GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

19

Kallan sa jama’ar dake wajen sukayi cikin rashin fahimta, d’aya daga cikin jama’ar wajen ne yace ” bamu fahimta ba, waye kuma Ayuba, a ina yake, mai kuma ya faru dashi?

Labarin Ayuba Khamal ya basu tun daga farko har k’arshe amma bai sanar da su Ayuba ne yayi kisan kan ba, babban jami’in wajen ya kalli shugaban prison d’in yace ” ya akayi basu san da maganar nan ba balle zaman sa a prison har tsawon 5yrs, cikin in’ina yace ” kisan kai yayi, a zafafen ogan su yace ” ina hujjar cewa shine yayi kisan kan, idan kuna da gaskiya mai yasa baku shigar da cess d’in file ba?

Shugaban prison d’in yayi shiru da alamar rashin gaskiya, tsawa Ogan ya daka masa yace ” je ka kira min shi yanzu, ya maida kallan sa ga Khamal ya sassauta murya yace ” bama musan da maganar ba, in sha zamuyi iya k’ok’arin mu dan ganin anyi masa adalci, wani cikin mutanan dake wajen ya kalli Khamal yace ” dama can ka san shine?

“A’a anan na sanshi Khamal yace sannan ya shiga fad’a farkon had’uwar su, sun jinjinawa Khamal sosai da akan amana da rik’on alk’awarinsa, Ogan yace ” a gaskiya ka cika mutumin kwarai, mai dattako had’i da adalci, suna cikin haka aka shigo da Ayuba, tambayarsa Ogan yayi gaskiyar abinda ya faru, Ayuba ya zaiyane musu komai, amma bai sanar dasu shine wanda yayi kisan kan ba.

Ogan ya mayar da kallansa ga Khamal yace ” karka damu in sha Allah zamuyi iya yin mu, zamuyi bincike sosai dan ganin gaskiya ta bayyana idan kuma muka kasa gano hujjar komai bayan 1yr zamu sake shi tare da wanke a idon duniya, ajiyar zuciya Khamal yayi cike da farin ciki, Ogan ya juya ya kalli Ayuba yace ” ka rik’e Khamal dan aboki ne na kwarai, domin shine ya kawo cess d’inka gaban mu, kallan Khamal Ayuba yayi fuskarsa d’auke da hawaye yace ” nagode sosai abokina ko iya haka aka tsaya na yaba da halaccin dakayi min kuma har abada bazan tab’a manta alkhairin dakayi min ba nagode sosai Khamal ya k’arasa maganar yana mai fashewa da kuka.

Rungumo shi Khamal yayi yace ” karka damu in sha Allah zanyi iya yi dan gani kaima ka kub’uta kaci gaba da rayuwa da iyalinka kamar kowa, Ayuba ya bud’e baki zayyi magana Khamal yayi saurin rufe masa bakinsa da yatsansa yace ” tsakanin mu ba godiya, Ayuba na kuka sosai Khamal na kuka suka rabu cike da kewar juna.

Dubban ‘yan jarida Khamal ya tarar a waje suna zaman jiransa, yana fitowa sukayi kansa suna yi masa tambayoyi, labarin komai Khamal ya basu, sai dai bai sanar dasu cewa d’an uwansa ne yayi masa wannan GADAR ZARE ba dan gudun bakin jama’a karya fad’awa Hamza dan yasa idan ya fad’i Hamza d’an uwansa ne uwa d’aya uba d’aya zai sha tsiniwa da Allah wadai, duk tashar daka kunna hotan Khamal zaka gani dana commissioner of police suna kwararo bayani, tas Khamal ya wanku a idon duniya.

Ranar da Khamal zai dawo Nigeria,tun safe Fateeha ta shiga kitchen take ta faman girke-girke Momy na taya ta, sai suka gama kaf ta shiga bathroom tayi wanka ta tsala kwalliya, ta zama kamar Alana saboda kyau, Dady, Momy da Fateeha suka tafi Airport taryarsa, tun a jirgi commissioner of police yabawa Khamal labarin namijin k’ok’arin da Dady dan ganin ya kub’uta, ya sanar dashi komai, akan Dady ne yayi komai har aka kama Hamza da Abba,sosai jikin Khamal yayi mugun sanyi a ransa yace dama baka tab’a sanin masoyi na gaskiya sai abu ya sameka na farin ciki ko bak’in ciki.

Idan kaga dubbunnan jama’ar da sukaje taryar Khamal sai ka d’auka president ne zai dawo, jama’a ko’ina maza da mata, dan su Fateeha basu samu damar shiga ba, hawaye ne suka shiga zubowa Khamal dayaga irin jama’ar data zo tarbarsa, wani irin sanyi ya rink’a ji a jikinsa, ido ya shiga rabawa dan ganin ta inda tauraruwarsa zata b’ullo, aiko can ya hango ta tana ta d’aga mai hannu da sauri ya nufi inda take itama a guje ta nufo shi, tana zuwa ta fad’a jikinsa ta rungume shi ta saki kuka sama Khamal ya d’aga ta ya shiga juyi da ita.

