” eh kasancewar yau ne rana ta farko dana ga hakan, dan kwata-kwata Fateeha bata kula samari, tun Fateeha tana yarinya nake aiki a nan gidan amma ban tab’a ganin wanda yazo yace yana sallama da ita ba sai kai yau.
Murmushin jin dad’i Khamal yayi yace ” Alhamdulillah, da sallama ya shiga falon ya iske Fateeha da Momy zaune suna aikin kallon, tare suka amsa masa sallamar tasa, Hajiya k’arama ana sallama dake, ido ta zaro tace ” ni? Momy ko saboda tsabar mamaki ta kasa cewa komai, dan tasan halin Fateeha duk wanda yace yana santa tsiyatsiya suke rabuwa, da kallon Fateeha kawai take da Mamaki, Fateeha tace ” je kace bata zuwa, har mai gadi yayi nisa sai tunaninta ya bata Kodai Khamal ne?
Aiko bata san sanda ta kwala mai kira ba, tace ” ce ne waye? Dawowa yayi yace ” wai yace ” Khamal ne, bata san sanda murmushi ya kufce mata ba, cike da murna tace ” shigo dashi d’akin bak’i, murmushi mai gadi yayi dan yasan bata isa tak’i amincewa Khamal ba, dan duk tak’amar kyan da takeyi Khamal ya fita, mai aikin su ta kira ta sata ta kaiwa Khamal ruwa da lemo.
Ita dai Momy shiru tayi tan kallon ikon Allah, aranta kuwa cewa take wannan wanne mai sa’ar ne? d’aki ta koma ta shirya cikin riga da zani na atamfa, ta shafa farar hoda da lip glo, ta saka takalmi da mayafi 2 match ta feshe ilahirin jikinta da perfumes, ta nufi falo cike da farin ciki, da d’okin ganin sa, ita dai Momy ido kawai ta zuba, tana ganin ikon Allah.
A zaune ta same shi, da sallama ta shiga, a d’aya daga cikin kujerun ta zauna, kallon ta yayi his face with smile, yace ” kinyi kyau, face ta ya mutsa tace ” wannan itace kalmarka mafi tsada? murmushi yayi dan ya fahimci Fateeha ba k’aramar ‘yar rainin hankali bace, hira suka d’an tab’a sama-sama tana yi tana bashi amsar rainin hankali, dakyar ta bashi phone number ta, harta kai bakin k’ofa zata fita yace ” ya b aki bani amsa ta ba, juyowa tayi tana d’an yamotsa fuska tace ” amsar me? “nace I love you, but u didn’t reply me, tsaki ta d’an ja ta fita, mik’ewa yayi yana murmushi ya fita, k’ofar dayaga ta shiga yabi da kallo yana ‘yar dariya, a hankali ta da fuskarta ta sakar mishi murmushi, dariya yayi mata yana cusa hannunsa cikin sumar kansa.
A hankali ta motsa bakinta tace ” I love you too, sai tin zuciyar sa ya dafe yana yi mata dariya marar sauti, haka kowannensu ya koma gida cike da farin ciki, da dare bayan ya gama duk abinda ya saba kan ya kwanta, sannan yayi dialing number ta, sai da yayi mata 2miss call, sannan ta d’aga, ” waye abinda ta fara cewa kenan, murmushi yayi mai sauti yace ” ur hubby, ” what my hubby? ni bana da wani hubby, please waye? ” ok Khamal ne, ” wanne Khamal kenan, ni ban san wani Khamal ba, sai da ta gama raina masa hankali, sannan suka tsunduma hirar soyayya, ranar kowannen su yayi kwanan farin ciki.
Washe gari bayan sun tashi daga lactures, a gajiye likis ta fito tana ta had’a hanya, a gabanta yayi parking fuskarsa d’auke da murmushi yace ” mu tafi ko? ba k’aramin kyau yayi mata ba dan haka bata san sanda ta sakar mishi murmushi ba, ba musu ta hau, suka tafi, a k’ofar gida ya sauke ta, sai da suka d’an tab’a hira sannan ta shiga gida, tun daga harabar gidan su take jiyo hirar mutane a falo, da sallama ta shiga falon Dady ta gani tare da Ja’afar d’an aminin Dady, ya dad’e baya Nigeria, a Malaysia yake karatun, lokacin dayake Nigeria he is her Best friend, da har iyayen su suna expecting soyayya suke, wacce ita a zaton Fateeha shak’uwa ce kawai ace shi a b’angaren sa, bahagon so yake yiwa Fateeha tun suna yara yake mata mugun so, da sauri ya mik’e ya nufe ta da murna, itama cikin farin ciki tace ” Ja’afar yau she ka dawo? ” yau dawowa ta kenan ko abinci ban ci ba nace bari na zo naga my Fatee nasan yanzu ta girma, cikin shagwab’a tace ” amma shene ko ka gaya min, ” sorry my Fatee so nake nayi surprising naki ne, ” to yanzu nasan dai baka ci komai ba, ban some minutes in sha na d’an watsa ruwa, nayi sallah na fito sai na girka maka best food dinka, Dady ko baki har kunne sai fara’a yake, ” ok yace, da sauri ta shige d’aki.
Wacece Fateeha
‘Ya ce ga Alhaji Nasir, tsohon soja ne dan har ya kai matsayin mojor general kafin yayi retired, Hajiya Zainab ita kad’ai ce matar sa auren zumunci iyayen su suka yi musu, Hajiya Zainab macece mai hak’uri da kawaici, Alhaji Nasir mutum ne mai zafi yana da fad’a da kafiya, Fateeha ita ce kad’ai ‘yar sa suka haifa, bayan ita Allah bai k’ara basu haihuwa ba, dan haka ta taso cikin gata da kulawa, amma duk da haka sun bata cikekkiyar tarbiyya, hakan bai sa sun saketa ko sun barta ta sangarce ba.
Daf da magrib Fateeha ta fito daga d’aki tace ” bari nayi sauri na d’an sama maka wani abun ko, tasowa yayi ya nufe ta yana dariya yace ” no ki raka ni restaurant kawai, naga lokaci ya k’ure, ” haba Jafy ka kadawo yau d’in amma ka ci abincin restaurant? ” eh bakomai yunwa nake ji sosai muje kawai gobe sai kiyi min girkin kinji please, ” ok tace ta shiga d’aki ta d’auko hijab ta zira suka tafi, da kallo Dady yabi su yana murmushi yace ” Allah ya nuna mana lokaci, ” Hmmmm Momy tace.