GADAR ZARENOVELS

GADAR ZARE COMPLETE

GADAR ZARE COMPLETE HAUSA NOVEL

Duk tarin dukiyar nan da Allah yayi masa amma baya cikin nutsuwa dan Allah ya rage shi da abu d’aya shine rashin haihuwa sun kai 10yrs da aure da mahaifiyata amma ko b’ari bata tab’a yi ba, anyi neman maganin har an gaji, zan iya cewa yawancin k’asashen duniya sunje akan neman haihuwa amma ko ina maganar d’aya ce lafiyarsu lau Allah ne dai kawai bai kawo lokaci ba, mahaifina ya sha d’ibar malamai sama da 50 ya kai su Saudi Arabia dan su rok’a masa Allah ko Allah yasa a dace amma shiru.

Duk da wannan jarabawar da Allah yayi masa hakan baisa ya kauce ba, dan gaskiya Abba ya kasance mutum mai tsoran Allah, adali mai taimako, da jik’an talakawa, ya kasance cikekken malami makarancin Al’Qur’an yana da matuk’ar tausayi, dan yana da gidan marayu, islamiyoyi, bohol, da masallatai bazasu tab’a k’irguwa ba, kai duk inda kake neman mutum na Allah Abba na yakai, shiyasa mutake ke kiransa da GARKUWAR TALAKAWA, haka ma mahaifiyata wacce muke kira da Ammi ta kasance mace mai biyayya, hak’uri, sanin ya kamata da taimako, itama kamar Abba haka take shiyasa ake kiranta da UWAR MAKAYU.

Babu yadda mahaifiya ta batayi da Abba akan ya k’ara aure ko Allah zai sa a dace ba amma yak’i, a cewarsa komai na Allah ne, da haka suka yanke shawarar zuwa gidan marayu su d’auko d’a, Ammi ce tajewa Abba da wannan shawarar aiko da sauri ya amince, ranar Monday da safe suka shirya su biyu suka tafi gidan marayu, basu tafi da kowa kasancewar a sirrin ce suke son aiwatar da komai.

Bayan su Abba sun gama kwarorowa shugaban gidan marayun buk’atar su ne ya sauke ajiyar zuciya yace ” Alhaji dan yara akwai su amma matsalar d’aya ce babu sabuwar haihuwa kamar yadda kuke da buk’ata, Abba yace ” ok badamuwa ba lalle sai yanzu ba idan aka samu sai kay….. bai k’arasa ba sakoman wata mata data shigo da gudu ta zube a gaban shugaban gidan marayun tana haki tace ” ranka ya dad’e mahaukaciyar nan ta haihu an samu d’a namiji, sai dai tana cikin mawuyacin hali, da sauri suka mik’e har su Abba suka biyan matar.

Suna shiga d’akin suka iske matar rik’e da d’anta a hannu cikin jini tana ta fisge-fisge da sauri Ammi ta k’arasa inda take ta rungumo ta tana ta faman jera mata sannu dakyar matar ta d’aga kanta ta kalli Ammi ta mik’a mata yaron dake ta faman tsala kuka cikin rawar murya tace ” ga d’a na nan amana kiji tsoran Allah ki kular min dashi kamar d’an cikin ki, ki bashi ingantacciyar tarbiyya kamar ke kika haife shi duk abinda kikasan zakiyiwa d’anki kiyi masa, yunk’urawa tayi da niyyar ta tashi amma ta kasa, dakyar ta bud’e baki tace ” mu ‘yan asalin Yobe ne cikin garin Yoben, sunana Khadija mahaifin yaron nan sunansa Isma’il ta bud’e baki zata kuma yin magana amma ina Allah bai bata iko ba, taita salati har rai yayi halinsa, a hankali Ammi ta kwantar da ita a k’asa ta rungume yaran tana zubar da hawaye.

Jana’iza akayiwa matar aka kaita gidan ta na gaskiya shugaban gidan marayun ne ke gayawa su Ammi had’ari matar sukayi ita da mijinta shi mijin ya mutu tun a lokacin ita kuma matar ta haukace, su Abba sun jinjina al’amarin sosai, duk wasu ka’idoji da ake bi wajan karb’ar yaro daga gidan marayu sai da su Abba suka bi, an ciccike takardu sannan suka tafi da yaron su wanda suka sawa suna IBRAHIM suke kiransa da suna Abraham, bayan sati d’aya da karb’ar Abraham Ammi ta tashi da wani mugun zazzab’i dan har bata iya ko d’aga hannunta, Family Doctor Abba ya kira ya duba ta, ganin yanayin ciwon yasa shi zargin ko ciki ne da ita dan haka ya buk’aci fitsarinta, bayan Abba ya bashi fitsarin ne yace zaije lab yayi test zai dawo da daddare, gwajin farko Doctor ya gano Ammi na da shigar ciki harna tsawon wata bakwai, bayan sallar ishsha yaje gida a falo ya samu Abba cike da farin ciki Doctor ya mik’ewa Abba hannu yace” congratulations sir your wife is pregnant, da sauri Abba ya mik’e tsaye yace ” are you serious Doctor? Cikin fara’a Doctor yace ” kwarai kuwa harna 7 mnts ma, sujjada Abba yayi yana godewa Allah.

