
Jikin Dady a matuk’ar sanyaye ya jawo ta jikinsa ya rungumeta yace ” kiyi hak’uri Mama na, ba laifi na bane k’addararsa ce haka, in sha Allah zai fito, cikin kuka tace” Dady kana ji fa, sunce kashe shi zasuyi, ” karki damu Mama na in sha Allah I will try my best, kinji, Momy dake zaune a gefe tana kallonsu hawayen tausayin tilon ‘yarta na zubo mata.
Umman Ja’afar ko tunda taji abinda ya faru hankalinta yak’i kwanciya dan har ga Allah su Abba Ja’afar take zargi,
cikin tashin hankali ta nufi d’akin Abba tana kai kanta zata shiga tajiyo hirar Abba da Ja’afar, cikin sanyin jiki Abba yace ” gaskiya na tausayawa yaron nan dan nasan bazai iya aikata irin wannan laifin ba, shima Ja’afar cikin sanyin jikin yace ” nima bana tunanin zai iya aikata haka, dan gaskiya yaron yana da hankali da nutsuwa ina ganin dai ya had’u ne kawai da sharrin mak’iya, Abba yace ” to sai dai mu taya shi da addu’a, Umma dake tsaye ta juya cikin mutuwar jiki.
Washe gari tunda sassafe Hamza ya fito k’ofar gida yana kukan mutuwa yana ihu da kururuwa yana d’ibar k’asa yana zubawa a jikinsa, mutane suka taru fal a kansa, suna tambayar shi lafiya, cikin kuka yace ” sakamakon abinda ya samu Khamal zuciyar Hajiya ta buga, harta mutu ma, aiko ‘ yan unguwa sun girgiza da jin mutuwar Hajiya dan sun san macece mai kyawawan halaye, sunyi kuma masifar tausayawa Hamza dan sun san bashi da kowa sai Khamal da Hajiya gashi kuma duk babu su, bayan anyiwa Hajiya wanka da sutura dakyar aka raba Hamza da gawarta dan bori ya hauyiwa jama’a baza’a fita daita ba yana kuka yana kari .
Kwanan Fateeha d’aya aka sallamo ta daga asibiti, tana dawowa ta shirya ta fita batare data bari kowa ya ganta ba, dan tasan idan aka ganta baza’a bari ta fita a halin da take ciki ba.
direct gidan su Khamal ta wuce, Fateeha na shiga ana k’ok’arin fitowa da gawar Hajiya Hamza nata ihu da birgima, ai Hmaza na ganin Fateeha ya k’ara fashewa da kuka yana birgima, ya tubure, a slow Fateeha ta k’arasa shiga idan,tsayawa kawai Fateeha tayi ta k’urawa Hamza ido.
Ido Hamza ya zuba mata yace ” Fateeha bani da kowa yanzu ba Yaya Khamal ga Hajiya ma ta tafi ta barni a dai-dai lokacin dana fi buk’atarta, sai lokacin Fateeha ta fahimci mai ke faruwa, durk’ushewa tayi a wajen ta shiga kuka kamar ranta zai fita, ba k’aramin tashi hankalin Hamza yayi ba ganin Fateeha na kuka, a hankali ya tsaida kukansa ya rarrafa zuwa gabanta, ya shiga lallashinta.
Dakyar Hamza ya shawo kanta tayi shiru, sai bayan magrib Hamza ya maida ita gida, had’i da k’ara bata hak’uri, bayan sati biyu da mutuwar Hajiya Hamza yayi sweeping sim card d’in Khamal, sai da ya dawo gida ya nutsu sannan ya turawa Fateeha text
Slm, ya kike ya gida hope kina lafiya, please my dear bana san ki sawa ranki damuwar komai, dan nasan zuwa yanzu kin samu labarin k’addarar data fad’a mana, ina mai bak’in cikin sanar dake cewa an yanke min hukuncin kisa, nan da 2weeks please don’t feel sad my heart, u know I really love you, please karki damarmin kanki, idan kika bari wani mummunan abu ya sameki akan wannan abunda daya faru, har abada bazan tab’a yafewa kaina ba, zamu rink’a exchanging text har zuwa nan da 2 weeks, amma banda waya saboda akwai risk
Yana gamawa ya turawa Fateeha,, Fateeha na kwance taji k’arar shigowar text, a hankali ta jawo wayar ta duba, kamar a mafarki taga number Khamal aiko da sauri ta mik’e, a gaggauce ta shiga karanta text d’in, tana gamawa ta fashe da wani iri kuka, jikinta na kirrma ta rubata mishi reply, haka Fateeha da Hamza suka dinga yin exchanging text tsakaninsu a zuwan Khamal ne.
