GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Murya saurayin ya d’aga yace ” please ku taimake ni, kuban aron 5mnt kawai dan girman Allah, kallon mai gadi Ammar yayi yace ” waye shi?

jikin Baba mai gadi na rawa yace ” wallahi ban san shi ba, amma yakai sati biyu kullum yana zuwa tun asuba har ku tashi daga office wai yana san ganin ku, ni dai na hanashi shiga.

Kallan kallo suka farayi a tsakanin su,sannan ahankali Fahad ya d’aga musu hannu alamar su kyale shi ya k’araso,s shigowa duk da Fahad ya bada umarnin a kyale shi ya shiga sai da security suka caje shi tsaf sannan, da gudu ya k’araso inda suke ya zube a gaban su, yace” dan girman Allah alfarma nake nema a wajenku.

Babu wanda yayi magana da ido kawai suke binshi, dashi yaci gaba da mgn muryarsa na rawa ” na had’a ku da girman Allah ku taimake ni, nayi hira da ku a gidan TV na, tsaki Abdul yaja yace ” u are fool, saurayin yace ” yes Sir, wallahi ogana nayiwa laifi yace idan ban nemo labarin dazai k’ayatar da al’umma da girgiza ZUCIYAR jama’a ba zai kore ni daga aiki, gaba d’aya suka juya suka nufi office, Khamal yace ” idan ya koreka kazo zamu baka aiki yayi maganar suna ci gaba da tafiya.

Saurayin yace ” no Sir tun ina yaro nake da burin zama cikkekken d’an jarida, mahaifiyata tasha fama da wahala matuk’a dan ganin cikar burina, please ku taimake ni, kada burina ya ruguje…yakarasa fadar Haka tamkar zai yi kuka sosai ya marairaice musu yana rokonsu .. please kodan k’anwata guda d’aya tak data rage min, idan aka korini gurin nan bansan yadda rayuwarta zata kasance ba. Ni kadai gareta duk duniya batada kowa sannan bazan iya jurar yin wani aiki ba byn wannan danake yi .nasha jin yadda tausayi da karamacinku yake Ga al’umar garin nan narokeku dan Allah Ku tallafawa rayuwarmu ni da kanwata nacigaba da aikin nan domin taimakawa rayuwar kanwata datayi min saura a duniya ….yakarasa mgnr hawaye nabin kuncinsa ..

Tun sanda kyakyawn saurayin nan ya fara mgn suka tsaya Cak gaba d’ayan su, suna kallonsa da jin wani irin tausayinsa dukan su suka k’urawa Naseer ido suna kallonsa , ga mamakin su.
sai sukaji Naseer yace ” kayi sanarwa ko ina, kace ranar Friday zuwa Sunday zamu bada labarin kana iya gaiyato ‘yan gidajen TV, radio, ku same mu a babban hall d’in 6’s STAR HOTEL, daga 12:00pm zuwa 4:00pm, yana kaiwa nan ya juya ahankali ya shige office dinsa sauran ‘yan uwansa suka take masa baya, suna shiga ciki gaba d’ayan su suka rungume juna cike da murna.

Sosai Abdul yake kuka dan gaba d’aya d’an jaridan ya tuna masa da baya.
, hankalin 6’s STARS gaba d’aya a tashe yake,da ganin yanayinsa dukkan su, kukan Abdul ya sasu kuka, sosai km ya taba ransu tare da karya, musu zuciyarsu .
ranar dai haka suka yini jikinsu a sanyaye Babu dad’i.

Koda kowannen su ya koma gida, haka matan su suka gansu sukuku, dan Abdul ko abinci kasa ci yayi.
ya rufe kanshi a d’akinsa yana ta faman aikin kuka,da tuno da rayuwarsa ta baya .
Bbu yadda Yasmeen batayi ba amma Sam yak’i yarda ya bud’e mata k’ofa, sai da tace idan bai bud’e ba zata kira ‘yan uwansa, da k’arfi cikin muryar kuka yace ” No please karki kira su zaki tada musu hankali zan bud’e miki, ” ok to bud’e, a hankali ya bud’e mata k’ofar, yadda ta ganshi ba k’aramin d’aga mata hankali yayi ba, cikin rawar murya tace ” waye ya tuna maka da bayanka?

Shiru kawai yayi ya kasa furta daidai da kalma daya jikinta a matukar sanyaye tarasa inda madaidaicin fridge dinsa yake ruwan me sanyi ta d’auko ta bashi yasha, sannan ta shiga aikin lallashi .

Duk gari jama’a an d’auka 6’s STARS zasu bada labarin su, duk inda ka duba sai maganar ake, makarantun boko dana islamiyya, majalissar yara da manya, kai harta tsofaffi, dai-dai da yara k’ana sai kaji suna maganar, kowa ya d’okanta ranar tazo, musamman samari da ‘yan mata, kowanne gidan TV ko radio maganar kawai akeyi.

