GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Hannu Fateeha ta d’ora a kai ta kurma uban ihu ta zube a wajen sumammiya, k’afa Dady yasa ya tsallake ta ya fice, a gigice Momy tayo kanta tana kuka, jijjiga ta tashiga yi amma shiru, da gudun maseefa ta nufi fridge ta d’auko ruwan sanyi ta zuba mata, ajiyar zuciya mai k’arfi Fateeha ta sauke, a hankali ta bud’e idonta ta zuba su akan Momy dake faman kuka.

Dady na fita ya kira Abban Ja’afar ya sanar dashi duk abinda ya faru tun daga zuwan Khamal har zuwa yanzu da Fateeha ta suma, dariya Abba yayi yace ” kaima kayi wauta, daka sani ka kyale su, da mu kuma sai mu b’ullo masa ta inda bai tab’a tsammani ba, amma duk da haka ka kyale ni dashi zan b’atar dashi b’at, kar ka kuma yi musu maganar, ” to kawai Dady yace had’i da kashe wayar.

Tun bayan faruwa al’amarin nan Khamal bai k’ara d’agawa Fateeha waya ba, tayi kiran harta gaji text kuwa a rana sai tayi masa sau 20 a rana amma ba reply babu irin hak’urin da bata bashi ba amma shi,kwata kwata ko ajikinshi dan haka duk ta sukurkurce ta fita daga hayyacinta kwata-kwata ma ta daina fitowa daga bedroom d’inta ta daina shiga harkar kowa, kullum tana d’aki tana ta aikin kuka, ganin haka yasa Momy zuwa d’akin ta same ta, a kwance ta iske ta tana kuka, cikin sanyin jiki ta k’ara kusa da ita ta zauna, ” Fateeha Momy ta kira sunanta, “na’am ta amsa amma bata jiyo ba, hannu Momy tasa ta jawo ta jikinta, ta rungume,ta aiko tana jin Momy ta saki wani rin kuka mai sauti da taba zuciya.

A hankali Momy ta shiga shafa bayanta, tace ” kiyi hak’uri Fateeha matuk’ar ina raye bazan tab’a bari a aura miki wanda baki so ba , in sha Allah Khamal ne mijinki, shi zaki aura koda kuwa zan rasa raina, rungume Momy Fateeha ta k’arayi cikin kuka tace ” please Momy ki taimake ni, wallahi shi kad’ai nake so, idan na rasa shi mutu zanyi Momy, bana san Ja’afar, ” karki damu kinji Fateeha.

Da dare Dady da kansa yazo ya sanar da Momy ta kira masa Fateeha ga Ja’afar nan yazo yana san ganinta, ko kallon inda yake batayi ta balle ta bashi amsa, yakai 10mnts a tsaye a kanta yana yi mata magana amma ko ta nuna tasan ma yana wajen batayi ba, d’akin Fateeha ya nufa da kansa, kuka ya iske ta tanayi, bai kalle ta back yace ” ki je falon k’asa Ja’afar na jiranki, kuma na baki 5 mnt ki fito, ” wallahi babu inda Fateeha zata fita, yaji sautin muryar Momy na magana a bayan sa, a fusace ya juyo, amma yana kallonta yayi shiru dan tunda yake da ita bai tab’a tsananin fushi a tare da ita irin yau ba,
ido cikin ido Momy take kallansa tace ” Nasiru tunda mukayi aure ban tab’ayi maka musu kona bijerewa umarninka ba, amma tabbas akan maganar Fateeha ina gaf da rabuwa dakai, dan wallahi matuk’ar kace zaka aura mata wanda bata so zama na dakai yazo k’arshe.

Kallon ta kawai yake da mamaki dan a iya saninsa ko had’a ido dashi Zainab bata iyawa ba, balle harta gaya masa bak’ar magana, taci gaba da cewa ” shi akan farin cikin d’ansa da kuma kwanciyar hankalin iyalinsa yake komai, amma kai ka rufe ido, ta wuce ta kama hannun Fateeha suka fita daga d’akin suka barshi.

Da gudu Hamza ya biyo Khamal, sosai Khamal da Hamza ke guje-guje acikin gidan tun daga falo har d’aki da tsakar gida, Hajiya na kallonsu tana dariya, dan ta riga ta saba da halinsu tun suna yara haka suke kuma har yanzu basu daina, Ba wani lokacin sai Khamal yayi nisa da waya da Fateeha Hamza ya zagayo ta bayansa ya warce wayar ya zuba da gudu haka zasuyita zagaye gidan da falon, hannun Hamza Khamal ya kama suka fita waje suna dariya, haka dai suke rayuwar su cikin farin ciki, da kwanciyar hankali.

