GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

A round about Khamal ya gansu danja ta tsaida su, gabansa ne ya fad’i, nan da nan yaji wani mugun kishi ya taso masa musamman yadda ya gansu tana zaune a gaban mota yayi dashi kuma yake zaune a mazaunin driver gaba d’aya ya karkata hankalinsa gare ta, sai dariya suke, danja na fasu hannu yabi bayan su, a Food Palace Ja’afar yayi parking, ya zagaya ya bud’e mata murfin motar, suka jera suka shiga, duk abinda ke faruwa akan idon Khamal, in banda tafasa babu abinda zuciyar sa keyi, parking shima yayi ya shiga a zaune ya hango su, gurinsu ya nufa d’aya daga cikin kujerun wajen yaja ya zauna ya sakar mata wani fitinan nan murmushi.

Ido ta zaru tana kallonsa, alama tayi masa daya tashi, dariya yayi yace ” ai da kika kira ni a waya kikace mu had’u anan nayi mamaki kasancewar a gida muka saba had’uwa, ya k’arashe magana yana kashe mata ido d’aya, zatayi magana service din gurin yazo ya fara gabatar musu da abinda suka bada Oder, gyaran murya Ja’afar yayi,.
Shima Khamal yayi kamar bai san yana zaune ba.

Kallon Ja’afar Khamal yayi ya mik’a masa hannu fuska d’auke da fara’a yace ” sorry ban lura da kai ba, kasan idan ina tare da my heart mantawa nake da kai na ma, shima fuska d’auke da dariya yace ” gaskiya kam, murmushi tayi tace ” Khamal wannan cousin d’ina ne sunan shi Ja’afar, ta kalli Ja’afar tace ” wannan ne Khamal, shagwab’e face Khamal yayi yace ” baki gaya masa waye ni ba, ta bud’e baki zatayi magana yayi sauri ya tare dan yasan tana iya bada shi yace ” bari kawai basai kin wahalar min da bakin ba zan gaya mishi ya kalli Ja’afar yace ” nine mijinta wanda zata aura very soon in sha Allah, yak’e Ja’afar yayi yace ” masha Allah, sanin halinta ne yasa shi mik’ewa tun kafin ta kunya ta shi, ya rik’o hannunta a hankali yayi mishi kiss, ya kashe mata ido d’aya, yayi kamar yayi mata rad’a a kunne sannan yace ” I love you too sweetheart, yayi saurin ficewa, itako mamaki ne ya hanata cewa komai.

Tasan tsabar kishi ne ke yawo da Khamal shine yasa shi yin hakan, kasa cin abincin Ja’afar yayi, ko a mota sama-sama sukayi hira, a falo suka tarar da Momy da Dady zaune, kusa da Dady Ja’afar ya zauna, ya kasa cewa komai Dady ne ya lura da yanayinsa dan haka yace ” lafiya dai, kaci abincin? ” eh Dady dan har Khamal ma ya yazo, ” waye kuma Khamal? cewar Dady ” nima ban san shi ba, Fateeha ce tayi masa waya ya same mu acan, sai sannan Dady ya gane dalilin canjawar Ja’afar murmushi yayi sannan ya kalli Fateeha yace ” waye shi? Dariya tayi tace ” Dady wani ne kawai ta fad’a tana mik’ewa, shiru Dady yayi baice mata komai ba, ta shige d’aki tabar Ja’afar anan yana ta faman kumbure-kumbure.

Sannu a hankali soyayya mai k’arfi ta rink’a shiga tsananin Fateeha da Khamal, had’i da muguwar shak’uwa, sosai suke mugun son junan su, ji suke kamar d’ayan su bazai iya rayuwa babu d’aya ba, kullum suna tare, idan ko suna gida to suna tare a waya, sunyiwa junansu mummunan sabo da juna, yayi da Ja’afar ke ta haukan son Fateeha dan ji yake kamar yayi hauka, sosai ya fara fita daga hankalinsa, kwata-kwata baya cikin nutsuwarsa, duk ya zama wane iri iyayensa sun kasa gane kansa, haka ma a b’angaren Hamza kwata-kwata yarinyar da yake so tak’i kula shi, yayi yin duniya amma taki bashi koda fuska ce, duk ya rud’e ya shiga matsanciyar damuwa ya rame yayi bak’i ya gode, ko abinci baya iya ci, sosai Khamal ya shiga cikin muguwar damuwa saboda halin da Hamza yake ciki, gashi yak’i nuna masa yarinyar.

