
A harajar gidan Abba yayi parking, waya ya ciro daga aljihu ya kira Alhaji Nasir ya sanar dashi zuwansa, fuskarsa cike da fara’a ya fito tarbar abikin nasa, juna suka rungume cike da murnar ganin juna, a falo suka zauna, bayan sun gama gaisawa ne Abba ya sanar da Alhaji Nasir dalilin zuwansa, cikin farin ciki Alhaji Nadir yace ” Alhamdulillah dama na dad’e ina da burin ganin mun had’a yaran mu auren, Allah ya sani ina da mafarkin hakan a raina, in sha Allah babu wata matsala, na amince na yarda na bawa Ja’afar auren ‘yata Fateeha, ai ko bani kai mai d’aurawa Fateeha aure ne da wanda kaga dama.
Shima Abba cikin murna yace ” to Alhamdulillah dama nasan baza’a samu wata matsala ba, amma gaskiya kar abin yaja lokaci nan da sati biyu ayi bikin kawai mu huta, ” badamuwa in sha Allah, cikin fargaba Abba yace ” wani hanzari ba gudu ba, ” to lafiya cewar Alhaji nasir, ” eh to lafiya sai dai ba lau ba, ” ya kayi Alhaji Nasir ya kum tambayar sa, ” shi Ja’afar ya sanar da ni cewar akwai wanda yake zuwa wajen ita Fateeha.
Shiru Alhaji Nasir yayi sai can kuma yace ” kai gaskiya ban sani ba, amma zan bincika naji koma meye, tattaunawa suka k’arayi daga basani sukayiwa juna sallama har bakin mota Dady ya rako Abba, sannan Abba yaja motarsa ya tafi, cike da murna Dady ya nufi wajen Momy, a zaune ya iske ta ita kad’ai a falonta, kusa da ita ya zauna ya fara sanar da ita dalilin zuwan Abba,ya kuma shaida mata har sun yanke rana nan da 2weeks, shiru tayi bata ce komai ba, sai kuma ya k’ara da cewa ” amma shi Ja’afar yace kamar akwai mai zuwa wajenta ko?
Shiru ta kuma yi tana d’an nazari sai daga basani tace ” nima dai bani da tabbas amma ina tsammanin haka, ” kamar ya baki da tabbas kuma kina tsammani a matsayinki na uwa, wacce kike zaune waje d’aya da ita, ke ya kamata kefi kowa sani, hakkin kine kula da lamuranta, shiru dai tayi bata ce komai ba, haka ya gama zuba masifarsa ya tashi ya tafi, da kallo kawai ta bishi dan inda sabo ta saba da halinsa.
Washe gari da yamma lik’is Khamal ya sauke Fateeha a k’ofar gidan su, Dady na sama yana kallon su, sai suka kusan 1hr a tsaye suna hira cikin so da k’aunar junansu sai dariya suke, kowa ya gansu a haka yasan akwai mugun soyayya a wajen ba k’arya, sallama Khamal yayi mata ya tafi ita kuma ta shiga gida, bayan tayi wanka tayi sallah, ta falo dan wata muguwar yunwa take ji, Momy ta hango zaune a dining ita da Dady nufar wajen tayi ta zaune bayan tayi sallama ta gaida iyayen nata.
Fuska babu yabo babu fallasa Dady ya amsa mata, itako Momy fuska a sake ta amsa mata, abincin suke ci babu mai yiwa wani magana, sai da ya kammala ya mik’e, ya kalli Fateeha yace ” idan kin gama ina son maga dake, ya wuce bai jira amsata ba.
Kallon Momy tayi tace ” lafiya Mom, naga Dady ya canja duk ya zama wani iri? ” hmmm nima ban sani ba idan kinje kyaji, sama-sama ta gama cin abincin, d’akinta ta nufa kasancewar an kira sallar magrib, sai da kammal komai sannan ta nufi saman Dadyn, da sallama a bakin ta ta shiga d’akin, kansa nakan jarida bai d’ago ya kalle ta ba yace ” kira min Momyn ki, ” to ta tace, ta mik’e ta tafi kiran Momyn tare suka shigo, kusa da Momy Fateeha ta zauna.
Kallonta yayi yace ” waye wannan wanda naganku d’azu tare? , murmushi tayi tace ” sunansa Khamal, “d’an ina ne, kuma su waye iyayen sa, sannan meye alak’arku dashi? babu wani tsoro ko fargaba a tare da ita tace ” a unguwar rimi yake, sannan a school d’in yake, amma shi ya gama, service ma zashi, amma ban san su waye iayens ba, ido ya k’ura mata yace ” nace meye alak’arku? shiru tayi nad’an wani lokaci, a hankali ta furta soyayya muke, ” kina sanshi? ba tare da wani b’ata lokaci ba tace ” eh Dady.
