
MOMYN ZARAH
[21/01, 04:12] +234 701 517 2910: GADAR ZARE!!!
(IT’S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)
~NA~
HAUWA A USMAN
JIDDARH
????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
GARGAD’I
MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES , SU KARANTA BA
~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDU
15
Da kyar da taimakon Allah Hamza ya samu ya fizgo numfashinsa, a hankali a hankali yake bud’e idonsa harya samu yayi controlling kansa, dan baya son koda wasa Khamal ya fuskanci akwai wani abu tsakanin sa da Fateeha, ya daure ya doje yayi kamar ba wani abu, amma acan k’ark’ashin zuciyar sa ji yake kamar ya mutu da sauri k’irjinsa ke bugawa, mak’ogwaron sa ya bushe bakinsa ya rinka yi masa d’aci.
Itako Fateeha bama tasan Allah yayi ruwansa ba, gaba d’aya hankalinta yana kan Khamal, kwata-kwata bata cikin nutsuwar ta, sosai ta matsa daf dashi ta yadda kowannen su yana iya jiyo numfashin juna cikin sanyin murya tace ” please Khamal karka barni, kai kanka kasan ina sanka, karka d’ora min laifin daba nawa ba, ya d’an matsa baya kad’an yana aika mata wani irin kallo, yace ” kinga please ki tafi gida, kai ta shiga girgiza masa cikin kuka tace ” a’a Khamal please karka barni, bazan iya jure rashin ka ba, wallahi idan ka barni mutuwa zanyi, ni kaina bansan ina yi maka wannan mugun son ba sai yanzu, Khamal kaine ruhi ne, idan ka barni tamkar ka tafi da rahi nane kabar gangar jiki na.
” Tunda nake ban tab’a yiwa iyaye na musu ko gardama na sai akanka duk abinda suka umarce bana yi musu gardama hakan ne ma yasa Dady ya yanke ranar aure na ba tare daya shawarce ni ba, cikin muguwar razana Khamal ya d’ago kai ka kalle ta, aiko karaf suka had’a ido, alama tayi masa da idonta na eh, taci gaba da cewa amma a kanka na kunya Dady na tubure nace a’a, akan ka nak’i yi masa biyayya, na bijire masa, yanzu haka Dady ko magana baya man, a kanka farin ciki da kwanciyar hanklin da iyaye na suka gina shekara da shekaru ke neman gujewa dan yanzu haka Momy da Dady neman rabuwa suke.
” Ashe duk tarin maganganun dakake fad’a min ba gaskiya, kasha fad’a min nice rauwarka, nice farin cikin ka, nice duniyarka, kace duk runtsi duk bazaka tab’a rabuwa da ni ba, Idan kasan baka sona mai yasa kace kana so, idan kasan bazaka iya rayuwa dani ba mai yasa ka koyamin yadda bazan iya rayuwa ba kai ba, idan kasan bazaka d’orewa so na ba mai yasa zaka koyar dani yadda zan soka, mai yasa Khamal mai yasa ta durk’usa a k’asa ta fashe da kula mai cin rai.
A matsayi na na mace mai kunya, daraja, k’ima, da Allah yayi min, na yarda jan aji na, na tako har gidan ku, amma duk da haka bazaka hak’ura ba, kai wanne irin mutum ne marar adalci wanda kansa kawai ya sani, baka damu da damuwar wani ba, taka damuwar kawai ka sani, wacce irin zuciya kake da ita mai kafiya marar yafiya.
Jikin Khamal yayi mugun yin sanyi, zuciyar sa ta harba da k’arfi, yayin da yake jin santa na k’ara ratsa ko’ina na jikinsa yana bin kowacce jijiya ta jikinsa yana bin jininsa, ya runtse idanunwa da gam, k’aunarta na fizgarsa zuwa gare ta.
Hamza ko zama yayi kamar ba mutum ya, ya sandare a waje d’aya, babu abinda zuciyar keyi sai bugawa, k’irjinsa nayi masa zafi, ji yake kamar ya mutu, dakyar yake iya controlling kansa, dan ji yake kamar zuciyar sa zata tsage, a gaban idon sa macen dayafi fiye da kowacce mace a duniya ke kukan son Yayar sa uwa d’aya uba d’aya, wanda duk duniya bashi da kamar sa, a hankali ya share siririn hawayen daya zubo masa.
