GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Shiru Khamal yayi baice komai ba, taci gaba da cewa ni dai abinda na sani shine, yayi tayi min nacin yana so na, yasha zuwa gidan mu, yasha rok’ona akan na so shi, ni kuma na fad’a masa ina da wanda nake so, a lokacin ban san alak’ar dake tsakanin ku ba, bayan na sani kuma shine ya hanani na sanar maka, ta fad’a masa zuwan da Hamza yayi gidan su, da yadda sukayi, duk cikin matsanancin kuka Fateeha ke magana.

Ajiyar zuciya Khamal ya sauke da karfin gaske kana yace ” lalle Hamza ya cika makiri maci amanar dan’uwa , wallahi tunda nazo k’asarnan banyi magana da kowa ba, sai shi ranar daya kira ni ya sanar dani shine yasa min koken a kaya na, cikin tashin hankali Fateeha tace ” baka san ma Hajiya ta mutu ba kenan?

“What Khamal yace da k’arfi, ya fashe da wani irin mahaukacin kuka ya dunk’ule hannushi ya naushi bango da karfi yace shikenan ” ya kashe ta, ya kashe min ita dama yace sai ya kashe ta, Hamza ka cuce ni, wallahi kozan yafe maka komai banda jinin Hajiya , bazan tab’a yafe maka abinda kayiwa Hajiya ba, Allah ya isa tsakanin mu dakai, macuci, mugu, azzalumi, maci amana, mayaudari, mak’aryaci, ya k’ara fashewa da wani mahaukacin kuka, fisge wayar Ayuba yayi ya kashe, tuburan Khamal ya haukace agurin ya rink’a wani irin ihu yana hauka, ya fita daga hankalinsa, nutsuwarsa tabar jikinsa, Ayuba ya tusa shi gaba yana yi masa nasiha yana bashi shawarwari, har ya samu ya dawo cikin hayyacinsa.

Fateeha na ganin an kashe wayar, tayi wurgi da wayarta, ta fita da gudu a falo sukayi karo da Momy da Dady da sauri Momy ta rik’e ta ganin gaba d’aya bata cikin nutsuwarta, kuka Fateeha take tana sambatu, a hankali Momy ta zaunar da ita, ta d’auko ruwan sanyi tabata tasha, sai da ta bari tad’an nutsu sannan ta kalle tace ” mai ya faru? duk abinda ya faru tsakanin su da Khamal ta fad’awa Momy da Dady, sosai suka shiga cikin mummunan tashin hankali, Momy ta kalle shi tace ” please Alhaji kayi wani abu akai mana, ajiyar zuciyar Dady ya sauke yace” tunani nake ta inda zan fara ne.

Cikin kuka Fateeha ta zube a gaban Dadyn ta tace ” please Dady ka taimaka mana idan na rasa shi mutuwa zanyi please ta k’arashe maganar hawaye na bin fuskarta, cikin sanyin jiki ya kalli Fateeha yace ” karki damu in sha zanyi iya k’ok’arina.

Bayan kwana biyu Dady ya samu Fateeha har dakinta a gefen gadon ya zauna, ya kalle ta yace ” kin nunuwa Hamza akwai wani abu?
kai ta girgiza masa alamar a’a, ajiyar zuciya ya sauke yace ” yawwa gud girl, yanzu abinda za’ayi ki kira shi yazo gidan nan yau, dan nayi magana da commissioner of police, mun gama tsara komai, amma dole sai Hamza ya shigo hannu za’a iya fitar da Khamal, jikinta na kirma ta d’auki wayarta ta shiga kiran Hamza, bugu d’aya ya d’aga, sai da ta saita kanta sannan tayi k’asa da murya tace ” hello my love, kusan fad’uwa Hamza yayi kasancewar yau ne rana ta farko daya ji makamanciyar wannan kalmar daga wajen Fateeha, da sauri yace ” hello my everything, tace ” please ina san na ganka ne, cikin zumud’i yace ” yanzu ko sai anjima, ” ah yanzu mana cewar Fateeha, da sauri ya mik’e yana cewa “OK gani nan zuwa.

Da sauri Dady ya kira police d’in da suke magana yace ” sun gama tsara komai, dan yana hanya ” yes sir cewar police d’in, ya kalli Fateeha yace ” ki shigo dashi har parlor, ” to kawai tace, ba’afi 10 minutes ba Hamza ya kira ta yace ya k’ara so, yana k’ofar gida, umarni ta bashi daya shigo parlor aiko ba musu ya danna kai, fuskarta d’auke da murmushi ta fito.