Babu yadda Fateeha batayi dan su had’o da Khamal ba amma yak’i, ko school d’in ma ya daina shiga tunda dama ya gama dan ita kawai yake shiga, da wuri Fateeha ta shirya tayiwa Momy sallama, ta tafi school, direct department d’insu ta wuce,.
tasha wuya matuk’a kafin ta samu wanda ya san gidan, ta lallab’eshi akan ya raka ta gidan, har k’ofar gidan ya kaita sannan ya juya, da sallama a bakinta ta shiga, gidan babu kowa sai Hajiya, har k’asa ta durk’usa ta gaida Hajiya, da fara’a a fuskar Hajiya ta amsa dukda bata santa ba, Bayan Hajiya ta kaita falo, ta kawo mata ruwa, a hankali Fateeha ta kalli Hajiya tace ” Mama kece Maman Khamal dan Fateeha bata tab’a sanin Khamal maraya bane, murmushi Hajiya tayi sannan tace ” yarinya ban gane ki ba, sunkuyar da kai Fateeha tayi tace ” Fateeha ce, sosai Hajiya tayi mamaki tace ” Fateehar Khamal? Murmushi Fateeha tayi ta k’ara sunkuyar da kanta k’asa tana wasa da ‘yan yatsunta, sosai Fateeha taji dad’i a ranta yadda Hajiyar Khamal ta santa, ta k’ara tabbatarwa kanta Khamal yana santa, tunda gashi har a gidan su an santa.

Mamaki ne ya kama Hajiya ganin kyan Fateeha, kyakykyawa ce ajin farko kamar aljana, gata da kunya ga ladabi da hankali, sosai Hajiya taji ta kamu da k’aunar Fateeha, lokaci d’aya taji tana san had’a zuri’a da yarinyar, murmushi Hajiya tayi tace ” masha Allah sannunki da zuwa amaryata, amma yasan da zuwanki ne?

A hankali Fateeha ta d’ago idonta tace ” a’a, na rasa mai nayi mishi idan na kira shi baya d’agawa, dan Allah Mama idan ya sanar dake wani abu daya faru ki sanar dani please, Hajiya bata b’oye mata komai ba, ta sanar da Fateeha duk abinda Dady yayiwa Khamal, sosai Fateeha ta razana, tace ” Dady ne yayiwa Khamal haka? Hajiya ta k’ara da cewa ” Khamal maraya ne, bashi da uwa ko uba, su biyu iyayensu suka haifa, ni Kakar su ce ta wajen uba, ni na haifiyar Abban su, daga shi har k’aninsa babu wanda yasan dad’in iyaye, shi Khamal yana da 3yrs iyayen sa suka rasu, shi kuma Hamza yana da 1yrs, basu san kowa nasu ba sani.

Tausayi Khamal da Hamza suka ya kama Fateeha, kuka tasa sosai, kamar ranta zai fita take kuka tace ” Hajiya ban tab’a sanin Khamal maraya bane, bai tab’a sanar dani ba,dariya Khamal da Hamza suka jiyo, a tare suka shigo falon sai dariya suke, Hamza na ganin Fateeha yace ” Alhamdulillah, ya nufe ta gadan-gadan dan Fateeha ita ce wacce yake haukan so, Fateeha ce wacce Hamza yake so akanta ne ya kamu da ciwon zuciya, yana ganinta yayi tunanin ko Fateeha tazo amsar soyayyarsa ne, ya d’auka ko tazo amincewa dashi ne, dan haka da sauri ya nufe ta yana murmushi, itama Fateeha ta mik’e ta nufe su, shi Hamza a tunaninsa ko wajen sa ta nufo, itako Fateeha bata ma ta lura da wani Hamza ba, hawaye na zuba a idonta tana kuma murmushi ta kalli Khamal tace ” why why, mai yasa ka barni wannan hukuncin yayi min tsauri I love you, Hamza na hawayen farin ciki ya bud’i baki yace ” I lov……. kafin ya k’arasa yaji Khamal yace ” don’t ever say u love me Fateeha, I hate you I don’t want you in my life, just go, please live from my side, sandarewa Hamza yayi a wajen ya kasa kwakwaran motsi, cikin matsancin kuka tace ” wallahi Khamal ina sanka, kai ne rayuwata, bazan iya rayuwa babu kai ba, wallahi idan ka barni mutuwa zanyi.

” innalillahi wa’inna ilaihirraji’un kawai Hamza ke maimaitawa, wani iri juwa yake gani take idonsa suka fara ganin bibbiyu kuma dishi-dishi, numfashinsa ya d’auke,cak k’irjinsa ya fara bugawa da k’arfi, jiri ya fara d’ibansa, a hankali idonsa yake rufewa har ya dai na gani, d’if numfashinsa ya d’auke………….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button