GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Bayan kwana biyu
Sosai gidan Alhaji Nasir ya shiga mummunan tashin hankali, dan kwata-kwata Momy ta fita harkarsa bata sakar mishi fuska, haka ma a b’angaren Fateeha kullum tana d’aki bata fitowa kullum tana d’aki tana aikin kuka, tun Alhaji Nasir baya damuwa har abin ya fara damunsa ganin gidan sa na shirin rugujewa, dan haka ya kira Fateeha da Momy yace su sameshi a samansa.

Sa sallama suka shiga, guri d’aya suka zauna, kallon d’aya yayi musu ya gauda kai ganin duk sun fita hayyacin su musamman Fateeha tayi muguwar rama, bayan sun zauna yayi gyaran murya ya kalle ta yace ” duk akan Khamal ne wannan abun yake faruwa? shiru sukayi babu wanda ya bashi amsa, ya kalli Fateeha yace ” kice masa gobe yazo ina san magana dashi, “to kawai tace, ya kalle ta yace ” tashi kije, tare suka mik’e har Momy ita tana shirin fita, da sauri yace ” Zainab banda ke, cak ta tsaya, sai da Fateeha ta fita sannan ya taso da kansa ya rungume ta, ta baya ya shiga aikin lallashi.

Khamal kuwa bayan kwana biyun da Dr yace za’a sallame su aka sallame su, Alhamdulillah za’a ce don jiki yayi sauk’i saboda sosai Khamal yake kwantar mishi da hankali, yana k’ara masa k’arfin gwiwa akan in sha Allah zai taimaka masa dan ganin ya sami abin k’aunar sa, bayan sun dawo da Magrib Fateeha ta kira shi take shaida masa kiran da Dady yake masa.

Sosai sukayi waya cike da so da k’aunar junansu yayin da kowannen su yake ji idan duniya zata tashi bazai iya rabuwa da d’ayan ba, duk irin son da sukeyiwa junan su, Hamza ya sani dan duk abinda ya faru a tsakanin su yana sanar dashi, wani lokacin ma a gaban sa suke waya har yasa hand free, dan haka Hamza yasan mugun son da Khamal ke yiwa Fateeha.

Washe gari da misalin k’arfen 8:00pm na dare Khamal ya shirya cikin wani yadi mai bala’in kyau ya nufi gidan su Fateeha, ita ce tayi mishi iso wajen Dady, bayan sun gama gaisawa ne, ya kalli Fateeha yace ” bamu waje, ba musu ta mik’e ta fita, kallon sa Dady yace ” waye kai? cikin ladabi Khamal yace ” sunana Khamal Ahmad, muna zaune ne a unguwar rimi, mu biyu iyayen mu suka haifa, cikin kallon wulak’anci Dady ya kalle shi yace ” su waye iyayen na ka? Murmushi Khamal yayi yace ” Maraya ne ni tun muna yara iyayen mu suka rasu, a hannun kakar mu muka taso.

“Ok, kana aiki ne, ko kuma karatu kake? ” eh to, nagama karatu service ma zan tafi, amma bana wani aiki ko sana’a, a fusace Dady yace ” idan na fahimce ka kana nufin kai zauna gari banza, baka da aikin yi ko sana’a amma a haka kake tunnin zan d’auki ‘yata in baka, kana zaman banza a gari, kana zauna a matsayin zauna gari banza, kai kan ka har yanzu ba’a yaye ka ba, kakarka ita keyi maka komai ciki kuwa harda acikin ci dazaka ci, da sururar daza ka saka, sai dai kabi wannan kango yau, gobe kabi wannan majalisar, kaima ci da kai ake, cikin sanyin jiki Khamal yace ” ba wannan ne abin dafi muhimmanci ba, abinda yafi mahimmanci wanne irin farin farin ciki zan bawa Fateeha a rayuwarta, wacce irin kulawa zan bata, amma in sha Allah zanyi k’orari na neman aiki, tsawa Dady ya daka masa ya balbale shi da bala’i ya zage yayi tayi masa masifa da yana gaya masa bak’ak’en maganganu, masu k’ona zuciya, daga k’arshe yace masa ” get out of house nonsense, fuska cike da hawaye Khamal ya fita zuciyarsa kamar zata tsaga k’irjinsa ya fito, idonsa yayi ja, bibbiyu yake gani dakyar yakai kansa gida, don ko takan Fateeha baibi ba…………..

MOMYN ZARAH
[21/01, 04:12] ‪+234 701 517 2910‬: GADAR ZARE!!!