FRIDAY 12:00PM

Kowanne ya taho da matar sa, da kuma yaran sa, dubbun jama’ar dake bakin get suka d’auki ihu da ganin motocin su, cikin takun isa da tak’ama mai cike sa izza suka fara takawa zuwa cikin hall din, kallon jama’ar da suka taru dan su sukayi take gaba d’ayan suka ji kwalla, a zuciyoyin su sukeyiwa Allah godiya abisa baiwar dayayi musu ta jama’a domin mutum rahama ne.

Bayan sun shiga cikin hall d’in mai d’auke da ‘yan jarida, gidan TV, radio, da sauran masu d’aukar labarai, dan an hana kowa shigowa hall d’in daga su sai ‘yan masu d’aukar labarai, da securities d’insu, Zaid ya kalli ‘yan jarida yace ” sun shirya, saurayin mai suna Al’amin yayi gyaran murya yace ” please Sir ko zaki bawa duniya labarin asalin had’uwar ku?

Murmushi Khamal yayi sannan ya fara magana…….

MOMYN ZARAH
[21/01, 04:11] ‪+234 701 517 2910‬: GADAR ZARE!!!

      ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????

بسم الله الرحمن الرحيم

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO

3

Filin wasan kwallon k’afa dake garin Holland cike yake tap da d’unbun jama’a, iri iri babu k’abilar bil Adama da babu, ciki wannan filli wasa wanda ya tattara kan bak’aken fata ‘yan Africa koma ince in Nigeria,da sauran kasashen duniya. ihun mutane daban daban dake zaune wajen ya cika filin wasan kwallon Yayinda wasu daga ‘cikin mutane gurin ke sanye rigar matches rike da flags suna Dagawa sama suna zabga matsanancin ihu alamun Yan team dinsu ne suka samu nasarar cinyewa..

Kyakykyawan saurayin dake gefe zaune ya b’ata rai, in banda tsaki babu abinda yake faman yi,cikin fushi ya cutsa laulausar tafin hannushi ‘cikin sumar kansa dake kama data Fulanin asali yana shafawa , cikin harshen Hausa yace ” aikin banza kawai sun b’atawa mutane lokaci a banza ashe babu abinda zasu iya.
” wani dake gefen zaune ya lalleshi fuska d’auke da murmushi yace ” Assalamu Alaikum, wanda ke zaune rai b’ace ya juyo ahankali ya tsurawa wanda keyi masa sallamar idanu yana kallonsa , had’i da amsa masa sallamar.

D’ayan yace ” naji kayi Hausa ne, shine nace bari nayi maka magana d’an uwa, murmushi yayi yace ” lalle ko, wani can daga gefe shima yayi dariya yace ” sannunku, nima naga ‘yan uwa, dariya sukayi su duka,uku d’ayan dake gefe ya taso ahankali cike da takun isa ya mik’a musu hannu yace ” am KHAMAL by name , dariya d’ayan yayi yace ” ni kuma NASEER, hannu shima d’ayan ya mik’o musu yace ” ni kuma ABDUL.

Take Kowanesu yagabatar da kansa, da dan’uwansa wani matsanancin ihun da aka kuma yi ne ya dawo da hanakalin su wajen filin wasan,sosai tsaki still NASEER ya kuma yi ya furzar da iska me zafi Daga bakinsa kana yace “aikin banza, aikin wofi ashe duk dakikai akatara anan dabasu iya koma kawai ana sa mutun bata lokacinsa .
dariya Khamal yayi tare da cewa ” haba ai Chelsea k’arshe ce wajen wasa,kwallon duniya Abdul yace ” haba dai Chelsea Malam.
kasan dai Amman idan ana maganar manya kwallon wasan duniya Barcelona ba’a mana ko itace kan gaba ?

Naseer dake zaune ya dan zamo kadan Daga kujerarsa yana me juyowa saitin da Abdul yake ya kalleshi yana lumshe idanunshi sannan yace ” Barcelona me? Suwaye ‘yan wasan ta?

Khamal yayi dariya yace “Barcelona cluv pleyers 1 stegen 2 segi roberto 3 pique 4 basquet 5 samul umtiti 6 ivan rikitic 7 usman denbelle 8 Philip coutinho 9 surez 10 leneal messi 11 jodi alba, kallansa Naseer yayi yace ” sannunka, gaskiya kai mayen kallon ball ne,na karshe amma ni nafison Real Madrid, saboda tana da manyan ‘yan wasa wayanda suke da kwarewa sosai akan fanin wasa .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button