A hankali ya sauke ta k’asa ya sake rungume ta yana sauke ajiyar zuciya take ya manta da duk halin daya shiga yaji wani farin ciki na ratsa shi tako’ina, ya tsinci kansa da zuciyar sa fess, idonsa ne ya sauka akan su Momy da Dady dake kallon su suna murmushi, da sauri ya saki Fateeha yace ” my heart ashe dasu Dady kika zo amma kika ja mana abin kunya?

Dariya tayi tace ” ni na ma manta dasu, ido ya zaro yace ” su Momyn kika manta, tace ” ba dole ba tunda ina tare da my life ta fad’a dai-dai lokacin dasuke k’arasawa wajen su Dady har k’asa Khamal ya durk’usa ya gaida su Dady, da fara’a suka amsa.

Bayan sunje gida sun ci abinci hankali ya kwanta, Khamal yayiwa Dady godiya sosai, dariya Dady yayi yace ” haba Khamal bakomai ai duk yiwa kai ne, kaima ka zama d’anmu yanzu, Momy tace ” kaje ka huta ka nutsu kayi bacci, ta kalli Fateeha tace ” kai shi d’aki ya kwanta, cikin nutsuwa Khamal yace ” a’a bakomai Momy zanje gida in yaso sai na dawo da daddare, dakyar suka yarda suka barshi ya tafi gida, ba k’aramin kuka Khamal yayi ba lokacin daya je gidan,yaga gidan yayi masa gida, sosai yayi kukan bak’in ciki da takaici, ya tuna irin rayuwar farin cikin da sukayi a gidan, ya tuna Hajiya, bayan sallar ishsha Khamal ya dawo gidan a parlor ya same dukkan su, bayan ya shiga ya zauna ne Momy tasa aka kawo masa abinci, amma fir yak’i ci, sai dakyar yaci kad’an shima sai Momy ta matsa masa, Dady ya kalle shi yace ” Khamal ranar asabar d’in nan mai zuwa nake san d’aura auren ku da Fateeha bana buk’atar komai daga wajen illa sadaki, sosai sukayi farin ciki, dan har sai da suka kasa b’oye farin cikin ya fito fili, Momy ta kalle su tace ” oh yaran yanzu baku da kunya, dariya sukayi gaba d’ayan su cike da farin ciki.

Ranar asabar da misalin 11:00am aka d’aura auren Fateeha da Khamal, babu yadda ba’ayi suyi biki ba, amma suka ce a’a saboda Hajiya batayi 40 ba, kasancewar Hamza ya riga ya gama gyaran gida yasa babu abinda Khamal ya k’ara yiwa gida, Dady cewa yayi babu wani ‘yan kai amarya, ya kira Khamal yace bayan sallar isha’i yazo ya d’auki matarsa, Khamal da Fateeha durk’ushe a gaban Momy da Dady suna ta yi musu nasiha mai ratsa jiki, sosai nasihar tayi tasiri a jikin su, daga k’arshe Dady ya sallame su, sai da Khamal ya tsaya yasai musu kaji da drinks da fresh milk, sannan suka wuce gidan su.

Bayan sunje had’add’en gidansu wanda sha kayaan alatu na more rayuwar duniya dan sosai Dady ya kashe kud’i wajen siyan kayan d’aki tsadaddu ga tilon ‘yar tasa, hannusu sark’afe da juna suka shiga falon, akan kujera ta zauna jikinta ba kwari, dan tasan hadda Khamal yake rawar kan nan ba kyale ta zayyi ba.

A hankali Khamal ya jawo ta jikinsa ya rungume, aiko tuni jikinta ya d’auki rawa, gabanta ya shiga dukan uku-uku, ganin yadda jikinta ke rawa ne yasa Khamal yin murmushi, a kunnan ya rad’a mata ” bari na shiga ciki nayi wanka, kema tashi Kije kiyi wankan, daga nan ki d’auro alwala, ba musu ta mik’e dan dama jira take ganin yadda duk ya narke mata a jiki, murmushi yayi shima ya mik’e ya nufi d’aya dak’in.

Sanye da jalabiyya a jikinsa ya shiga d’akinta, iske ta yayi ta shirya cikin doguwar riga, cike da fargaba ta shinfid’a musu prayer mate, suka gabatar da sallah raka biyu bayan sun idar ya dafa kanta ya shiga kwararo mata addu’oi a hankali ya mik’e ya nufi kitchen a plate ya zubo musu kaji da drinks d’in, dakyar Fateeha ta d’an dan gaba d’aya a tsorace take, cup ya cika da fresh milk ya mik’a mata ba musu ta karb’a ta shaye tas, kayan ya kwashe ya kai kitchen daga can yayi d’akinsa yana fita itama ta rage kayan jikinta ta saka wata fitinaniyar rigar bacci me shara shara wacce ta bayyana sirrin jikinta domin har kan nipple d’inta ana gani ta sake feshe jikinta da turaruka kala kala masu tsuma zuciya Khamal wanda shima ya gama shirinsa na bacci ya dawo dakin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button