Hajiya dake tsaye tana kallonsu, tausayin su ya cika mata zuciya, cikin sanyin jiki ta tako har inda Fateeha ke durkushe tana kuka, a hankali ta d’ago ta, takai ta kujera ta zauna ta shiga lallashinta had’i da bata hak’uri, a hankali Khamal ya tako ya durk’usa a gaban kujerar da Fateeha ke zaune, Hajiya ta shiga yi musu fad’a daga k’arshe ta zarce dayi musu nasiha, sosai nasihar Hajiya tayi tasiri a jikinsu, a hankali ya rik’o hannunwanta ya k’ura mata ido ya langwab’ar da kai yace ” am sorry my life, murmushi tayi ta kama kumatunsa tace ” bakai ne yace zaka iya rabuwa dani ba, ” dariya yayi yace ” wallahi pretending ne, ba gaskiya bane, dariya Hajiya tayi ta mik’e tace ” ja’irai.
Mik’ewa Khamal yayi ya rik’o hannun Hamza ya kawo shi gaban Fateeha yace ” my cweet ga brother na, mama da Baban mu d’aya, mu biyu iyayen mu suka haifa, Hajiya kuma grandpa d’inmu ce, ita ta rik’e mu tun bayan rasuwar iyayen mu, bamu san kowa na mu sai ita, ya kalli Hamza yace ” Bro ga my heart, sai lokacin Fateeha ta kula da Hamza aiko da k’arfi k’irjinta ya buga, cikin seconds ta shiga tension, da sauri Hamza yayi mata signs ya girgiza mata kai, alamar a’a, da sauri yace ” yau dai Allah yayi naga amaryar mu, ya kalli Khamal yace ” kai Yaya ka iya zab’e she is very beautiful, murmushi tayi tace ” nagode irin wannan kod’awar haka.
A dining Hajiya ta shirya musu abinci, suka ci, cikin raha da wasa da dariya kamar babu abinda ya faru, komai ya wuce an zama normal kamar babu abinda ya faru, da Fateeha zata tafi Hajiya ta had’a mata kayayyaki dakyar ta karb’a had’i dayi mata godiya, Khamal ya raka ta.
Washe gari har gida Hamza yaje wajen Fateeha bayan ta fito sun gaisa yace ” please Fateeha ki manta da batun soyayyar danazo miki da ita, a baya, saboda matuk’ar Khamal yasan kece wacce nake so ko sama da k’asa zata had’e Khamal baizai tab’a auren ki ba, nasan kece rayuwar Khamal shine tako rayuwar, shi kad’ai kike so, ke kad’ai yake so, nasan bazaku tab’a kasancewa cikin farin ciki da walwala ba matuk’ar bakwa tare, ina son Yaya na akan shi zan iya komai, murmushi tayi tace ” bakomai Hamza, gabansa ne ya fad’i dan yau ne rana ta farko da Fateeha ta fad’i sunansa, ji yayi kamar tafi kowa iya furta sunansa, murmushin yak’e yayi yace ” not Hamza bro, ok, murmushi tayi tace ” ok.
Kwata-kwata Khamal bashi da kwanciyar hankali burin shi kawai ya samu aiki, kullum acikin neman aiki yake dan ya sawa ranshi bazai tab’a k’ara taka gidan su Fateeha da niyyar neman auren ta ba har sai yana da abinyi, saboda yace koda zasu kai 10yrs a haka shida ita bazai tab’a auren ta sai yana da madagara.
Babu yadda Fateeha tabayi ba dan ganin ta shawo kan Dady amma ina ya riga yayi nisa, abun yaci tura, sakamakon zuga dayake samu daga wajen Abban Ja’afar domin ba k’aramin ingiza shi yake yi ba, kullum cikin zuga shi yake aka kar ya sake ya bawa Khamal auren tilon ‘yarsa ga mutumin da bashi da gobe, dan haka kullum abin k’ara kwab’ewa yake.
Dady da Abban Ja’afar ne zaune a falo suna tattaunawa yayinda da Abba sai k’ara zuga Dady yake, ya kalle shi yace ” ni dai ina k’ara baka shawara karka sake ka d’auki tilon ‘yarka ka bawa mutumin da yake zaman banza jobless, bawai dan Ja’afar d’ana bane, Fateeha bata dace da kowa ba sai Ja’afar shine kad’ai zai jiyar da ita dad’in dake cikin aure, shine zai bata farin ciki da kwanciyar hankali, saboda yafi kowa sanin darajarta kuma duk tsiya shi d’an uwanta ne, kaga kuwa ai ya bare, koba komai wannan had’in zai k’ara dank’on zumuncin mu, kasan wani abu? Abba ya tambayi Dady, kasa magana Dady yayi illa girgiza masa kanshi dayayi, murmushi Abba yayi yace ” matuk’ar Khamal bai rabu da Fateeha ba sai na b’atar dashi, kai idan ta kama ma na kashe zan iya kashe wallahi, a hankali zugar Abba ta rink’a tasiri a zuciyar Dady har yaji ya tsani Khamal fiye da komai da kowa.