GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Na fito da kwana biyu na kashe shi dan haka zargi ya hau kai na, babu irin binciken da basuyi ba amma basu samu kwakwkwarar hujja ba, kasancewar zargi ne kawai yasa aka kawo ni nan aka ajiye ni yau 5yrs kenan, amma tuni iyalina sun koma gida Nigeria, ajiyar zuciya Khamal yayi yace ” tab kai kenan da Kake da hujja bare ni da aka kama k’uru-k’uru, Allah dai ya shige mana gana kawai zamu ce.

Fateeha da Hamza sai zabga soyayya ake ta text ita a tunaninta Khamal ne, ana gobe satin biyun da Hamza ya cewa Fateeha za’a tafi yanke mishi hukuncin kisa ya kira ta, ringing d’aya ta d’auka, sak irin muryar Khamal yayi yace ” hello my life kuka Fateeha ta fashe dashi yace ” haba my love ya zakiyi min haka, dakayar Hamza ya samu Fateeha ta yi magana saboda kukan dayaci k’arfinta,, sosai sukayi magana ya kwantar mata da hankali, ya rarrashe ta, daga k’arshe yace ” please dear ina neman wata alfarma a wajenki, cikin rawar murya tace ” fad’i koma meye nayi alk’awarin zanyi maka shi koma meye, sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan cikin matsanancin kuka yace ” please dear ki auri Hamza, dammm gabanta ya buga yashiga dukan uku uku kukanta ya tsaya cak yaci gaba da cewa Hajiya ta yaba da hankalinki da tunaninki, shiyasa take da burin had’a zuri’a dake.
pls my heart duk da bata raye muyi mata wannan alfarmar, sosai ya shiga rok’onta akan ta yarda ta auri Hamza, yace” wannan kad’ai zakiyi min na mutu cikin farin ciki,sannan km ruhina yasamu salama pls dear ki yarda ki auri d’an uwa na ni da shi duk d’aya ne, pls wannan kad’ai zakiyi min ki tabbatar min da kina so na, sai daya sha wuya sannan Fateeha ta amince, cikin kuka tace ” kayi magana dashi Hamzan?

“Eh na kira shi, nayi mishi bayani shima da farko k’in yarda yayi sai dakyar ya yarda yace amma naji ta bakinki tukunna, munyi dashi gobe zai kiraki sai kuyi magana, cikin kuka tace ” dan kai zan auri Hamza dan a soyayya akwai sadaukarwa, ta k’ara fashewa da kuka, ranar Fateeha tayi kukan da tunda tazo duniya bata tab’a yinshi ba, dakyar sukayi sallama.

Hamza kuwa ranar kasa bacci yayi dan murna, tunda daga ranar Hamza da Fateeha suka dai-dai ta kansu amma ita sama-sama take kula shi, dan harga Allah bata wani jin son Hamza a zuciyarta bata tab’a jin d’igon son shi, atare daita ba ita kanta ta rasa dalili kwata-kwata ta tsani ta ganta dashi a tsaye shi kuma gashi da naci tsiya , haka dai har magana takai gun iyaye sosai jikin Dady yayi sanyi yayi kuma danasanin abinda ya aikata da farko,.
dan haka babu wata-wata kawai ya amince, aka saka rana, amma Fateeha dole ce kawai ta sata yarda da Hamza, ba’a wani saka lokaci mai tsayi ba wata 1 kawai aka saka.

A kwana atashi ba wuya agurin Allah yau gashi har ana saura kwana 5 d’aurin auren Fateeha da Hamza, gidan Hajiya Hamza ya gyara dan anan zai ajiye Fateeha, sai shirye-shiryen biki ake ita ko Fateeha ko a kanta.

Khamal da Ayuba zaune suna hira, Ayuba ya kalli Khamal yace ” wai kai baka da kowa ne ban tab’a jin kace zakayi waya ba, da sauri Khamal ya d’ago idanunshi yana kallon Ayuba yace ” dama da waya anan ne, murmushi Ayuba yayi yace ” sosai ma, ai koni ina da ita sai dai matsalar bani da caja kuma ga ba caji, da sauri Khamal yace ” OMG amma shine baka tab’a gaya man ba, kaga ni duk ba wannan ba, yanzu ya za’ayi nayi magana, shiru Ayuba yayi yace ” ni dai tawa sai Friday, za’a kawo min caja, amma zo muje wajen wani abokina.

Ba tare da b’ata lokaci ba aka bawa Khamal waya, Ayuba ya kalle shi yace ” kayi wayarka ba damuwa idan ma kwana zakayi kana iyawa, take your time friend, number Fateeha ya fara kira, da kamar bazata d’aga ba, ganin number Saudi Arabia yasa ta saurin d’agawa, tace ” hello ido Khamal ya lumshe hawaye na zuba daga idonsa, murya can k’asan mak’ogwaro yace ” my heart gabanta ne yayi muguwar fad’uwa numfashinta ya nemi d’aukewa jikinta ya dauki rawa.. ……..