Khamal ko a prison bashi da wani aiki saina kuka, da surutai ya zama kamar wani mahaukaci ko tab’abb’e, yayi bak’i ya rame, ya koma kamar ba shi ba, kullum yana cikin kuka, ranar Friday Khamal na zaune yana ta faman kuka, yaji an dafa shi ta baya a hankali Khamal ya jiyo, wani mutum ya gani wanda a k’alla zai kai 40yrs ba murmushi mutumin yayiwa Khamal yace ” ni sunana Ayuba,naga kana ta kuka ne kuma naji kana yin yaren hausa hakan ne ya tabbar min kai d’an Nigeria ne, ko?
Ko sake kallan inda Ayuba yake Khamal baiyi ba, saboda ji yake ya tsani komai da kowa a duniyar nan , Ayuba yayi maganar duniya amma Khamal yak’i amsa masa, dole tasa Ayuba ya hak’ura ya tafi, wajen k’arfe tara na dare Ayuba ya dawo wajen Khamal,dan tunda ya ganshi yaji tausayinsa ya shige shi, ganin sa yayi a dunk’ule a waje d’aya yana ta rawar sanyi, da sauri Ayuba ya k’arasa wajen yana “fadin Subhanallah lafiyar ka kuwa, kana neman kashe kanka a banza,?
Ayuba ya rik’o Khamal da sauri Khamal ya fizge hannunsa yace ” malam lafiya? dan Allah ka kyale ni,
“ka rabu dani ka barni da bala’in dayake damuna, murmushi Ayuba yayi yace ” Yaro ba’a wulak’anta mutum kaji kodan gaba, dan baka san darajar da Allah yayi masa ba, ka sani ni zan iya fitar dakai daga cikin wannan damuwar dakake ciki.
, ka sani ko hanyar fitarka daga cikin bala’in yana hannun na, bai kamata kayi haka ba, gashi dai da ganinka ka fito ne daga gidan tarbiyya da mutunci da bakayi kama da mutumin banza ba , ka tsaya na taimake ka, ya fad’a yana k’okarin rik’o hannun Khamal a karo na biyu.
Khamal bayyi k’ok’arin hana shi ba, saboda jikinsa daya mutu, Ayuba na tab’a Khamal yace ” Subhanallah ai bakama da lafiya, tashi muje hospital d’in dake cikin prison, ya fad’a yana jan hannun Khamal ba tare daya jira amsarsa ba, bayan sunje an gama duba Khamal aka bashi magunguna akayi masa allurai, Ayuba ya wuce dashi yayi wanka ya canja kaya sannan ya matsa mishi ya bashi abinci yaci dakyar dan sai da Ayuba yayi da gaske sannan Khamal yaci abincin yasha maganin.
Tun daga ranar Ayuba da Khamal suka zama abokai sosai, dan Ayuba sananne ne a prison babu wanda bai san shi ba, sosai Ayuba ke d’aukewa Khamal kewa da damuwa dan ya kasance mutum ne me barkwanci da wasa da dariya, sosai suka saba da juna, Khamal da Ayuba zaune bayan Khamal ya gama bashi labarin sa, dan sosai Ayuba ya matsawa Khamal akan sai ya bashi labarinsa, dakyar dai ya shawo kan Khamal ya bashi labarin, sosai Ayuba ya jinjina al’amarin, ya kuma tausayawa Khamal, amma fa Ayuba yayi bala’in tsorata da firgici.
daya ji laifin da akama Khamal dashi dan yasan idan duk duniya gatansa ne sai sun datse mishi kai.
Tsoratar da Ayuba yayi harta fito fili Khamal ya gane, Khamal yace ” ya naga duk ka tsorata haka? Yak’e Ayuba yayi yace ” bakomai yana k’ok’arin mik’ewa tsaye, murmushi Khamal yayi yana maida Ayuba zaune yace ” nasani kashe ni zasu yi, da sauri Ayuba ya d’ago kai kwalla na son zubo mishi, dariya Khamal yayi yace ” please karkayi min haka mana, karka karya min zuciya, duk wanda kaga ya mutu kwanansa ne suka k’are, idan idan da rabon shan ruwa a gaba zan sha, kaga ni gaya min naka labarin, Khamal yace dan ya kawar da wancan maganar.
Murmushi Ayuba yayi dan ya gane mai Khamal yake nufi, yace ” haifaffen garin Sokoto, zama ne ya kawo ni saudiyya ni da matata da yara na, ‘ yata wani labarabe ya sace yakai gidan sa sukayi ta cinta shida abokanan sa, harta mutu, sun zo yarda gawar tata ne wani Bahaushe ya gansu, ya d’auki number su, bayan kwanaki aka gane nine mahaifinta aka zo har gida aka sanar dani abinda ke faruwa munyi kuka sosai nida matata, nakai shi k’ara koto to kasan ni mazaunin k’asar ne kawai su kuma cikakkun ‘yan k’asa ne, dan haka akak’i yi musu komai bayan ga shaidu ga hujjoji amma aka danne gaskiya daga k’arshema aka ce sharri nayi musu, dan haka aka kaine gidan prison kasancewar bani da galihu, bayan nayi wata 3 na fito, bak’in ciki ya sani nabi shi ainahin wanda ya sace ya fara kaita gidan nasu, na kashe shi.