
Bayan tafiyar Dady ne Abba ya shiga gida, Umman Ja’afar dake zaune tana jiyo hirar su hankalinta yayi mugun tashi, ta shiga mummunar damuwa, gabanta sai fad’uwa yake dan taji abinda Abba yace, a haka Abban ya shigo ya same ta, mik’ewa tayi cikin sanyin jiki, ta shiga yi nasiha , ” haba Abban Ja’afar, saboda tsabar san kai, wato naka d’an shine kad’ai d’a shi ba d’a bane, wannan wane irin zalunci ne, da rashin tausayi yarinyar nan tace batasan shi, ga wanda take so, shima fa d’a ne kamar naka, kuma shima iyayen sa suna sanshi kamar yanda kake son naka may be ma sunfi k son d’an su, yanzu Alhaji ashe zaka iyaye kisa, wata irin mahauciyar tsawa ya daka mata cikin fushi sai huci yake yace “bana son jin komai daga wannan banza bakin naki, shashasha kawai, banza lusarar mace, ke kin isa ki zaunar dani kina min wa’azi, ke kin isa ki fad’a min abinda ya kamata nayi, ok wato yadda baki sanshi baki damu da damuwar sa ba, nima so kike nayi watse dashi, wallahi badan akan ido kika haife shi da saina ce dan ba d’anki bane,dan haka na riga na gama yanke hukunci kawar da Khamal kowa ya huta ” Alhji dan ina fad’a maka gaskiya kake jifana da wad’an nan maganganun, kadai tuna da mutuwa, da ranar tsayuwa, hannu ya d’aga mata kawai saboda ya kasa magana sai hhuci yake tsabar bak’in ciki ya wuce.
Sannu a hankali rayuwa ke tafiya sabuwa suka dinka faruwa suna wucewa, cikin haka ne Khamal ya buga ball d’in k’asa, cikin sa’a da taimakon Ubangiji yaci ball d’in cikin k’ank’an lokaci Khamal ya farayin suna a Nigeria, cikin haka gwamnati ta zab’e a wanda zai jagoranci Nigeria, a worlds cup wanda a yi Saudia a garin Riyadh, aiko murna da farin ciki ba’a magana suman wajen Hajiya da Hamza.
Khamal da Fateeha kuwa sunfi kowa farin ciki dan gani suke nesa tazo kusa, soyayyar su kullum k’ara gaba ji suke kamar su had’eye juna, kullum k’ara shak’uwa suke sunan su, Khamal da Fateeha na tsaye a harabar gida su, sai zuba soyayya suke suna sakarwa juna k’ayataccen murmushi, da tattausan kallo, cike da k’aunar juna, duk wanda ya gansu a haka yasan ko ba’a tamaya ba akwai tsaftacciyar soyayya, Abba da Dady suka fito, cikin zafin rai Dady ya nufe su, da sauri Abba rik’o shi, yace ” mai yasa ka cika gagagwa ne, saura k’iris mu kai ga gaci, kai ka b’ata mana plan, ai na riga na gama shirya masa GADAR ZARE
Fateeha da Khamal zaune a Shagalin ku restaurant, Oder suka bayan ta abinci da drinks, murmushi d’auke a fuskar kowannensu, Khamal ya kafe ta da ido, iska ta hura masa tace ” yadai wannan kallo haka?
Dariya yayi yace ” ba dole ba kin san bana gajiya da kallonki, ko a cikin b’akin ciki nake idan na kallonki sai naji na zama freshman, murmushi kawai tayi, suna cin abincin suna hirar soyayya cike da tsantsar so, kowannen su ji yake idan duniya zata tashi bazasu iya rabuwa da junan su, shauk’in k’auna ke fizgar kowannen su, duk wanda ya kalle su yasan ba k’arya akwai true love, sai lumshe ido suke, Ja’afar dake zaune a gefe yana shan coffee, ya sauke idonsa a kansu.
Wani irin mugun kishi ne ya taso masa, zuciyar sa ta shiga bugawa da k’arfi, gabansa yayi muguwar fad’uwa, take yaji k’irjinsa na neman daina aiki, lokaci d’aya ya rud’e ya figa daga hayyacin sa, ya rasa abinda me masa dad’i a duniya, ya rink’a jin zuciyar sa kamar zata kama da wuta, idon shi ya rufe da sauri ya sake bud’ewa, ya sauke su a kansu, bai san sanda ya nufe su ba, yakai wajen 5mtn tsaye a kansu amma basu sani ba kasancewar sun da tafiya wata duniya, cikin zafin rai ya buga table din da suke zaune, a firgice suka mik’e suna kallonsa, wani wawan tsaki taja, ta watsa mishi kallan banza, ta kalli Khamal tace ” please have a set my life, don’t worry about him, a hasale Ja’afar yace ” dama baki daina bin wannan d’an iskan yaron ba, zauna gari banza jobless wanda shi kanshi bai iya ci da kanshi ba balle ke, murmushi Khamal yayi baice komai ba, cikin zafin rai Fateeha tace” wannan shine zab’in rai na, masoyayi na, burin zuciya ta, kai da kake da aikin yi bana sanka bazan kuma tab’a auren ka ta, wai kai wanne irin maye ne jarababbe, nace ban san ka, ko dole ne, ana soyayya dole ne?