MOMYN ZARAH
[21/01, 04:12] ‪+234 701 517 2910‬: GADAR ZARE!!!

(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)

       ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????
(united we stand and succed our ambition is to entertain & motivate the mind of readers)

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation

GARGAD’I

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO

BEST FRIEND FOREVER & EVER
ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~

18

Numfashinta ya nemi d’aukewa cak… saboda rud’anin sautin muryar daya doki dodon kunneta cikin rawar murya ta bud’e bakinta dake rawa tace” my life kai ne?

Shima cikin rawar murya yace” eh nine my heart, ya kike, ya su Momy da Dady?
” duk muna lafiya, kai ya kake?
Murmushin k’arfin hali yayi yace ” Alhamdulillah, am sorry dear ban samu waya bane shiyasa kika ga ban kira ba sai yau, kuka ta fashe mishi dashi, da k’arfi Khamal ya runtse idonsa saboda bak’in cikin daya taso masa, babu abinda Khamal ya tsana kamar b’acin ran Fateeha, balle har yakai ga ta koka, sosai Fateeha ke kuka, cikin kuka tace ” am sorry ya dear bazan iya cika maka alk’awarin dana d’aukar maka ba , bana san sa, bazan iya auren sa ba, bana jin zan iya rayuwa da wani d’a namiji a matsayin miji in ba kai ba, kai kad’ai nake so, kai ne rayuwa ta, kaine duniyata wallahi na yarda zan jira ka komai tsayen lokacin, amma Allah bazan iya AUREN dan’uwanka HAMZA ba kamar yadda kace .

Da sauri ya bud’e idonsa dake rufe, gaban sa yayi masifar fad’uwa, kansa ya juye ya kasa fahimtar abinda Fateeha ke nufi, kalmarta ta k’arshe kawai yake maimaitawa bazan iya auren dan’uwanka Hamza ba to me hakan ke nufi?
, bai k’arasa tunanin dayake yi ba yaji tace” wai ni za’a d’aurawa aure nan da kwana 5 kuma bada kai ba, I cant my love, I can’t, am sorry, cikin rashin fahimta yace ” Fateeha ban gane mai kike nufi ba, ban fahimta ba kin sani a duhu, waye zaiyi auren nan da kwana 5?

Cak ta tsayar da kukanta ta cire wayar daga kunnenta ta k’urawa wayar ido, jin Khamal nata “hello hello yasa ta mayar da wayar kunnenta tace ” wai waye, bada Khamal nake waya bane?

“Eh nine mana my heart, please kiyi min bayani yadda zan gane ban fahimci zance ki ba, itama cikin rashin fahimta tace ” kamar ya baka gane abinda nake nufi ba, ba da kai muke exchanging text ta layinka na Nigeria ba? ” Eh bani bane ya akayi? “What!!? Fateeha tace da k’arfi, you means badai kai mukayi magana ba, ba kaine kace na auri Hamza ba?

Cikin firgici da matsanancin tashin hankali yace ” ni! yaushe? kinga please ki nutsu ki dawo cikin haiyacinki kiyi man bayani yadda zan gane, aiko Fateeha ta shiga bashi labarin duk abinda ya faru tun daga farko har k’arshe, daga k’arshe tace ” this coming Saturday za’a d’aura mana aure, tab tashin hankali wanda ba’a saka masa rana, nan take Khamal ya canja kamanni, idonsa sukayi ja, hankalinsa yayi mugun tashi, jikinsa ya d’auki rawa in bada huci babu abinda yake fitarwa, ita kanta Fateeha ta fahimci hakan dan tana jiyo hucinsa, ta cikin wayar .
Cikin rawar murya tace ” my life kana nufin duk wannan shirin Hamza ne?

Dakyar ya iya bud’e baki ya bata labarin abinda Hamza yayi masa, yace ” koken d’in da aka kamani da ita a kaya na shine shi ya saka min a kaya na, ya fad’a mata duk yadda sukayi da Hamza, kuka Fateeha ta fashe dashi, saboda mamaki itama kasa magana tayi, Khamal yace ” Fateeha, gabanta ne ya fad’i dan indai taji Khamal ya kira ta da real name d’inta ba lafiya ba, yaci gaba da cewa ” mai yasa zaki munafurce ni, mai yasa baki sanar dani gaskiyar abinda ke tsakaninki da Hamza ba? Cikin mamaki Fateeha tace ” kamar ya ban sanar dakai abinda ke tsakanin mu ba, me ke tsakani na dashi, koya ce maka akwai wani abu a tsananin mu ne?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button