GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Sai wajen k’arfe 3:30 na k’asar Saudia su Khamal suka sauka a babban birnin Saudia Riyadh, jirginsu na sauka suka ga dubban jama’a masu taryansu, ba k’aramin dad’i Khamal yaji ba, take yaji hawaye na k’ok’arin zubo masa, jami’an tsaro sai gadin su suke direct hanyar fita suka nufa, duk suka bi layi a inda ake caje kaya kafin kasamu damar shiga k’asa, duk aka gama caje kayan kowa lafiya, amma me ana bod’e jakar Khamal akaci karo da KOKEN babu komai acikin jakar face kayan maye, mamaki ne ya cika mai duba kayan, dan ya tabbatar wa da idonsa gaskiyar abinda yake gani, ya mik’e da sauri cikin rawar jiki, da gudu balaraben ya zagayo ya zazzage kayan Khamal a k’asa, yana zazzage kayan yaga KOKEN fal, aiko da k’arfi yace ” arrest him!

Kafin Khamal yayi magana dubbun jami’an tsaro sun zagaye shi da bundigogi, cikin tsoro da firgici da mugun tashin hankali yace ” wat!!! Koken kuma a kaya na, kafin ka k’ara maganar yaji wayar sa na ringing, cikin firgice ya d’auki wayar, wata mahauciyar dariya Khamal yaji an tinture da ita, cikin rawar murya Khamal yace ” waye kai?

” Gaggawar me kake yi hakan ne d’an uwana, ai dan nasar dakai na kira ka, nine HAMZA D’AN UWANKA tab!!!!! ai tashin hankalin da Khamal ya shiga yafi na koyaushe, cikin rawar murya yace ” why Bro why, sai kuma ya fashe da mahaukacin kuka shima Hamza kukan yake yace ” Yaya tun muna yara kake kwace duk abinda nake da burin mallaka, ka fini sa’a Yaya duk wani abu da nake da burin zama ko mallakarsa sai naga kai kake samu Yaya, tun ina da k’arami nake da burin yin suna a duniya sai gashi tun kafin aje ko’ina Yaya kai kayi sunan, ni ko a unguwar mu babu wanda ya sanni, haka a b’angaren karatu ina so ace nake yin 1st position, sai gashi kai keyi, haka da muka zo University nan ma kayi min zarra, bani da wani burin dayafi na karanci Medicine, amma nan ma na fad’i kai ka samu, sai kuma uwa uba FATEEHA, wacce itace macen dana fi a duniya itace nake hauka akanta, a kanta na kamu da ciwon zuciya, itace komai nawa, farin ciki, jin dad’i kwanciyar hankali na duk suna tattare da ita, amma itama sai gashi a kanta kayi min fintin kau, bata ko san kallo na, kai take so bayan ita d’in rayuwa tace.

Kasan meye next target d’ina? shiru Khamal yayi bayyi magana ” hmmmmm Hamza yace sannan yace ” zan KASHE HAJIYA dan ita kad’ai ce matsalata a yanzu, bayan nan bani da wata sauran matsala, dan nasan hanyar da zanbi wajen mallakar FATEEHA.

” nasan kai yanzu taka ta k’are, kasan meye hukuncinka? Khamal dai ba baka sai kunne, ya zama mutum mutumi kawai, murmushi Hamza yayi yace ” hukuncin kisa ne a kanka, dan ina da tabbacin bazaka tab’a barin Saudia da ranka, domin k’asa ce ta musulci da musulmai masu hulunci da Quran, da Hadith, wad’anda basu kai ka laifi ba bama an yanke musu hukuncin kisa bare kai, da aka kama da laifin safarar muyagun kwayoyi, kaga yanzu bani da sauran mak’iyi balle ciwon kai na gama da matsaloli na, dan Fateeha tasan ta yadda zan biyo mata, sai wata rana d’an uwana sai mun had’u a next world

Wata mahaukaciyar k’ara Khamal yasaka had’i buga wayar da bango ta tarwatse, ya tsugunta ya d’ora hannu aka yana kurma ihu yana kukan mutuwa kamar ransa zai fita………

MOMYN ZARA
[21/01, 04:12] ‪+234 701 517 2910‬: GADAR ZARE!!!

(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS)

       ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

GARGAD’I

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA ‘YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO

17

D’aya daga cikin ‘yan sandan ne ya danna wata ‘yar k’ararrawa, ba’afi 2 minutes ba saiga dan dazon motocin police sun zo wajen, kama Khamal sukayi suka danna shi cikin mota, sai da sukayi tafiya takai ta 8hrs sannan suka k’araso Shimesi prison, baban gidan yarin dake k’asar saudiyya kenan, nan aka kai Khamal wanda duk wanda ya aikata babban laifi can ake kaishi.

Sosai Khamal ke kukan mutuwa yana ihu kamar ransa zai fita, yace ” haba bros bai kamata kayi min haka ba, bai kamata ka nemi hallaka ni akan mace ba, kai d’an uwana ne na jini, kai kad’ai gare ni, duk duniya bani da kowa sama da kai idan dan Fateeha ce meyasa baka sanar dani ba?

” me yasa baka sanar dani itace wacce kake so ba?

“haba my only blood bros, why Hamza?

ya k’ara fashewa da wani irin mahaukacin kuka mai cin rai da tab’a zuciya.