(IT’S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)

      ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

GARGAD’I

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES , SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO

14

A falo yayi zaman dirshan yasa kuka kamar wani k’aramin yaro, sautin kukan sa Hajiya da Hamza suka ji suka fito, ” subhanallahi Yaya lafiya meke faruwa? jajayen idonsa ya d’ago ya zubawa Hajiya da Hamza ya kasa koda furta kalma d’aya, sosai hankalin Hamza yayi mugun tashi, Hajiya tayiwa Khamal tambayar duniya amma yak’i magana sai faman aikin kuka yake.

Hakan ne yasa Hamza fashewa da matsanancin kuka, cikin kuka yace ” Yaya duk duniya bamu da kowa daya wuce mu ukun nan, mu kad’ai mu kad’ai muka mallaki junan mu, Yaya idan baka fad’a mana damuwarka ba wazaka sanarwa, Yaya please ka sanar damu matsalarka tun kan mu shiga fiye da damuwarka.

Kallon Hamza Khamal yayi, cikin kuka yace ” Bro wai yau ni ake kira da cima zaune, k’aton banza, wanda har yanzu ba’a yaye shi ba, ya k’ara fashewa da wani kuka yace ” wai bani da aikin yi sai yawon majalisa,.
nine zauna gari banza, yadda yake kukan ne ya bawa Hajiya tausayi itama ta fashe da kuka ta rungume shi tana tambayarsa waya jefe shi da wad’annan bak’ak’en maganganun, cikin kuka ya sanar da Hajiya da Hamza duk abinda ya faru tsakaninsa da Dadyn Fateeha, bai b’oye musu komai ba, cikin kuka Hamza ya rungume Hajiya da Khamal, yace ” Yaya kayi hak’uri in sha Allah wata rana sai labari.

” Nasani Bro, Khamal ya fad’a yana gogewa Hamza da Hajiya hawayensu, sosai su Hamza suka lallashi Khamal, sai da suka kwantar mishi da hankali sosai, har suka saka shi dariya, cikin barkwanci Hamza ya mik’e yace ” Yaya banci abince ba kai nake jira ka dawo ka bani a baki, nace Hajiya ta bani tace wai nayi girma, shine na bari ka dawo ka bani dan nasan Yaya na bazaice nayi girma ba ko?

Dariya Khamal yace ” ah ina ni ina cewa Bro yayi girma ai da kaina ma zan d’anko na baka abakin, ya fad’a yana shirin mik’ewa, da sauri Hmaza ya mik’e yace ” a’a Yaya ni zan d’auko kuma na baka a biki, Hajiya na kallonsu tana dariya, a baki Hamza ya rink’a bawa Khamal abincin har ya k’oshi, haka suke tun suna yara, duk wanda yayi fushi to ranar a baki za’a bashi abinci, gidan ya taso cikin farin ciki da walwala.

Fateeha kuwa da taji ne yasata komawa part Dady, bata iske kowa ba a falon, dan haka da sauri ta koma d’akinta dan ta kira Khamal a waya, ta kira shi ya kai sau 30 amma bai d’aga ba, iyakar tashi hankalin Fateeha ta tashiga sosai, don tasan tabbas ba lafiya,ba hankalinta duk yak’i kwanciya, gabanta sai fad’uwa, yake .
Allah .
Allah kawai take gari ya waye, dan ko bacci ta kasa.

Washe gari kowa a falo ya iske Fateeha tana ta faman jiran fitowar Dady, dan ko kayan jikin ta bata canja ba, duk wanda ya ganta yasan bata cikin nutsuwarta, kwana tayi tana kiran Khamal amma yak’i picking, zama ma gagarar ta yayi ta mik’e tana ta kai kawo a falo, tana cikin hakan taji motsin saukkowar Dady, ido ta k’urawa step d’in, Dady yana d’ora idonsa akan Fateeha ya murtuke fuska wai dan kar tayi masa maganar Khamal.

Sosai ya b’ata rai, a dining table ya zauna ko kallon inda take bayyi ba, ga mamakinsa ko zama bai k’ara yi ba, balle akai ga cin abinci, bata ko gaidashi ba cikin murya mai rauni yaji tace ” Dady ya kukayi da Khamal ne please?

Face ya k’ara b’atawa yayi kamar baiji abinda tace ba, hankali kwance yake break fast d’insa, duk abinda ke faruwa Momy tana gani kuma tanaji, sai da ya kammala komai ya mik’e zai fita ta kuma cewa ” Dady please I need to knew what is going on btwn you an him, kallonta yayi face ba walwala yace ” nayi mishi tambayoyi kamar yadda ya kowanne uba yake yi, amma ni ban gamsu dashi ba dan bashi da Qualities d’in da zan iya bashi auren ‘yata, dan gaskiya banza iya bawa marar sana’a, zauna gari banza wanda shi kansa har yanzu d’aukar nauyinsa ake a gidan su auren ‘ya ta ba, dan bazan sai da akuya ta dawo tana cimin danga ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button