Hatta Hajiya kakarsu tana cikin damuwa sakamakon ganin Hamza cikin muguwar damuwa, duk sun tada hankalin su, sosai Khamal ke kwantar mishi da hankali had’i da fad’a masa in sha Allah zai mallaketa.

Ganin irin mawuyacin halin da Ja’afar ke cikine yasa iyayen sa tsare shi a d’aki, ganin a koyaushe suna iya rasa shi, da gaf yake da jefa kansa a halaka, Umman sa ta zauna kusa dashi tana shafa kansa, Abban sa yana gefe a zaune, Abban sa ya kalle shi yace ” Son meke damunka ne, munyi munyi ka sanar damu damuwarka amma kak’i bayan kasan duk duniya babu wani mahaluk’i daya cancanci sanin matsalarka sama damu, ka sanar mana idan muna da abinda zamu taimaka maka zamuyi iya k’ok’arin mu dan ganin mun magance maka matsalarka, shiru yayi baice komai ba, a hankali Ummansa ta shiga lallashinsa, tana k’ara kwantar mishi da hankali had’i dayi mushi magiya akan ya sanar dasu damuwar shi, shiru yayi yana tuna sanda Fateeha take fad’a masa irin mugun son da take yiwa Khamal har ce mishi tayi idan ta rasa Khamal tasan rayuwarta bata da wani amfani bayan lokaci kad’an zata bar duniya.

Ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama tuna irin maganganun Fateeha akan haukan son da take yiwa Khamal, gashi kuma iyayen sa sun saka shi gaba akan sai ya sanar dasu damuwar shi, yasan kuma idan bai sanar dasu ba, ran su zai iya b’aci, ba kuma zasu jure ganin sa cikin wannan yanayin ba, suna iya shiga matsala, dan haka ya yanke shawarar sanar dasu, a hankali ya furta ” Fateeha ce damuwata, cikin zubar hawaye yake magana ” wallahi Abba ina mugun son ta, akanta zan iyayin komai, zan iya mutuwa saboda da ita wallahi Umma da in rasa ta gwamma na rasa komai ciki kuwa harda rayuwa ta, sosai yake kuka yana sambatu akan Fateeha wanda shi baima san yanayi ba, murmushi Abbansa yayi yace ” da akan wannan ka tsaya kana damun kanka?

“Karka damu kaji Son Dadyn ta ya dad’e dayi min maganar mu had’a ku aure nine nace kar muyi muku haka mu bare sai mun dai-daita kanku, da shi yaso ma tun kana Malaysia ayi auren, “Abba me yasa kak’i daka sani daka bari anyi, kanshi Umman shi ta shafa tace ” kwantar da hankalinka Son koyan zuma lokaci bai k’ure ba, ko gobe kake son a d’aura auren ku za’a d’aura, ” eh wallahi Umma na yarda a d’aura goben ma, maganar yake amma kwata-kwata baya cikin hayyacin sa, ” don Allah Umma ina nema na rasa ta, ta fara mugun son wani, nan ya kwashe komai dake tsakanin Khamal da Fateeha ya sanar dasu ” karka damu kaji Son wallahi koda zan k’arar da abinda na mallaka a duniya zan k’arar dan ganin farin cikin ka da walwalarka sun dawo, wallahi zanyi komai dan ganin ka mallake ta kaji Son, karka damu, maza tashi kaje kayi wanka kazo dining muna jiranka, ” please ku taimaka Abba, ” nace karka damu gobe iyanzu Fateeha tana a matsayin matarka kaji, ya mik’e ya shiga bathroom, suka bishi da kallo cike da tausayawa, Abba ya kalli Umma yace ” wallahi bazan tab’a bari nayi asarar tilon d’a na ba, ko kisa ne ya kama nayi zanyi, saboda farin cikin sa………

MOMYN ZARAH
[21/01, 04:12] ‪+234 701 517 2910‬: GADAR ZARE!!!

(IT’S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)

      ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

GARGAD’I

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES , SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDU

13

Da mamaki Umman Ja’afar ke Abban tace ” Alhaji komai fa kace? “Eh kamar yadda kikaji nace komai to ina nufin komai, cikin sanyin jiki tace ” Allah ya kyauta, a fusace yace ” Amin ya fita, da daddare Abba ya shirya, ya kalli Umma dake zaune a gefe yace ” zani wajen Alhaji Nasir kan maganar yaran nan, ” Allah yasa a dace tace, ” zama a dace, ya fice, kasancewar tun da rana ya sanar da Dadyn Fateeha zuwan sa, hakan ne yasa Dady sanin da zuwan nasa, dan haka bai fita ko’ina ba ya tsaya jiran abokin nasa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button