GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Sai da Abba yaci mugun duka da bak’ar wahala sannan yayi bayanin komai kan cewa dama can sana’ar da yake yi kenan sama da 30yrs, kuma shine ya bawa Hamza koken ya sakawa Khamal a kayansa, jinjina kai DPO yayi yace ” dama can kasan Hamza ne?
“A’a ban san shi b cewar Abba, DOP ya sake kallansa yace ” yanzu tare kuke sana’ar? A’a wannan ne karo na farko dana sashi aiki, DPO yace ” ya akayi ka san shi?

Abba yace ” wata rana ne naje gidan Alhaji Nasiru naga Hamza da Fateeha tsaye naji yana rok’onta akan karta sanar da Yayansa abinda ke tsakanin ta dashi, daga yanayin kallon dayake mata nagane yana yi mata mugun so, tunda daga nan nasa aka nemo min yaran, ban wani sha wuya ba ya amince min akan zan bar masa Fateeha ya aura, amma ni a raina bari nayi sai ana gobe d’aurin auren shi da Fateeha zan sa a kashe shi, ni kuma na lallab’i Dadyn ta kan kar a fasa d’aurin auren gobe sai a d’aura da d’ana Ja’afar.

A firgice Hamza ya d’ago kai yana kallon Abba, shima Abban shi yake kallo yace ” eh Hamza niya ta kenan, to wai ma in banda abinka dan me nake san kawar da Khamal ai daman da Ja’afar ya mallaki Fateeha ne, tunda abin ya faru Hamza baiji nadama ba sai yau, jikinsa yayi sanyi idonsa ya fara zubar da hawaye cikin kuka ya kalli Abba yace ” ka cuce ni, ina zaune lafiya da d’an uwana da kakata kasa na tarwatsa mana farin cikin mu da kwanciyar hankalin mu, tsawa DPO ya daka musu, duk sukayi shiru, DPO ya kalli Dady yace tunda duk sun amsa laifin ku, gobe sai mu kai su Saudian Embassy dake nan Nigeria, “ok kawai Dady yace saboda tsabar mamakin Abba.

Jikin Dady a sanyaye ya zauna a kujerar dake kusa da Momy da Fateeha, da sauri Fateeha tace ” Dady ya ake ciki? Cikin sanyin jiki ya shiga basu labarin abunda ya faru, dukkan su suka shiga jimamin Abba, had’i da jinjina irin san kai irin nasa, tunda Umma da Ja’afar sukaji abinda Abba ya aikata hankalin su yayi masifar tashi fiye da tunani, dukda Umma ba wani dad’in zama take ji dashi ba.

Tunda Khamal yaji mutuwar Hajiya kwata-kwata yaji ya tsani duniya da abinda ke cikinta ya tsani Hamza fiye da komai da kowa dan da duk abinda Hamza yayi baiji ya tsane shi ba sai da ya kashe Hajiya, sosai Khamal ke kuka yana yiwa Hajiya addu’a, yayinda Ayuba yake ta faman k’ok’arin kwantar mishi da hankali.

Ranar Monday Commissioner of police ya mik’awa Saudian Embassy Hamza da Abba, akan yarjejeniyar zasu saki Khamal had’i da wanke shi a idon duniya, washe garin ranar da aka mik’a su za’a wuce dasu zuwa Saudia, ranar Umma da Ja’afar suka samu Abba a Air port, ba k’aramin kuka Umma take ba, shima Abba cikin kuka ya kalle su yace ” please ku yafe min, duk abinda nayi nayi ne domin ku dan ku kasance cikin farin ciki da wadata, cikin kuka Umma da Ja’afar suka rungume shi, dakyar aka raba su, suka rabu cike da bak’in, bayan sun isa k’asar saudia ne aka mik’awa gwamnatin k’asar su, tare da kwararan hujjoji, da sake kwakwkwaran bincike, sai da aka tabbatar da komai sannan aka yanke musu hukunci, shi Abba kasancewar ba’a kama shi da kayan maye a hannunsa ba, sannan ba’a k’asar saudiyya yake safarar muyagun kwayoyin sa ba, bai kuma tab’a aikatawa k’asar laifi ba, yadai bada koken ne kawai an saka a kayan wani dan haka suke tuhumar sa da laifin K’AZAFI, bai kuma wahalar da shara’a ba shiyasa suka yanke masa hukuncin 5yrs in prison had’i da horo mai tsanani bayan an datse masa hannu d’aya.