Zuciyar Ja’afar ta k’ara yin zafi yaji kamar zai mutu, a harzuk’e yace ” dolenki ki aure ni Fateeha matuk’ar kina raye ina raye baki da wani miji daya wuce ni, ya kalli Khamal wanda shiru kawai yayi zuciyar sa sai tafasa take, yace ” kai kuma katon banza, matsiyaci zaman uwar me kakewa mutane anan, banza sakarai marar zuciya, uban yarinya yace bazai baka ‘yarsa ba, amma dayeke kai maye ne ka nace, ” dalla Malam rufewa mutane wannan k’azamin bakin naka, kai har zakayi maganar rashin zuciya, maye kawai wanda baison ciwon kansa ba, zuciyar Khamal ta k’ara hasala ganin yadda Fateeha ke ci masa mutunci akan Khamal, kuma yak’i tanka masa, ya kai hannu zai ci kwalar Khamal, cikin zafin nama Fateeha wacce bak’in ciki yayi mata katutu ta zabga masa zafafan mari,gaba d’aya hankalin jama’ar dake zaune yayo kansu, idonta yayi ja ta nuna masa hannu tace ” wallahi koda maza sun k’are babu abinda zanyi dakai, ta nuna masa hanyar fita tace ” get out from here, kad’an ya rage numfashin Ja’afar ya fizge tsabar firgicin daya shiga, lokaci ya d’auka yana kallanta da mamakinta, yace ” ni kika mara akan wannan jakin matsiyancin, a tsawace tace ” get out, da k’arfi babu wanda baiji ta ba, kai ya girgiza ya kalli Khamal yace ” zaga ni, murmushi Khamal yayi yace ” aini d’an gata ne, dan ina damai shigar min, kaga kuwa idan kana mayyi maka kai baka yi, tsaki Fateeha taja, ta rik’o hannun Khamal, sai da ta taka k’afar Ja’afar sunnan suka fice, suka bashi zuciyar sa kamar zata tarwatse.
Bayan kwana biyu zuciyar Ja’afar ta kasa akan abinda ya faru tsakanin shi da Fateeha, duk yadda yaso ya yakice ta daga zuciyar sa amma ya kasa, gashi idan ya kira ta a waya bata picking, babu abinda yake san gani kamar kyakykyawar fuskarta, ya rasa yadda zanyi, dan haka ya shirya a falo ya zauna kasancewar falon ba kowa, ya aika mai aikinsu ta kira amma fir tak’i zuwa, yayi aiken duniya tak’i zuwa, mik’ewa yayi cikin sanyin jiki zai tafi, Dady ne ya shigo falon ganin Ja’afar yasa shi sakin fara’a, da sauri Ja’afar ya nufe shi, ya gaida shi, ya kalle shi yace ” yau she kazo, ko har kun gama da Fateehar ne?
Murmushi Ja’afar yayi yace ” yanzu nazo ban iske kowa bane shiyasa zan tafi, Dady yace ” zauna bari na shiga ciki na turo maka ita, dad’i Ja’afar yaji dan ko bakomai ya ganta koda zaginsa zatayi, murmushi yayi had’e dayi masa godiya, a d’aki ya same ta yace ” kije falo Ja’afar yana jiranki kuma minti 2 na baki, idan ba haka ni da ke ne, ya juya, direct kitchen ta nusa, sob’on (zob’o) da Momy ta had’a ta d’auko, ta nufi inda yake zaune, sanye yake cikin farin boyel da gani sabo ne, tana zuwa bata yi wata-wata ba ta juye masa zob’on a jiki, da sauri ya mik’e yana kallonta ta kalle shi tace ” wai kai wanne irin maye ne marar zuciya, ko dai kare ya d’auke maka ne?
Shiru yayi kawai yana kallonta, karka k’ara zuwa gidan mu idan kuma ka sake ka k’ara dawowa wallahi sai nayi maka abinda yafi haka dan harka mutu bazaka manta ba, murmushi yayi yace ” ko k’in k’i ko kin so baki da wani miji daya wuce ni, kallon sa tayi shek’ek’e tace ” wallahi matuk’ar Khamal yana raye bazan tab’a auren ka ba, a hasale yace ” lalle kuwa Khamal zai mutu koda bai shiryawa mutuwar ba, lokacin barin sa duniya yayi, ke da kanki kikace idan baya raye zaki aure ne kinga kuwa dole ya mutu, ke da kanki kin jawo masa mutuwarsa kusa, bakin ki ya jawowa masoyinki mutuwarsa a kwana kusa daga yau daga wannan lokacin ki fara k’irga kwanakinsa na mutuwa, kin jawo masa bala’i sai saka shi kukan mutuwa, sai yayi tsere da mutuwar sa, sai na k’ulla masa GADAR ZARE, sai na ya tsani ratuwarsa, sai tsani duniya da abinda ke cikinta, wallahi hatta ke sai ya tsane ki Fateeha, kwalar rigar sa taci ta zaro idanuwa waje tace ” wallahi k’arya kake Ja’afar babu abinda zai same shi sai alkhairi, Allah yana tare da, kuma ka sani komai za’a Khamal bazai tab’a tsana ta ba, kamar yadda nima ko rayuwa ta za’a cire min bazan tab’a rabuwa dashi ba.