Fad’ar farin ciki wajen Ammi da Abba ma b’ata lokaci ne, kuka sosai sukayi aka rasa mai rarrashin wani a tsakanin su, Doctor kuwa yasha kyauta kala-kala, haka Abba ya rink’a haukan rabon duniya kamar a rijiya yake hak’owa, bayan wata biyu Ammi ta haihe ni, aka saka min sunan kakana Baban Abba na ZAHRADEEN ake kira na da ZAID, kunga Yaya na Abraham ya bani wata biyu kenan, dayake duk duniya babu wanda yasan maganar Abraham babu wanda ma yasan dashi har aka haife ni, dan haka Ammi da Abba suka shaidawa duniya mu ‘yan biyu ne, duk duniya babu wanda yasan mu ba ‘yan biyu bane balle har a san Abraham ba d’an Abba da Ammi bane ba, saboda sun riga sun gama tsara komai shiyasa cikin Ammi yana isa haihuwa Abba ya fitar da ita waje, a turai Ammi ta haihu shiyasa asiri ya k’ara rufuwa, ko mu kan mu ni da Abraham bamu san mu ba twins bane ba, gaba d’ayan mu Ammi ke shayar da mu.

Haka muka taso cikin gata, da so ga kulawar da muke samu, yayinda duk duniya ta shaida mu ‘yan biyu ne ciki kuwa harda kakannin mu, tun tasowar mu Allah yayi Abraham d’an k’arya ne, Allah ya sanya masa girman kai da wuk’anci kwata-kwata baya son talakwa shi k’amar su ma yake yake ji gashi da tsinannan san matan tsiya tun muna yara yake soyayya, gashi da son gayu dan Abraham d’an kwalisa ne kaya da turarurrukan sa, takalma, agoguna ma abin kallo ne dan shi komai sai mai tsada first class yake sawa, yayinda ni kuma kwata-kwata mata basa gaba na, haka ma kayan mai tsada da k’arya dan ni komai na samu sawa nake ba ruwa na, haka ma a b’angaren hali na iyaye na na d’ebo dan Allah ya sani bani da k’amar talakawa dan lokuta da dama sanda ina yaro cikin masu gadi da drivers d’in mu nake cin abinci, ga ni da taimako da tausayi, haukan ko bak’aramin soyayya ya k’ara jawo min a wajen iyayena da mutane ba.

Haka dai muka ci gaba da girma yayin da munanan halin Abraham na k’aruwa iskancin sa na k’ara kankama, ga shi da shaye-shaye da son zuwa club, yayinda da halin da Abraham ya saka rayuwarsa yayi mugun damun iyayen mu, sun sha yi masa fad’a da nasiha amma a banza, halin Abraham yasa kwata-kwata bama shiri tun muna yara, bama tab’a zama inuwa d’aya nida shi ko’a makaranta kowa harkar gabansa yake ba mai shiga harkar wani, lokacin da muke primary school Allah ya had’a jini na da MUKHTAR.

Mukhtar ya kasance d’an mai gadin gidan mu ne, halayyarmu ce tazo d’aya ni da shi dan haka muka k’ulla abota da Mukhtar duk duniya bani da wani aboki kamar Mukhtar shine babban aboki na a duniya, Allah ya sani ina mugun son sa, shima Mukhtar haka, ganin haka da iyaye na suka yi yasa suma suke son Mukhtar har suka mayar da shi d’an gida kamar d’an su, dai-dai da makaranta d’aya Abba ya samu da Mukhtar komai tare yake yi mana dashi bai tab’a ban-banta mu ba, duk duniya idan da abinda Abraham yafi tsana a duniya to bayan Mukhtar yake, kwata-kwata baya san sa baya son ganin sa, dan haka nima sama-sama muke da Abraham, dan ba wani shiri muke da shi sosai ba, musamman ma da halayyar mu ba d’aya dashi ba, kowa da yanayin rayuwar sa.

Haka dai muka gama Secondary school, Abba ya fitar da mu waje karatu mu duka uku, ni ina karantar Business Adminstration, Mukhtar yana karantar Low (Barrister) Abraham yana karantar Medicine, cikin haka har muka gama masters d’in mu kowa ya fito da kwali mai kyau, haka ma b’angaren karatun islama babu wanda acikin mu bai sauke Qur’an ba, muna girma kyawawan halayenmu ni da Mukhtar na k’ara fitowa, haka munayen halayen Abraham na k’ara bayyana dan yanzu ya zama cikekken mazinaci d’an shaye-shaye, a b’angaren kyawawan halaye kuwa idan bance Mukhtar ya fini ba to ban isa nace na fishi ba, dan tunda nake dashi ban tab’a ganin yasa koda k’ananan kaya bane kullum yana cikin manyan kaya, koda muke karatu a waje Malam ake ce masa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139 140 141 142 143 144 145 146 147 148 149 150 151 152 153Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button