” Momynki bata fad’a miki na dad’e dayi miki miji ba? ” what! ta fad’a a razane, cikin tashin hankali tace ” miji Dady? ” Eh na dad’e da bawa Ja’afar ke, “wanne Ja’afar d’in ta fad’a ciki razana, ” Ja’afar dai wanda kika sani, jiya ma Abbansa yazo muka saka ranar auren ku nan da 2 weeks, wani mahaukacin kuka tasa tace ” wallahi Dady bana san shi, Khamal nake so, Khamal ne rayuwa ta idan kuka raba ni Khamal wallahi Dady mutuwa zanyi, shine rayuwa , shi kad’ai nake so, wallahi da in auri Ja’afar gwara na mutu ba aure, Khamal ne…….. wata mahaukaciyar tsawa ya daka mata yace ” ke kin isa ince ga abinda zakiyi kice a’a, wallahi ko kin k’i ko kin so Ja’afar ne mijinki, sai dai ki mutu, cikin kuka tace ” to wallahi Dady kuna gaf da sarani, dan wallahi sai dai ya auri gawata, wasu mahaukatan marika ya zuba mata, wallahi sai dai ki mutu, kuka ta k’ara fashewa dashi tayi waje da gudu, sai da Momy ta tabbatar Fateeha ta tafi sannan ta mik’e ta kalli Dady tace.
“Zan iya jurar komai amma banda bazan iya jure tauyewa Fateeha hakkin ta, duk wani hali naka na jure shi shekara da shekaru, amma akan wannan wallahi duk inda za’aje sai dai aje, shi akan farin cikin d’an yake komai amma kai ka zab’i musmugunawa rayuwar tilon ‘yarka akan farin cikin d’an wani, tsawa ya dakawa Momy ya kalle ta ido cikin ido idonja sun canja zuwa ha, ya nuna mata hannu yace ” wallahi kome zakuyi sai dai kuyi, amma nagama yanke hukunci, yayi shigewarsa d’aki.
Tana komawa d’aki ta shige ta rufe k’ofa, ta fad’a gado ta saki sabin kuka mai cin rai,Abban Ja’afar kuwa yana komawa gida, ya sanar da Ja’afar da Umman sa, ihu Ja’afar ya saka ya daka uban tsalle ya rungume Abban yana yi masa godiya, yayi d’aki da gudu ya fad’a kan bed, yana murna da farin ciki, ya rungume filo yata sak’e-sak’e yana sakin murmushi.
Khamal na komawa gida ya iske mummunan tashin hankali, dan Hamza ne yake ta suma had’i da aman jini guda, yana sandarewa kamar zai mutu, cikin Firgici ya k’arasa inda Hajiya ta rungume Hamza tana ta faman kuka, yana ganin Khamal ya saki kuka ya kalle shi yace ” Yaya tace bata so na, wai tana da wanda take so kuka shi zata aura, wai shine rayuwarta, wallahi Yaya idan ban same ta ba mutuwa zanyi, rayuwata tana cikin had’ari Yaya, ita ce rayuwata, itace farin ciki na, ya k’arasa maganar yana mik’awa Khamal hannu yayin da bakinsa keta bulbulal da jini guda guda.
Kuka sosai Khamal ya saka ya rasa meke yi mai dad’i a rayuwarsa, baiyi magana ba ya sangumi Hamza yayi asibiti dashi a hanya ma sosai Hamza ke kuka yana sambatu, shima Khamal kukan yake har ya k’arasa dashi hospital, da saurki aka karb’e shi aka shigar dashi emergency, a k’ofar emergency room d’in Khamal ya tsaya sai zarya yake yana zubar hawaye, sai da akayi 1hr sannan Dr ya fito.
Kallon Khamal yayi yace ” muje office, a hanzarce yabi yabansa, bayan sun shiga ya nunawa Khamal wajen zama yace ” bismillah, zama yayi jiki ba kwari, kallon sa Dr yayi yace ” gaskiya rayuwar Hamza tana cikin matsala dan zuciyarsa tayi mugun tab’owa, yana cikin matsanciyar damuwa, ya kamata ku kula dashi sosai, amma zai kwana biyu anan idan komai ya dai-daita zamu sallame shi, ga wad’annan magungunan ka siya, bayan ya siyo maganin ne ya dawo d’akin da aka kwantar da Hamza, ya iske shi yana bacci da alama allurar bacci sukayi masa.
Kiran Fateeha yayi ya shaida mata halin da ciki, muryarta yaji kamar tana kuka, a hankali yace ” my heart lafiya? ” daurewa tayi ta k’ak’aro murmushin karfin hali kamar yana kallonta tace ” lafiya lau my life, d’an hira sukayi tace masa zatayi sallah, bayan ya kashe wayar ne tabi wayar da kallo ta saki sabon kuka.