Da sauri ya mik’e tsaye yana kallonta, ido ta k’ura masa, yayinda wutar tsanarsa ke k’ara ruruwa a zuciyar ta, ya bud’e baki zaiyi magana yaji kan bindika a kansa d’an sandan yace ” you are under arrest, kana motsawa zan fasa kanka da harsashi , suna cikin haka Dady ya shigo da ‘yan sanda sama da 20, ido ya k’urawa Fateeha dake tsaye hard’e da hannayenta duka a k’irji tana murmushi hawaye na zuba daga idonta, a hankali ta tako har zuwa gabansa, cikin muryar kuka tace ” kayi asara Hamza kaji kunyar duniya, ka rasa wanda zakayiwa haka sai d’an uwanka uwa d’aya uba d’aya, kallon ta yayi idonsa na zubar da hawaye yace ” duk abinda nayi a kanki ne Fateeha, nayi-nayi akan na bawa zuciya ta hak’uri akanki amma na kasa, i love you Fateeha kuma wallahi banyi danasanin abinda nayi ba, bak’in ciki na d’aya na rasa ki da zanyi, amma matuk’ar ina raye bazan tab’a bari wani ya mallakeki ba, duk wanda yayi k’ok’arin hakan sai na tsinke masa numfashinsa.

Murmushi Fateeha tayi tace ” ni kuma duk duniya babu wanda na tsana sama da kai, bana sanka, ba kuma zan tab’a sanka ba , i hate you, ta tofa masa yawo a fuska, lumshe ido yayi yace ” thanks my love, ganin yana b’ata musu lokaci ne yasa ‘yan sandan tusa k’eyarsa suka saka shi a mota suka tafi office dinsu dashi, Fateeha ta durk’ushe a wajen ta saki kuka mai cin rai.

Ba k’aramar wuya Hamza yasha ba amma yak’i yayi magana balle a samu abinda ake so, sosai ran wani d’an sanda ya b’aci, cikin zafin rai ya shiga cell d’in da Hamza ke ciki ya damk’o wuyansa ya rink’a jan shi a k’asa har d’akin shocking, sosai d’an sandan nan ya rink’a ganawa Hamza azaba, sai da yaji wuya na neman kashe shi sannan yace ” zanyi bayani, bayan an kyale shi ne kuma ya shiga raina musu hankali aiko a zuciye d’an sandan yaci gaba da gana masa azaba, wanda daga karshe aka saka shi cikin underground akayi masa me rad’a’di da muni wanda kusan duk wanda zakaga an sashi cikin underground laifinshi me girma ne sannan yasa taurin kai gurin rashin bada hadin kan bincike dakyar dai aka samu Hamza yayi bayani, Dady zaune a DPO office aka shigo da Hamza wanda gaba d’aya kamaninsa sun canja, Dady ya kalle shi yace ” waye kace ya baka koken?

Dakyar Hamza ke magana saboda wuyar dayaci yace ” abokinka Abban Ja’afar, k’irjin Dady ne ya buga da k’arfi, gaske cikin firgici yace ” what!!! wallahi k’arya kake sharri zaka yi masa, cikin k’arfin hali Hamza yace ” idan da wanda zanyiwa sharri ai bayanka yake, tunda kake dashi ka tab’a sanin ainahin sana’ar da yake yi?

Dammmmm!!! gaban Dady ya kuma fad’uwa, shiru yayi ya shiga tunani, shidai a iya saninsa bai san shi da wata sana’a data wuce business d’in kaya daga k’asashen waje zuwa Nigeria ba, Dady ya bud’e baki zayyi magana police yace ” karka damu Alhaji zamuyi bincike sosai dan ganin gsky ta bayyana, yanzu munsa aje a taho,dashi kafin ya gama rufe baki sai ga ‘yan sandan sun shigo da Abban Ja’afar, yana ta wani cika yana batsewa, murmushi d’an sanda yayi sannan ya sanar dashi zargin da ake yi masa.

Mik’ewa yayi tsaye yace ” maganar banza maganar wofi ma kenan, ni zaku rainawa hankali wallahi idan bakuyi wasa ba duk sai na ja muku asarar rasa aikin ku, murmushi DPO yayi ya kalle Abba ya nuna masa Hamza dake zaune a gefe yace ” kasan wannan? Abba yana ganin Hamza gabansa ya fad’i ya firgice ya shiga in’ina, ji yayi an dafa shi ta baya ya jiyo a firgice DPO ya gani tsaye a bayan sa yana yi masa murmushi, gumin dake zuba masa yasa hannu zai goge, da sauri DPO ya rik’e hannun ya mik’e masa tissue yace ” goge da wanna, DPO na tsaye yana kallansa sai daya gama yace ” zakayi mana bayani cikin dad’in rai ko sai nasa an tambaye ka,cikin tashin hankali cikin rawar murya yace ” ni fa ban san kome ba, “agame da abinda ake tuhumata akai ba, “ok DPO yace, yaran sa ya kira ya kalle su yace ” ku tambaye shi, ta yaren da zai fi fahimta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button