Shiko Hamza kasancewar shine wanda ya saka koken a kayan Khamal,shine wanda ya shigo musu da koken k’asar su, tunda shine yasa a kayan, kuma ya aikata kisan kai, duk da laifin wa k’asar sa yayiwa, sannan Khamal d’an uwan sane na jini, shiya suka yanke masa masa hukuncin LIFE IN PRISON, sannan za’a datse masa hannayen sa duka biyun, had’i da huro mai tsananin gaske, ba k’aramin kuka Hamza yayi ba, yayi kuka kamar ransa zai fita, yayi danasani da nadama, shiko Abba godiya yayi tayiwa Allah dayasa hukuncin sa yazo da sauk’i.

Khamal na zaune shida Ayuba yana ta faman sana’ar tashi ta kuka, wani d’an sanda yazo ya kira shi, bayan police d’in yabi, wani babban hall aka kai shi inda ya tarar da manyan mutu ne, da jami’an tsaro a kalla sun kai 50,umarni aka bashi daya zauna, bayan ya zauna ne aka fito dasu Hamza ganin Hamza yasa Khamal saurin mik’ewa, tsaye yana masa wani irin kallo me cike da tsantsar tashin hankali a gabansa Hamza ya zube yana rusa kuka yana rok’on Khamal yafiya, Khamal kansa ya d’aga sama hawaye nabin fuskarsa, Abba ma ya zube a gabansa yana bashi hak’uri a hankali Khamal ya sauke ajiyar zuciya yace ” kaga yadda Allah yake ikon sa ko? kai da a tunaninka kaci banza, ai Allah ba azzalumin sarki bane, Hamza kaban mamaki, sannan ka bani misali ta yadda bazan k’ara yadda da kowa ba koda kuwa ni da kai na ne, ka tsora tani, ka cuce mu, ka tarwatsa mana rayuwar farin cikin mu, kasa na tsani kaina Hamza.

” mai yasa ka aikata mana haka mai yasa? , kasa zamu rayu cikin k’unci da k’unar zuciya ka tsinke min walwalata ka rabani da duk wata annashuwa ta?
, to amma ni na yarda da k’addara mai kyau ko marar kyau, na yarda Allah ne yake tsarawa kowa rayuwarsa, shike aikata komai akan kowa a lokacin daya so, nasan haka Allah ya tsara mana, ni dai daga b’angare na na yafe maka duniya da lahira akan abinda kayi min, jinin Hajiya ne daka zubar bazan tab’a yafe maka ba, dan wallahi ko duniya zata tashi bazan tab’a iya yafe maka ruhin Hajiya ba duk ranar dana yafe maka jinin Hajiya bazan tab’a yafewa kai na ba, ya juya ya kalli Abba yace ” kai ne tushen faruwar komai, kai ka tarwatsa mana ahlin mu, ka ruguje mana gidan mu, kaje Allah ya isa abinda kayi mana Allah yayi maka kai ma, da sauri Abba ya rik’o k’ofar Khamal yace ” bazan yi maka musu ba, duk laifin daka d’ora min naji na k’arb’a, amma ka dubi girman Allah ka shafe min, jikin Khamal yayi sanyi ya kalli Abba yana goge kwallar dake zubo masa yace ” na yafe maka, babban jami’in dake wajen ne yayi gyaran murya, kowa yayi shiru ya fara magana da harshen turanci ” to dukkan mu dai mun san mai ya faru, dan haka mun saki Khamal sannan zamu wanke shi a ido duniya, bayan haka kuma gwamnati ta bashi kyautar 100 million naira, ido Khamal ya lumshe yana zubar da hawaye, a ransa yace ” Allah sarki Hajiya kin sha wahala akan mu, yanzu kuma ga dad’i yazo sai dai baki raye, Khamal na gani aka tusa k’eyar su Hamza suna kuka.

Shugaban wajen ya kalli Khamal yace ” idan kana da buk’atar wani abu ka fad’a, hawayen dake zubo masa ya k’ara gogewa yace ” alfarma d’aya nake nema a wajen ku, dan Allah ku taimaka ku duba cess d’in AYUBA kuyi masa adalci…….

NASO NA NAYI K’OK’ARI NA GAMA MUKU LABARIN KHAMAL A WANNAN PAGE D’IN , SABODA LABARIN ZAID, AMMA NAGAJI GASKIYA AMMA IN SHAALLAHU NEXT PAGE ZAMU GAMA

MOMYN ZARAH
[21/01, 04:13] ‪+234 701 517 2910‬: GADAR ZARE!!!

(IT’S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)

       ~NA~

HAUWA A USMAN
JIDDARH

????KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍????

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

GARGAD’I

MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA

~DEDICATED TO~
AISHA A BAGUDO

BEST FRIEND FOREVER & EVER
ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA
~(UMMU AMAN)~

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button