Hamza ko cikin farin ciki ya kashe wayar ya juya fuskarsa d’auke da murmushi, yana juyawa yayi arba da Hajiya wacce tunda ya fara waya da Khamal take tsaye akanshi tana sauraran sa, babu abinda jikinta keyi sai kerrma, gumi ya gama jik’a mata duk ilarin jiki, kamar wacce akayiwa wanka da ruwa, cikin tsoro da firgice take nuna Hamza da yatsan hannunta bakin ta na rawa tace ” Ham…za Ham..za.. kai ne kuwa?

” Kai ne ka yiwa d’an uwan ka uwa d’aya uba d’aya haka, Hamza meka fara sha, ?

“mai ya sameka, meke damun Rayuwarka akan mace Hamza?
, kai ta fara girgizawa cikin tashin hankali tana “‘ a’a wannan bakai bane Hamza , bakaine ainahin Hamza na ba.
, “Hamzan dana sani na rik’a da hannuna jikana ba haka yake ba, murmushi yayi ya tako a hankali har gabanta ya tsaya ya zuba mata ido kana yace ” Ok kinji abinda nace kenan?
, cikin tsawa yace ” amma duk da kinji kika tsaya a gaba na kina yimin tamboyin banza da wofi tare da surutan iska cikin kuka Hajiya ta rufe shi da duka tace ” Allah ya isa tsakani na dakai, bazan tab’a yafe maka ba, dan ba irin wannan tarbiyyar na baka ba.

Dariya yayi yace ” da kinji nace ki yafe min ne, Hajiya tace” kaci amanar mu Hamza, ka yaudare mu, ka munafurce mu, kai mugu ne mai fuska biyu mai mugun nufi a zuciyarsa, azzalumi, in sha Allahu amanar mu daka ci bata ta tab’a barinka ka rayu cikin farin ciki da kwanciyar hankali ba.
“kuma alfarmar Ubangiji ko Khamal yana raye ko baya raye baza ka tab’a mallakar Fateeha ba, matuk’ar ina raye in sha Allah bazan tab’a bari Fateeha ta zama matarka ba.

A zuciye Hamza yayo kanta ya shak’e mata wuya yana gurnani yace” aiko lalle zaki mutu, kinyi ganganci Hajiya, dan duk wanda ya nemi yimin katanga wajen cikar buri na, to zan kawar dashi, daga doron k’asa batare da shakka ko tsoro ba.
Hajiya ta shiga haure-haure da shure-shure tana kokuwa da Hamza amma ina, bai sake ta ba sai da yaga ta daina motsi da numfashi alamar rai ya fita.

Gaba d’aya Idonta duk sun firfito waje,sunyi tulu tulu alamun shan wahala numfashin ta ya d’auke, ya wurgar da ita gefe, ya tsugunna a gabanta yana dariyar mugunta yace ” sai ki hana ni mallakarta, shima yana hanyar biyo ki, gawarta ya d’auka yakai kan gadonta ya kwantar da ita, ya ja mata bargo ya lullub’e ta kamar mai bacci, shi kuma ya nufi d’akisa ya kwanta yana tunanin abinyi.

Cikin 2hrs labarin Khamal ya bazu a ko’ina a cikin kasashen duniya duk tashar daka kunna zancen akeyi, Aljazira, BBC, CNN, da sauran tashoshi, aiko nan da nan labarin ya cika Nigeria, Dadyn Fateeha na zaune a falo Abba ya kira shi yace ” su kunna BBC ba musu Dady ya sauko falon k’asa inda Fateeha da Momy ke zaune suna hira, a hankali ya d’auki remote ya kunna TV, aiko pic d’in Khamal ya bayyana a jikin plasma, da sauri Fateeha ta mik’e tsaye jikinta na rawa ganin an rubuta Breaking news, (Nigerian baller he is an criminal ) live aka shiga nuna sanda aka kama koken a kayansa, har zuwa inda aka kai shi prison, wata mahaukaciyar k’ara Fateeha tasa ta zube a k’asa sumammiya.
cikin firgici Dady da Momy suka yi kanta, da gudu Momy ta d’auko ruwa tashiga zuba amma babu alamar motsi, aiko da sauri Dady ya sungume ta yayi mota, da gudu Momy tabi bayansu, suna shiga hospital direct emergency aka wuce da ita, Doctors sun kai 5 a kanta amma a banza, sai da Fateeha tayi 10hrs a hospital sannan ta farfad’o tana ihu, da sauri Momy da Dady sukayi kanta cikin kuka tace ” wallahi Momy he is not criminal, k’arya suke yi masa sharri ne, nasan halinsa, bazai taba aika haka ba. …..ta fashe da wani irin mahaukacin kuka Momy ki taimake ni wlh sherri aka masa nasan Khamal d’ina bazai taba aikata mugun aiki irin wanna ba.
shafa kanta Momy ta shiga yi, tana rarrashinta, rungume Momy tayi tana sauke ajiyar zuciya, kusa da ita Dady ya zauna cikin sanyin jiki, jajayen idonta ta d’ago tana kallonsa tace” ka gani ko Dady?
Kaga abinda kaja ko, a sanadinka Khamal zai rasa rayuwarsa, mai yasa Dady, ta k’ara fashewa da wani sabon kuka, hawayen masu zafi ke tsiyayo mata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button